***
Numfashe ya ajje da wani irin yanayi, wanda yake jin wani abu mai kama da dutse da ya jima a tsakanin zuciyarsa da maƙoshinsa na kara samun wajan zama.Hannu ya kai yana dafe kirjinsa yana mai runtse idanu wani irin yanayi yake jin kansa a ciki dukkanin jikinsa yake ji yana masa wani irin sanyi na ban mamaki.Buɗe idanuwansa ya yi da suka kaɗa lokaci guda sukayi jajir, numfashin sa yake ji har yanzu yaki zama daidai don haka ya shiga buɗe bakinsa ko zai samu sassauci, Ko dashi ba likita bane amma zai iya ganewa akwai ciwo cikin zuciyarsa, yadda yake jin motsin zuciyarsa cikin watanni takwas da ya yi rabonsa da gida, yana bashi mamaki, a duk daƙiƙa yana jin bugun zuciyarsa na sauyawa da wani irin yanayi wanda har wannan lokaci ya kasa gane manufarsa, ya kasa zuwa wajan likita ya duba shi, don ko yaje ya san abu ɗaya ne shine zuciyarsa na ciwo don haka bai ga dalilin zuwansa asibiti ya ɓata wa kansa lokaci ba.
Miƙewa ya yi zaune daga ɗan madaidaicin gadon hutu wanda ya kasance na raga ne mai kwari an ɗaure igiyoyinsa tsakanin bishiyun da suke wajan reras, ba ka jin komai sai sautin kukan tsintsaye, daga can nesa da wajan kuma tanti ne kashi-kashi wanda ya kasance da kalar kayan sojoji.
Ƙafarsa ɗaya ya saukar da ita ɗaya kuma ya tankwashe ta, hannunsa riƙe da robar lemo a hankali ya shiga ɗagawa yana ɗaɗɗakawa cikinsa, amma duk da sanyin lemon ko kadan bai jin sassaucin zafin da yake ji yana tasowa daga ƙasar zuciyarsa, lumshe idanu ya yi ya buɗe yana mai bin inda tantin suke girke kashi-kashi da kallo kafin ya ɗauke kansa yana duban gefen hagunsa in da ya kasance daji ne sosai mai ɗauke da dogayen bishiyu, da tsaunuka daga can nesa, yatsine fuska ya yi kamar wanda ya ga wani mugun abu, kafin ya sake ɗaga robar lemon yana tuntulewa cikinsa gabaɗaya yana matseta a tsakanin yatsunsa yana wurgar da ita.
Miƙewa ya yi yana sauka daga kan gadon, jikinsa sanye yake da wando iya guiwa wanda ya kasance kalar kayan soji, sai riga fara tas mai gajeran hannun wacce ta kama masa jiki sosai ta fiddo da tsarin halittar jikinsa na ingarmar namiji damatsansa duk murɗe suke haka kirjinsa ya cika sosai kamar zai yaga rigar.
Kallo ɗaya zaka yi masa ka hango zallar rama a idanunsa da suka zurma fuskarsa tayi fayau sai sajen da ya fito masa kadan ya zagaye masa fuska, kansa ma gashi ya fara fita alamu bai dade da yin aski ba, amma sabida rashin gyara duk ya yi wani kala daban.
A hankali ya fara takawa kafafuwansa sautin busassun ganyayyiki da ke zube wajan na amsawa, da wani irin sauti wanda yake sanya shi yatsine fuska alamun baya so. Tafiya ya yi sosai yana nufar cikin dajin kafin ya isa wajan wani dutse mai girma da faɗi daga kasansa kuma wani dan gulbi ne wanda ruwansa yake fari tas sai guduna yake.
Gefen ruwan ya isa yana mai harɗe hannayensa a kirji idanunsa zube cikin ruwan, a hankali yake ajje numfashi cikin kansa yake jin wani irin abu mai kama da agogo yana kaɗawa, ba yanzu ya fara jin wannan sautin ba, zai iya rantsewa tun ranar da ya tako ya baro gida hakan ya fara kasancewa a gareshi har zuwa wannan lokaci.
Bugun zuciyarsa kau! ba zan iya cewa ga adadin canza bugu da ta yi ba, mafi yawan lokaci ya na jin bugun zuciyarsa na bugawa da yanayi kamar na tashin hankali, hakan ya fara ne wata uku bayan dawowarsa wajan aiki, ko cikin barcinsa hakan na faruwa wani lokacin numfashin sai ya ji kamar zai ɗauke, ko kuma in ya tashi ya kasance cikin damuwa da ɓacin rai har bai so wani cikin abokanan aikinsa su nufe shi da wani zance, kamar yadda ya kasance yau.
Tun daya tashi yake jin wani kunci na danne masa zuciya, ga kwakwalwarsa da yake taji tana ɗaukar dumi na rashin dalili, tunani yake ji na daban yake jin kwakwalwarsa na kaiwa zuciyarsa amma ya kasa gane tunanin akan meye, ya san dai zuciyarsa na zafi kwakwalwarsa na haifar masa da ciwon kai na ɓarin ɗaya.
"Sadauki".
Runtse idanu ya yi, ba abinda yake bukata kenan ba, baya so ko kaɗan a irin wannan halin da yake ciki ya ji muryar wani, amma a yanzu yadda yaji sautin kiran da ake masa ji yake kamar ya ɗaura hannu a ka ya kurma ihu dukkanin dajin ya ɗauka, amma ya san haka ba mafita bace gareshi.
YOU ARE READING
MATAR MIJINA...Completed
General Fiction...Zuciyarta sosai take mikata wani mataki na firgici, ba ta shirya ansar wannan lamarin ba, lamarin da take hango cikin sa ba komai ba illa tashin alkiyamar duniyarta.Tana tsoron sake afkawa tashin hankalin rayuwa sosai take jin zuciyarta bata yi a...