🐝
🐝🐝
🐝🐝🐝
🐝🐝🐝🐝
🐝🐝🐝🐝🐝🐝*_ƙᴜᴅᴀ ʙᴀ ᴋᴀ ʜᴀʀᴀᴍ_*
🐝🐝🐝🐝🐝🐝
🐝🐝🐝🐝
🐝🐝🐝
🐝🐝
🐝*_❝Imɑm Shɑfi'i yɑ ce: "Zinɑ bɑshi ce, 'yɑ'yɑ mɑtɑ ke biyɑ. Idɑn kɑ biyɑ dirhɑmi dubu kɑyi dɑ 'yɑr wɑni to kɑi sɑi ɑnyi dɑ 'yɑrkɑ kyɑutɑ.❞_*
≪━─━─━─━─◈─━─━─━─━≫
_Written by:_
*Sɑdik Abubukɑr*_Wɑttpɑd @sɑdikgg_
👮👮👮👮👮👮👮👮👮
*Wɑnnɑn lɑbɑri kirkirɑrre ne dɑ bɑi shɑfi kowɑne mɑhɑluki bɑ. Idɑn sunɑ ko siffɑ sukɑ dɑce dɑ wɑni, to ɑkɑsi ɑkɑ sɑmu. Bɑnyi dɑn cin zɑrɑfin wɑni bɑ.*✍️
👮👮👮👮👮👮👮👮👮*_Shɑfi nɑ 29 & 30_*
Binta ta ce: “Kin ganni nan kofar gidanku na zo wajenki yanzu mummy ta ce wai kema kin tafi gidanmu.”
Cikin rawar baki da kame-kame Humaira ta ce: “E e a e hakane, amma da na zo ban same ki ba sai... Sai na tafi gidan su wata kawata.”
“Okay, to ba komai ina ne gidan sai na zo mu hadu a nan din ko?”
Humaira ta sauke wani irin numfashi me cike da firgici sannan ta ce: “Aa ki bari kawai ba sai kin zo ba, gobe Lahadi zamu hadu kawai.”
“Lafiya dai na ji kamar kina yin haki? Idan gidan babu nisa ni yanzu ba abin da zan yi a gida kawai ki fada mini na zo kin ji.”
“Aa fa na ce miki, kawai ki bari sai gobe za mu hadu koma mene ne ki ji abin da nake fada miki.”
“To shi kenan ba komai da yau da goben duk daya ne a wajen Allah.”
Tana fada ta kashe wayar ta nemi Mai Adaidaita Sahu ya dawo da ita gida abinta, Shigowarta gidan ta yi tsammanin Baba Abu za ta fada mata cewa Humaira ta zo ba ta same ta ba, amma sai ta ji shiru. Hakan ya sa ta tambayi Baba Abun ,“Humaira ta zo mun yi sabani ko?”
“Ban gane sabani ba? Nima yanzu nake shirin tambayar ki, har kin je gidan nasu?”
Wannan tambaya ta Baba Abu ta sa Binta ta fahimci lallai Humaira ba ta zo nemanta ba, akwai dai inda ta nufa ba ta so a sani ne. Wani zancen Binta ta soko da shi domin wanda ya kauda na zuwan Huamira. A zuciyarta kuma ta nutsatsa tunanin to me zai sa Huamira ta yi mata karya? Har ba ta son su hadu? Kuma ga shi ta cewa Mummynta ga inda za ta je amma ba can ta nufa ba?
To ita kuwa Humaira da ke can kwance a tube haihuwar uwa da uba, Usman ne ya ci gaba da shafa jikinta yana tambayar ta, “Wacece wannan ta kira ki a waya?”
“Wata kawata ce, wallahi na manta mun yi alkawari da ita zan je gidansu, ta ga ban je ba har rana ta fara yi shi ne ta kira ni.”
“Okay, to babu damuwa.”
Yini suka yi cir! Su na abu daya, har barci suka yi .Sai kusan la'asar sannan suka farka, nan Humaira ta shiga toilet ta yi wanka ta gyara jikinta sosai. Haka nan shi ma gogan naku ya shiga ya watsa ruwa ya fito ya mayar da kayansa.
A da can Humaira ba ta iya hada ido da Usman indai suka aikata wannan lalatar ,kunyarsa take masifar ji, amma yanzu ba wannan batun sarai take kallonsa idonta cikin nasa. Don haka baya sun gama shiryawa, zama suka yi a gefen gado tana kallonsa shi ma yana mayar mata da kallon tamkar mata da miji a dakinsu na aure.