***
Durkushe yake gabanta laɓɓan bakinsa sai faman ƙaɗawa suke yi cikin sauri. Alamun son magana yake yi amma bata fita.Hannu ya mika yana son riko nata da sauri ta ja da baya tana mai girgiza masa kai hawaye ne suka shiga zubo mata masu tsananin zafi jin su take yi kamar za su yayyage mata fatar fuska.
Guiwowinsa ya dire kasa da karfi wanda sautin dirarsu har cikin zuciyarta taji su da sauri ta runtse idanu tana mai dafe kanta wata irin juya take ji tana kai kawo da ita kamar zata watsar da ita.
Numfashi yaja mai zafi wanda yake ji kamar ransa ne zai fi gyaɗa kai yake yi ga wani murmishi mai ciwo da kokarin yayyaga zuciya da yake ta faman wanzuwa a fuskarsa.
Cigaba ya yi da motsa baƙinsa hannunsa daya yana saitin da yake zaton nan ne mazaunin zuciyarsa zafi,zugi,raɗaɗi,ciwo duk su ne yake ji sun cinkushe masa a zuciya suna barazanar tarwatsa masa kirji.
A hankali ya ja wani numfashi da har sai da ya sanya kirjinsa motsawa hawaye suka zubo masa da sauri ya cigaba da gyaɗa kai bakinsa na sake kecewa da rawa.
"Don Allah Nusayba...".
Sauran maganar da ya yi niyya ta maƙale jin yadda kirjinsa ya buga da saurin laɓɓansa lokaci guda suka tsaya wani irin nauyi mai kama da an daura masa dutse yake jin harshensa ya yi.
Ware idanu take yi sosai tana jin yadda ita ma zuciyarta ke wani irin buɗewa tausayi,jin ƙai, duk sune take jin suna samun mazauni a duk wani gurbi na zuciyarta game da Farouq ji take yi kamar ta dauke masa ciwon da yake ji a jikinsa ko suyi raba dai-dai za ta so haka.
Amma ihun da take ji cikin kanta da wasu razanannun kalamai da suke amsa mata cikin kwakwalwa hakan ya dakusar da duk wani hanzarinta game dashi a hankali ta shiga ja da baya idanuwanta na sake kecewa da hawaye.
"Ban san me zan ce miki ba, ki ga ne cewa zuciyar tawa ta zama taki da gaske son ki nake yi Nusayba, don Allah ki gasgata haka...".
Numfashi ya sake yana mai sunkuyar da kansa kasa don ji yake yi in ya cigaba da duban idanuwanta zuciyarsa bindiga zata yi ta yo waje.
"Jini...!!!".
Abinda ta faɗa kenan da wata irin murya mai sauti tana mai tako kafafuwanta cikin hanzari ta iso gareshi durkushewa tayi ita ma tana mai sanya yatsunta biyu tana shafo gefen bakinsa tana mai kai yatsun nata saitin idanuwanta da wani irin razanannen yanayi take duban jinin kafin ta kai hannayenta duk biyun saitin kunnuwanta tana rufewa gami da furta.
"Da gaske nima...".
Wata irin dagowa ya yi fuskarsa na sauya launi da wani irin abu da ya sanyata kasa karasa furucinta cikin yanayi na gajiyar gangar jiki da zuciya ya dago hannunsa guda yana mai kokarin kai wa saitin ta.
Ba abin da bakinta da gangar jikinta suke yi sai rawa ta shiga girgiza kai da sauri tana mai faɗin.
"A,a..."
**
A razana ta farka tana mai sauke ajiyar numfashi mai tsananin karfi ga wani irin gumi da ta haɗa kamar wacce akayiwa sura ce a hankali take jan numfashinta da take ji bai kai wa inda ya dace hannun biyu ta kai saitin goshinta tana dafewa jin kanta take yi kamar zai rabe gida biyu.
YOU ARE READING
MATAR MIJINA...Completed
General Fiction...Zuciyarta sosai take mikata wani mataki na firgici, ba ta shirya ansar wannan lamarin ba, lamarin da take hango cikin sa ba komai ba illa tashin alkiyamar duniyarta.Tana tsoron sake afkawa tashin hankalin rayuwa sosai take jin zuciyarta bata yi a...