GABATARWA

529 22 6
                                    

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah maɗaukakin Sarki. Tare da fiyayyen halitta Annabi Muhammadu (SAW), Tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi.

Hakkin Mallaka nawa ne ni Fadrees_20✅.
Ban yadda a juyamin littafina ta ko wane irin tsiga ba, ko kuma ayı audio ba tare da izinina ba domin hakan ze iya janyo ma mutum matsala.
Dan haka a kiyaye🧏.

Wannan labarin kirkirarre ne idan kuma yayi kamanceceniya da rayuwar wani ina mai neman gafara.

______________

👑👑

TSOKACİ

MASOYA DUNIYAR WATA

"Idan na daga kai na na kalli sama
Ina iya hango taurari masu matukar haske a sararin samaniyan....,
Hasken su ka iya sa mutum ya manta da kansa,
Sannan ya ɓata a cikin tunanin sa,
Ko kuma ya ji shi cikin begen dan uwansa.
Haƙiƙanin Gaskiya....,
Hasken su mai matukar daukar ido ne,

Na sake daga kai na a karo na biyu na hango hasken wata kuma....,
Sai naga hasken wata yafi taurarin haske,
Domin....,
Hasken wata ka iya saka rai cikin aminci, zuciya kuma cikin salama
Daga nan se na yanke hukuncin,
Ina nan tare da kai a duniyar wata
Domin....,
Duniyar wata itace duniyar Masoya,
Sannan itace duniya me cike da dimbin haske".

Da murmushi akan fuskarsa a lokaci guda kuma zubar hawaye ya rufe idanunsa, yana me tuna lokacin da ta kira sa da watan ta, shi kuma ya ƙira ta da tauraruwar sa, bacci na me masa wata makauniyar runguma cike da tunanin Hafsan sa da kuma ranar da shima zeje ya iske ta, se kuma tunanin yaransu, da kuma Suwaiba da Hafsa ƙarama.

______________

👑👑

RABUWA

Babu abinda ya kai kalmar nan ta 'Rabuwa' zafi,
A lokacin rabuwa.....,
Za kana tuna lokacin da kuka yi cikin jin dadi a baya,
Domin....,
Lokacin da kuka yi a cikin jin dadi a bayan,
Za kayi tunanin baka da kishiya kamar kalmar nan ta 'rabuwa',
Amma yanzu da rabuwar tazo ta,
Se ka rungume ta da hannu bibbiyu,
Domin....,
Babu kalma, ko hawaye, kai koma meye da ya isa ya gyara ta,
Haƙiƙanin Gaskiya....,
Wata rabuwar itace zata yi silan samun farin cikin ka a cikin rayuwar ka na baƙin ciki.

Hawaye ne ya kwaranyo masa daga idanun sa, gaskiya ne abinda ta rubuta, sede shi kuma rabuwar sa da ita be sama masa farin cikin komai ba sema ƙuncin da yake ciki, sede kuma wani sa'in yana ɗan jin nau'in farin ciki in ya tuna da yaran su, wani lokaci ya tuna sanda suka hadu a gidan gonan Sulaiman lokacin da aka sallame ta daga Masarauta, murmusawa yayi tuna lokacin cizon shi tayi, tace masa ta rama abinda yasa su barau suka mata ne, sake tuna wani lokacin da suke yin ɓadda kama suje cikin gari yayi, in sunje gun saida abinci cewa yake baze ci abincin waje ba, ita kuma ta dinga basa a bakin sa mutane su yi ta sha'awar su.
Tuna wani lokaci yayi sanda suka je lambun cikin masarauta suka zauna ya kawo mata furanni, sai murmushi take yi a lokacin, ashe dai zata barshi ne, murmushin mata na lokaci ƙalilan ne.

____________

👑👑

CASTS

CASTS

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

👑👑

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.


👑👑

Mu Haɗe a shafi na farko

All rights reserved ©fatimaidrissbello
FADREES🖋️🖋️
09020588802

YARİMAN HAFSA Where stories live. Discover now