Da gudu ta fice daga cikin motar ko tsayawa kasheta ba tayi ba jakarta da wayarta duk ciki ta bar su mai-gadi da ya yi sakato da baki yana kallonta sai da ya ga ta isa kofar falon ta tura tashiga sannan ya mai da bakinsa ya rufe yana mai duban motar dake fake tsakar gidan tana ta faman nishi
**
Babban robar ruwan C-ways ta mai rangwamin sanyi ta janyo daga cikin firij din ko ina na jikinta rawa kawai yake yi haka ta murɗe kan robar ta shiga tuntulawa cikinta cikin hanzari don jin zuciyarta take yi tana ci da wuta in ba saurin kai mata agaji tayi ba babbakewa za ta yi.
Cillar da robar tayi tana mai da numfashi da sauri-sauri ki take yi kamar numfashin nata zai dauke gabadaya.
Buɗe baki tayi tana mai kara karfin numfashin nata don ji take yi baya kai mata yadda ya kamata.
Runtse idanu tayi tana sake buɗe ganin komai take yi kamar ba gaske ba ganin komai take yi kamar a duniyar Baɗini ba zahiri ba.
Zubewa tayi cikin daya daga kujerun falon idanuwanta har zuwa lokacin a lumshe zuciyarta sai faman sake firgicewa take yi game da furucin Farouq so take yi ta tabbatar mata da cewa gaskiya ne amma wani sashi na zuciyarta ya ƙi aminta da hakan amma yadda gangar jikinta ya ki amsa shima.
Dumin hawayen da taji saman kumcinta ya sanya ta buɗe idanu da sauri tana mai kai hannunta tana dangwalowa tana saita da idanuwanta gyaɗa kai tayi tana mai tambayar kanta wadannan hawayen na mene ne?.
Sai dai ta rasa amsar da zata jogana wa hawayen illah cigaba da nishi da tayi zuciyarta na kara buɗe wani sashi da ta jima tana jin sa can kasar zuciyarta sai yau taji ya buɗe wani sanyi take ji yana ratsa zuciyarta ta lokaci guda.
'So'.
Taji kalmar nayi mata yawo cikin kai tana kuma karawa zuciyarta nauyi danɗanon da take ji wani kala daban ne wanda b aza ta iya tantance shi ba wanda ta tabbata game da waccen kalmar ce danɗanon harshenta ya sauya.
"Yaa Rabbi".
Ta furta a bayyane tana mai yawata idanuwan zuwa cikin falon ba ta taba zaton zata iya kawo kanta gida ba, don tunda ta fallo daga cikin Company zuciyarta ke duka ta sadakar ta ta ta kare ikon Rabbi kawai ya kawo ta.
Mikewa tayi don ji tayi zaman ya gagare ta kamara wacce ta haɗiyi tabarya ta shiga ka kawo tsakiyar falon tana faman dukan hannun guda da dayan.
Tunani take so tayi amma kwakwalwarta da alamun taje hutun wucin gani don ba abinda take kokarin kawo mata sabo illa kalaman Farouq ta suka ki yin sanyi waccan fallasa kan su.
Kamar wata wacce take fareti haka ta koma a tsakiyar falon idanuwanta a rufe abubuwan da suka faru ne kawai suke yi mata gizo so take yi ta manta komai ko zata samu ta dawo kan doka da oda amma hakan ya garara.
Tana ji aka buɗe kofar aka shigo amm aba ta sadadu daga fareti din da take yi ba sannna ba ta buɗe idanunta alamu ya nuna ma bata da niyya.
'Wai ni yake so? Yaa Rabbi'.
Ta faɗi can kasar zuciyarta sai dai abinda ba ta sani ba furucin nata ya fito fili sosai kuma daidai lokacin Maami ta iso gareta idanuwanta akanta mami ya cika ta sosai ganin yanayin Nusaiba din bata kara tsinkewa da al'amarin nata ba sai da taji furucin da tayi ya daki dodon kunnuwanta cak! ta tsaya tana mai ajiyar zuciya kafun ta kara buɗe idanunta cikin yanayi na al'ajabi tana duban Nusaiba din.
YOU ARE READING
MATAR MIJINA...Completed
General Fiction...Zuciyarta sosai take mikata wani mataki na firgici, ba ta shirya ansar wannan lamarin ba, lamarin da take hango cikin sa ba komai ba illa tashin alkiyamar duniyarta.Tana tsoron sake afkawa tashin hankalin rayuwa sosai take jin zuciyarta bata yi a...