MM-81

95 9 3
                                    

Kallon Zaheera ya cigaba da yi yanayin ta na kara tsinkar mata da zuciya. Yadda fuskar Nasreem ɗin ta canza lokaci guda ya tabbatar mata ko waye dambe suka yi don goshinta ya tasa ya yi jajir ga gefen bakin ya kumbura sosai.

Numfashi ta ja tana fesarwa kafin ta durkusa gabanta tana kamo hannayenta ta riƙe cikin nata. Yadda take kuka da yadda take jin jikin Nasreem na karkarwa ya kara tabbatar mata ba karamin al'amari bane ya afku. To ita da waye. Kar dai ace Farouq ne?.

Zuciyarta ta ji ta sake zurmawa da tashin hankali. Tabbas Farouq zai iya haka don ta tabbatarwa kanta tuntuni ba ƙaunar Nasreem yake kawai dai zama suke na cutar kai. Tuntuni tana so a raba auran don bata ga amfanin zaman da ba so sannan ba kulawa ba akwai ɗauƙar hakki.

Amma kuma abin da ya ɗaurewa mata kai lokuta da dama musamman in Maami ta dawo tana yawan jin su suna waya da Nasreem abubuwan da suke zance akai ya ɗaure mata kai sosai tun bata ganewa har ta gane in da suka nufa karfi da ya ji ana nemarwa Nasreem gurbin zama a zuciyar Farouq ɗin.

Ba ta yi Amanna ba ko kaɗan da tsarin da suka ɗauko don ta tabbatarwa kan tsarin sam ba mai bullewa bane. Sai dai kuma da tayi magana abin da fito daga bakin Maami shi ya sanya ta zuciya ta share batun.

"Ke sam ba kya kishina da na yar uwarki da ke kan ki. In ban bakya kishi ya za ayi ace ƴar uwarki nacin wahalar gidan Miji amma kin ka sa ko damuwa da taya ta zaman Alhini. Sai an yi magana ki shiga kawo wa mutane kauli da ba'adi da zancen ayi Hakuri. Ni ban son rashin zuciya. Sannan kuma ki kiyaye don zan yi mugun ɓata miki rai in har naji cewa kin je gidan Nasreem kin yi kokarin ɓata min abin da nake".

Da mamaki take dubana Maami gani take kamar ba ita ta haifeta ba wasu hawaye in tana yin su abun har tsoro yake bata gabaɗaya rayuwar Maami ta rasa ina ta dosa ita dai bar ta a neman kuɗi kasuwanci kawak bata damu ma ta zauna da iyalanta ta ji koken su musamman da suke Ƴaƴa mata tun kafin Nasreem tayi aure suke wannan rayuwar sai su shafe sati ba su ga Maami ba tana can tana faman yawo kasashe da sunan kasuwanci ita tun bata zargi har ta fara zargin anya Maami ba wani Boyayyen Al'amari a rayuwarta.

"Maami me kike so nayi. Hakuri ne dai shine zan ce tayi don zaman aure musamman gidan Nasreem dole a ci hakuri a rungume shi kuma. Amma dai wannan tsarin da kike kokarin ɗaurata a kai ba mai billewa bane".

Wata irin tsawa Maami ta doka mata har sai da ta zabura. Ta shiga nuna da  yatsa tana zazzare mata idanu.

"Ke ki kiyaye ni tun kafin na mugun saɓa miki tun da na lura ba ki da hankali ana neman muku tsarin zaman rayuwa ingantacce ko gidan miji ba ku wulakanci amma ke sam ba ki da wannan hankalin. Na dai faɗa miki in kika kuskura naji wani batu Allah sai na saɓa miki".

Da yake Zaheera akwai ƴar banzar zuciya tun daga wannan lokacin bata sake ko kallon Al'amarin nasu ba ko Maami ta kira Nasreem iyakarta da ita gaisuwa da tambayar gidan mijin ta kafin ta cigaba da abiɓ da take tana kallo za su kulle a ɗaki wanda ta tabbatarwa kanta ba Alheri ake ƙullawa ba.

Numfashi ta sauke tana cigaba da duban Nasreem wacce sautin kukan ya fara raguwa sai dai zubar hawaye da ajiyar zuciya da take ta faman yi hannun ɗaya ta ƙwace shi daga hannun Zaheera ɗin ta danne kirjinta gefen hagu don ji take kamar kasusuwan hakarkarin za su karkarye zuciyarta ta yo waje.

"Ni gabaɗaya kin ruɗa ni Nasreem. Wai me ke faruwa ne. Me yasa me ki haka na ganki cikin wannan daren".

Runtse idanu Nasreem tayi wasu zafafan hawaye masu kokarin dauke fatar fuska ne suka zobo mata kafin ta buɗe su tana duban Zaheera.

MATAR MIJINA...CompletedWhere stories live. Discover now