Shɑfi nɑ 37 & 38

4 1 0
                                    

🐝
🐝🐝
🐝🐝🐝
🐝🐝🐝🐝
🐝🐝🐝🐝🐝🐝

       *_ƙᴜᴅᴀ ʙᴀ ᴋᴀ ʜᴀʀᴀᴍ_* 

             🐝🐝🐝🐝🐝🐝
                      🐝🐝🐝🐝
                          🐝🐝🐝
                              🐝🐝
                                  🐝

*_❝Imɑm Shɑfi'i yɑ ce: "Zinɑ bɑshi ce, 'yɑ'yɑ mɑtɑ ke biyɑ. Idɑn kɑ biyɑ dirhɑmi dubu kɑyi dɑ 'yɑr wɑni to kɑi sɑi ɑnyi dɑ 'yɑrkɑ kyɑutɑ.❞_*
≪━─━─━─━─◈─━─━─━─━≫
 

_Written by:_
           *Sɑdik Abubukɑr*

_Wɑttpɑd @sɑdikgg_

https://lafazinnishadi.blogspot.com

👮👮👮👮👮👮👮👮👮
*Wɑnnɑn lɑbɑri kirkirɑrre ne dɑ bɑi shɑfi kowɑne mɑhɑluki bɑ. Idɑn sunɑ ko siffɑ sukɑ dɑce dɑ wɑni, to ɑkɑsi ɑkɑ sɑmu. Bɑnyi dɑn cin zɑrɑfin wɑni bɑ.*✍️
👮👮👮👮👮👮👮👮👮

*_Shɑfi nɑ 37 & 38_*

Haka nan dai Anty Sakina ta saka hannu suka fara cin abincin, da ma dai ita ma'abociyar shinkafa da wake ce. Tana matukar son wannan abincin, ba ta rufa sati guda ba tare da ta yi shi ba. Cinye abincin suka yi tas! Suka dora da lemon.

Bayan sun gama ne suka dan taba hira, Anty Sakina ta ce, “Za ki dan jima kenan idan kika tafi?”

“E to, gani nan dai, Abban Annur ya ce kada na wuce kwana goma, amma ni kuma sati biyu nake son na yi. Na dade ban je gida ba wallahi, ina kewar mamana sosai.”

“Allah Sarki, ai hakane da ma idan mutum ya dade bai ga 'yan uwa ba haka yake ji. Ba ma ke ba da kike da suke nesa, koni nan idan na haura watanni biyu ban je gida ba duk sai na ji hankalina ya koma can. Lallaba shi za ki yi idan kika je sai ki yi masa waya ki ce don Allah ya kara miki sati daya, za ki ziyarci dangi sosai. To karshe sai ku daidaita a sati biyun.”

“Kuma fa hakane! Gaskiya na ji dadin wannan shawarar na gode sosai ta wajena.”

“Hmm! Mene ne abin godiyar kuma a nan, duk yi wa mai ne. Ke ma haka kike bani shawarar ai, mun zama daya.”

Hirar suke yi a zahiri, amma a can karkashin zuciyar Zainab tunanin abin da Usman yake aikatawa take, gabadaya tausayin Anty Sakina ne ya kama ta, gaskiya ba za ta iya barin wannan cin amanar da ake yi wa kawarta ba.  Kai ba ma kawarta ba wacce yake akwai aminci a tsakaninsu, kowacce mace ake yi wa irin wannan cin zarafin da keta alfarmar aure dole ne ta taimaka mata.

Don haka ya kamata ta sanar da Anty Sakina koma mene ne zai faru ya faru din, gara ta san me yake faruwa, idan ya so sai ta dauki matakin kare kanta daga cutukan zamani da ake dauka yayin jima'i. Saboda duk namijin da yake neman matan banza to karshen abin da zai samu shi ne cutar sanyi ko kuma cutar kanjamau ko kuma duk ma wata cuta me yaduwa sanadiyar hakan.

Wannan shi ne tunanin da a yanzu ya kewaye zuciyar Zainab, wanda ta alwashin tona asirin Usman. To sai dai inda gizo ke sakar shi ne, ta ya ya za ta fada wa Anty Sakinar? Wace hanya ya kamata ta bi wajen sanar da ita din, wacce za a yarda da ita?  Dole sai ta samu kwakkwarar hujja domin gudun kada ta kwana a ciki. Wadannan tambayoyin ne kuma suka ziyarci zuciyar Zainab.

A nan Anty Sakina ta yi sallar Azahar sannan ta isa gidanta ta bude ta shiga. Wannan kenan.

Kawo yanzu dai Humaira ba ta da lokacin Najib ko kadan. Idan masu karatu za su iya tunawa a can an bayyana Najib a matsayin saurayin Humaira tun tana karama, akwai alkawarin aure a tsakaninsu.

ƘUDA BA KA HARAMNơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ