MM-84

83 17 0
                                    

Wani irin azababben gumine taji yana saukar ma a dukkanin jikinta. Numfashinta lokaci guda taji yana kokarin ƙwace mata. A hankali ta shiga buɗe baki tana rufe kafin ta sanya tafukan hannayenta tana fifita fuskarta da take jin tana wani irin turiri kamar wacce aka fidda daga cikin sura ce.

Gabaɗaya ta take jin duniyar kamar ita kaɗai ne a cikinta tans murɗewa da ita jijiyoyin jikinta ds gaɓoɓinta suna takurewa waje ɗaya.

Ta kasa gasgata abinda ke faruwa a yanzu, zuciyarta ta ƙi amin ta dacewa dagaske komai ƙe faruwa ba mafarki bane. Ta kass yarjewa kanta cewa MAFARKIN IDO BIYU a yanzu haka yake faruwa .kenan dai komai a zahiri ba a baɗini ba.

'Yaa Rabb'.

Ta furta daga can ƙasar maƙoshinta zuciyarta take ji tana sake curewa.

'Dagaske Batool amanarta za ta ci. Da gaske duk abin da take mata kokarin cutar da ita take. Da gaske rayuwar auran ta take so tarwatsawa. Shin yaushe ta fara son Farouq ita ma?'.

Ta shiga jero wa kanta tambayoyin da ta san ko wuƙa a makoshi za a ɗaura mata bata da amsar su.

Lumshe idanu tayi tana buɗe su lokaci guda tana duban Batool da har yanzu take faman sakar mata murmushi mai nuni da cewa 'Nayi nasara akan ki'.

"Na tabbata Batool ba za ta kawo miki mafita ta hanyar da ta dace ba. Na san halinta ke ma kin san halinta".

Kalaman ta ji suna sauƙar mata cikin kai, amma ta rasa waye ya faɗa mata su a lokacin tana ganiyar neman mafita idanunta sun rufe nasara kawai take bukata akan Farouq burinta kawai ya so ya kauna ce ta ta ko wacce irin hanya ce. A lokacin ta kasa amfani da maganar gani take kamar cutar da ita za ayi gani take kamar ba a kaunar ta da Farouq.

'Kullum ba ki da mafita illa kice in yi hakuri na gaji ba zan iya ba'.

Ihun kalaman taji cikin kanta a lokacin da ta furta su ga Hayat. Sai yanzu ta tuna sai yanzu take hango kuskure da yaudarar kanta da tayi sai yanzu ta fahimci abinda Hayat take kokarin sanar mata sai yanzu ta gane abin da take so ta fahimta amma ta ƙi har ya kai matakin da ta yi mata gorin aure.

"Farouq".

Sunan Farouq da Batool ta kira shi ya katse mata tunanin zuci da take yi da sauri ta juya tana kallon sashin ɗakin barcin ta. Farouq ne ya fito har zuwa lokacin hannayensa na goshinsa idanunsa sun kaɗa sun yi jajir. Amma ita Nasreem ba haka take kallonsa ba.

Gani take kamar yana yi wa Batool murmushi mai ban ƙaye tare da saƙon ni na musamman da suke bayyana cikin idanunsa.

Wani irin jiri tana ji yana ɗibarta juyar na zuciya mata Farouq yana kara canza mata daga yadda ta san shi zuwa wani daban.

"Ina! Ba zai yuwu ba".

Ta furta a zuciyarsa sai dai abin da bata sani ba kalaman sun fito sun amsa kuwwa a cikin falon har hakan ya sanya Farouq toshe kunnuwansa da yake jin su kamar za su tarwatse.

Kafin ta juya ta nufi Batool gadan ganda wacce ita gabaɗaya hankalinta ya tafi ga Farouq. Zuciyarta na tabbatar mata da aikin ta ya tabbata tayi nasara.

"Ki ji a ranki kamar kin mallake shi ne tuntuni tsayim shekaru. Ki ji a ranki kamar kece kwal a duniya mace a duniyarsa. Ki ji a ranki tamkar ke kaɗai ce macen da ta fara sanin shi a matsayin miji".

MATAR MIJINA...CompletedWhere stories live. Discover now