Bai san me zai yi mata ba, wanda zai sanya ta gane ba wai kaunarta ne ba ya yi ba,...ya ya ma za ace yaya zai ki kanwarsa abinda ba zai taba yuwuwa bane tashin hankalinta ne baya so ko kadan bai son ya ga damuwa kunshe a fuskarta ko ya ya take shiyasa yake kamfa-kamfa...
Bai so Mami ta faɗa mata yau zai tafi ba, saboda ya san dole ayi rikici rikicin da zai kasance cikin damuwa a gareshi har ya bar gidan sannan ita ma Nusayba haka za tai ta kunci gar zuwa yaje ya dawo.
Miƙewa tayi daga bakin gadon da take jiki a sanyaye ta tako zuwa gareshi tana mai goge fuskarta kafun ta dube ta kau da kai.
"Yaa Jamaal ka fifita Kaƙin soja fiye dani, Yaa Jamaal ka fi kaunar kasancewan cikin kaƙin soja fiye da farinciki na Yaa Jamaal ban san me yasa ka ki yarda KAUNARMU ta musamman ce ban san me yasa ka rabata da kaƙin so ji ba Yaa...
"Enought!!".
Ya faɗi yana daga mata hannu idanuwansa lokaci guda suka kaɗa sukayi jajir fuskarsa ta kara murtukewa waje daya kamar ba shi bane mai dariya da kyalkyatawa a duk lokacin da yake tare dani.
Ras! Taji gabanta ya yi wani irin dokawa da sauri ta ja baya tana rufe bakinta jin kuka mai karfi da ya kawo mata farmaki girgiza kai take yi hawaye na sauka saman kuncinta.
Zuciyarta yake ji tana buɗewa da bacin rai sosai bai san ya yi mata tsawa har haka ba abin da tunda suke da ita bai taba yi mata shi ba...kalamanta sosai suka taɓa masa zuciya yana jin saukarsa kamar saukar narkakkiyar dalma cikin kunnuwansa jin su yake yi suna yayyaga masa zuciya.
Laɓɓansa ya tura cikin bakinsa yana cizawa kafun ya dafe kanshi yana faman furta 'Yaa Subhanallah!'.
"Am...so sorry Nusee".
Ya furta yana jin duniyar gabadaya ta canza masa da wani irin yanayi mai girma NADAMA yake ji tana saukarsa masa ta ko ina wai shine yau ya yi wa Nusee tsawa?. Ya kasa gasgata lamarin gani yake yi kamar ba gaske bane amma yadda zuciyarsa ke canza mugu da yadda yake kallon tsoro mai girma a idanun Nusee din ya tabbatar masa ya yi kuskure mai girma.
Shafe hawayenta ta shiga yi kafun fuskarta ta saki wani murmushi wanda da ka kalle ta za ka gane yafi kuka ciwo.
"Ba komai Yaa Jamaal please buɗe mani kofar na fita kar nayi latti".
Ta karasa cikin danne abin da take ji yana taso mata tun daga kasar zuciya yana koƙari danne mata harshe.
Girgiza kai ya shiga yi don ya rasa ma me ya dace ya yi da na sani yake yi da na sani mai girma wanda ba ya zaton komai zai koma daidai tunda har ya iya yi mata tsawa dole ta buɗe gurbi mai girma na tsalar aikin Soja da yake yi don alhakin faruwar komai yana kan aiki sa dole ta ji a ranta yafi kaunar kaƙin soja fiye da ita kanwarsa da suke UWA DAYA UBA DAYA.
"Don Allah Yaa Jamaal".
Ta sake faɗi cikin yanayi na rawar murya da sauri ya juya ya buɗe mata kofa gefe ya koma ya jingina da bango yana runtse idanuwansa haɗi da dafe kansa da yake jin yana sara masa.
Bai san wata irin kauna bace tsakaninsa da Nusayba ba, bai san ya zai kwatanta son da yake yi mata ba, ba ya jin akwai wata halitta da zai yi wa irin wannan son bayan iyayensu.
Ya shaku da ita shakuwa mai girma wacce ta assassa kauna da so mai tsananin yawa a zuciyarsa kamar yadda ita ma wannan kauna da so zallar su suke narke a zuciyarta so da kaunar da ke sanya su kin yiwa juna laifi sannan ba sa so ko wani ne ya taba daya daga cikin su.
YOU ARE READING
MATAR MIJINA...Completed
General Fiction...Zuciyarta sosai take mikata wani mataki na firgici, ba ta shirya ansar wannan lamarin ba, lamarin da take hango cikin sa ba komai ba illa tashin alkiyamar duniyarta.Tana tsoron sake afkawa tashin hankalin rayuwa sosai take jin zuciyarta bata yi a...