"Batool".
Nasreem ta faɗi cike da Mamaki a karo na ba'adadi.
"Mamaki ya kasa barina da gaske nake faɗa miki".
Batool dake fama taunar cingum ta dube ta a sheƙe sabida takaicin dake citta yadda ta ga ƙawarta ta canza gabadaya kamar wata wacce ta faɗo daga sama.
"Yo ba dole kiyi Mamakin gani ba, tunda kin yi aure kin yi bulunbukui ke dadi miji yaushe za ki tuna da wata Batool. Har kirin ki nake a waya amma kika kasa gane ni".
Mamaki ne ya cika Nasreem sai yanzu take tuna wani abu tabbas watannin baya an sha kiranta amma bata taɓa daukar murya ba, bata taɓa zaton Batool bace ƙawarta.
"Don Allah kiyi hakuri Batool abubuwa ne duk suka ɗaure min kai".
"Dole abubuwa su ɗaure miki kai tunda kin ɗaurawa kan ki jidali, har gida naje lokacin Mami bata nan sai Zaheera na samu nan nake tambayar ta ke, take faɗa min ai kin yi aure ga halin ma da kike ciki raina ya yi mugun ɓaci ba kadan. Ban taɓa zaton za kiyiwa kan ki wannan gangancin ba".
"Batool kenan".
Dubanta kawai take cikin wani irin yanayi na takaici kafin ta kai hannu tana taɓa kashin wuyar da suka firfito wa Nasreem.
Taɓe baki tayi.
"Ban taɓa ganin wacce bata son rayuwa kamar ki ba, ban taba ganin wacce ta mai da wahalar ɗa namiji abin so gareta ba. Har yaushe zan yarda. Sai kace shi kaɗai ne namiji da za ki zauna kina wahala haka..anya da zuciya a jikin ki Nasreem".
Gyaɗa kai kawai take tana duban Batool don bata san mi zata ce mata ba ta lura bata san so ba shiyasa take yanke mata hukunci ta yadda ta ga dama.
"Batool baki san so ba"
Gyaɗa kai tayi tana murmushin takaici.
"Son ya ci ubansa. Ni har akwai Namijin da zan zauna ina wahala akan sa don ina son sa, wallahi ba ayi shi ba uwarsa ma bata zo duniya ba balle ta haife shi".
Nasreem ji tayi kamar Batool zagin Farouq take don haka ta dubeta cike da yanayi na damuwa.
"Plesea Batool mu bar zancen nan. Me ke tafiya ne yaushe za ki yi aure?".
Wani kallon galala Batool tayi mata na kin raina min hankali. Kafin ta bushe da dariya.
"Aure ni nayi aure? Haba Nasreem ai ke ma kin min faɗa, ji fa yadda kike, sannan kice na bi sahunki ina ba zai yuwuwa ba. Ba zan taɓa yin aure a halin da ake ciki ba yanzu don ba yanzu na shirya masa ba, ba ma wannan ba nifa in kika nayi aure to tabbas mijin da zan aura shi ke mugun sonq ba ni ke son sa ba, don yadda na fahimce ki, ke kike son Mijin nan naki ba shi ke son ki ba, Uban wa ya aike ni wannan gangancin. Wasu maza ba mutunci gare su ba a waje ya aka kare da su bare kuma ka shigo hannunsu sun ɗaure ka da igiyoyin aure".
Gyaɗa kai Nasreem tayi don ita kanta tabbatar da cewa Aure baya gaban Batool don tun ba yau ba ta faɗi ta kuma nanatawa ba za tayi aure da kananun shekarunta ba haka kawai namiji ya mai da ita tsohuwa a kankanin lokaci.
Turo kofa akayi aka shigo dukkan su suka mai da kallon su ga ƙofar Farouq ne ya shigo jikinsa sanye da kananun kaya wanda suka yi mugun amsar sa sai faman murmushi yake waya maƙale a kunnan sa. Wata irin dokawa zuciyar Nasreem tayi wani kyau na ban mamaki Farouq ke mata a yan kwanakin nan kuma tasan hakan na da nasaba da auren da zai yi wanda ya kasance yau saura kwana Uku.
Batool da ta saki baki da hanci idanuwanta kur! akan Farouq zuciyarta dokawa take da wani irin yanayi mai girma kafin ta lumshe idanu tana buɗewa lokaci guda ta ji wani irin yanayi game da Farouq ya saukar mata a duk sassan jikinta.
YOU ARE READING
MATAR MIJINA...Completed
General Fiction...Zuciyarta sosai take mikata wani mataki na firgici, ba ta shirya ansar wannan lamarin ba, lamarin da take hango cikin sa ba komai ba illa tashin alkiyamar duniyarta.Tana tsoron sake afkawa tashin hankalin rayuwa sosai take jin zuciyarta bata yi a...