Duk da ya taɓa ganinsa, amma yau da suka kuma haɗuwa sai ya ji sam baya ra'ayinsa yanayin sa bai kwanta masa ba.
Ba ya jin zai iya yarda Nusaiba ta zauna inuwa daya da wannna mutumin domin ba su dace ba ta ko wani bangare.
Nisawa ya yi yana sake gyara zama sosai, idanuwansa na kara buɗewa a jikin Farouq da yake ta faman jawabi ga baƙon nasa da Yaa Jamaal ya tadda.
Bayan ya Sallami Baƙon nasa ya juyo yana duban Jamaal, fuskarsa da yanayi damuwa sosai amma ya yi kokarin ƙirƙiro murmushi yana mai kokarin magana, amma Jamaal ya tare shi gami da miƙewa tsaye sosai.
"In har da gaske kake kana sonta, za ka iya turo manyanka".
Ya faɗi yana mai kokarin ficewa daga office ɗin. Farouq dake zaune ya zuba masa idanu ji ya yi zuciyarta ta buga da sauri, a hankali ya runtse idanu yana jin wani kara cikin kwakwalwarsa kafin ya miƙe gami da buɗe idanunsa akan Jamaal.
"Ce maka nayi ina son ta, ko ce maka nayi ina ra'ayin aurenta?".
Ya faɗi a zafafe fuskarsa tana kara murtuke wa, duk da a cikin zuciyarsa tana karya ta shi amma ya ƙi yarda da hakan. Gaban Jamaal ya iso wanda ya gama shan mamakin Farouq yadda ya nuna masa rashin mutuncinsa a bayyane.
"Ita ta faɗa muku zan aure ta?".
Ya sake faɗi yana mai runtse idanu, wani jiri jiri yake ji yana kawo masa farmaki kafin ya jure yana mai tura laɓɓansa cikin baki.
"Ta ce ba ta sona ta ya ya za aure matar da bata so na, tace bata fara so ba ko ta fara baza iya yin soyayya dani ba, kana tsammanin aure ya cancanta a tsakanin mu?.Tambayarka nake ka bani amsa!".
Ya karashe da tsawa cikin muryarsa.
Ba karamin ɓatawa Jamaal rai ya yi ba, musamman tsawar da ya yi masa ji ya yi zuciyarsa ta ɗau dumi sosai, sassan jikin sa sun fara rawa hannu ya daga kamar zai kafta masa mari sai kuma ya fasa, ya naushi iska ya cigaba da fesar da huci mai zafi.Yaushe Nusaiba ta fara karya har haka, yaushe ta fara barin zuciyarta tana son wani ba tare da ya nuna yana son ta ba?.
Tambayoyin da suka shiga yi masa yawo cikin kai kenan, ransa na kara ɓaci ji yaƙe yi kamar ya shaƙi wuyar Farouq har sai ya daina numfashi.
Bai taɓa zaton rashin mutuncin nasa har ya kai haka ba amma zai yi maganinsa.
Kokarin barin Office ɗin ya ke so yayi, amma yadda zuciyarsa ke tafarfasa ba ya jin zai iya barin Farouq haka ba tare da ya nuna masa wa nene shi ba.
Juyo ya yi sosai yana fuskarsa sai dai yadda ya ganshi ya dan sanya shi waro idanu. Dafe kai ya ga ya yi sai faman nishi yake yi kamar mai cutar Asthma.
Hannunsa guda ya riƙo yana mai tambayarsa lafiya? Fizge wa ya yi yana mai yi masa mugun kallo gami da juyawa ya koma kan kujera ya zauna yana mai dafe kansa.
Hakan da Jamaal ya gani ya sanya shi daga kafaɗa alamu ko a jikinsa ya juyo yana kokarin barin Office ɗin. Nusaiba ya hango tsaye jikin kofa idanuwanta fal da hawaye jikin ta ba in da ba ya rawa.
Wani takaici ne ya turnuke Jamaal ganin Nusaiba a wajan. Ya tabbatar da maganar Farouq kenan ita take ka kawo masa kanta tana tallata masa akan ya aureta. Girgiza kai ya shiga yi kawai rantsa na kara ɓaci, zuciyarsa na kara ɗaukar zafi sosai.
A hankali ya shiga takunsa wanda ana jiyo sautin takun har ya isa gareta, hannu ya sa ya janye ta gefe guda yana mai tura kofar zai fita, juyowa ya yi ya kalleta yana mai jinjina kansa kafin ya karasa ficewa.
Ita kam mutuwar tsaye tayi ji take kamar ba a duniya take ba, ganin komai take kamar mafarki ba gaske ba. Zuciyarta ciwo take sosai ji take kirjinta ya yi mata wani irin mugun nauyi numfashin ma ji take ba ya yi mata yadda take so.
YOU ARE READING
MATAR MIJINA...Completed
General Fiction...Zuciyarta sosai take mikata wani mataki na firgici, ba ta shirya ansar wannan lamarin ba, lamarin da take hango cikin sa ba komai ba illa tashin alkiyamar duniyarta.Tana tsoron sake afkawa tashin hankalin rayuwa sosai take jin zuciyarta bata yi a...