Wani irin take jin kanta a ciki, ta kasa bambance farinciki take ciki ko kuma akasin hakan.
Zuciyarta take ji tana harbawa a duk daƙiƙa da wani abu mai girma wanda take ji ya tsaya mata cak! A tsakanin maƙoshi da kirjinta shi bai faɗa cikinta ba, bai kuma fito waje ba.
Hannunta ta sanya tana goge goshin ta, wani irin gumi take ji yana karyo mata na rashin dalili, duk da sanyin Ac dake busawa a ɗakin amma gumin kara fitowa yake a dukkan wata ƙafa ta jikinta.
"Allah ya sanya alheri. Ya kaimu lokacin".
Sautin da taji ya dire mata cikin kunnuwa kenan. Yana sanya zuciyarta tsalle kafin ta koma gurbin ta.
Har yanzu ta kasa yarda, gani take kamar mafarki ne ke faruwa da ita. Amma yadda take jin muryoyi daga falon su na tashi ya tabbatar mata da gaske ita ake yiwa Baiko yau tare da Zaɓinta Farouq Ma'arouf Kutigi.
'Me ya kamata tayi?'.Ta ji laɓɓanta na faɗin haka. Runtse idanu tayi tana jin wani abu mai kama iskar yanayin damina na kaɗawa a duk sassan jikinta har cikin zuciyarta da wani irin yanayi. Za ta yarda in har wani ya zo ya kamata a kafaɗa ya jinjiga ya sanar da ita ba mafarki take yi ba. Zata yarda in ta ji Mami ta shigo fuskarta da fara'a tana sanar da ita komai ya Kammala fuskarta ɗauke da murmushi.
Wata irin dokawa zuciyarta tayi har sai da tayi saurin kai hannayenta duka tana dafewa zuciyarta take ji kamar zata faso kirjinta ta faɗo kasa.
'Mami'.
Ta ji sunan ya sake amsa kuwwa cikin kunnuwanta suna sanya zuciyarta karkarwa kafin ta koma mazauninta tana zama.
"Ban hana ki auren saba, amma ni ba zaɓin da bane".
Ta tuna da kalaman Mami a dazu da safe bayan sun kammala Breakfast ana zancen abin da ya kamata ayi na taryar baƙin da za su zo daga gidan su Farouq.
"Sam bai min ba. Bana jin sa ya kwanta min a rai, kawai ba yadda zan yi ne, ban so na tauye miki ra'ayinki. Ke za ki zauna dashi ba ni ba. Amma har ga Allah zuciyata motsawa take da wani irin yanayi game da zaɓin nan naki".
Hawaye taji marasa gudu sun fara gangaro mata zuciyarta na matsewa da wani irin ciwo da ta jima dashi a zuciya. Tun lokacin da Mami ta raina zaɓinta. Ta tabbatar wa kan tun haɗuwar Mami da Farouq a karon farko ta hango rashin so a idanunta a game dashi.
'Yaa Ilahi'.
Ta shiga faɗi tana faman girgiza kai. Tana cikin yanayi na tsananin damuwa ba karamin tashin hankali take hangowa kanta ba rashin samun damar Mami game da lamarin nan dari bisa dari na ruguza mata duk wani muraɗin da ta daura kan son Farouq.
'Anya ba hakuri za ta yi ba?'.
Ta ji wani sashi na zuciyarta na faɗi mata haka.
'A,a hakan ba mafita bane, ki cigaba da addu'a da kuma kara kusancin halayen Farouq nagari ga Mami za ta amince dashi kafin lokacin'.
Wani sashi na zuciyarta ya sake sanar da ita. Nan da nan ta aminta da wannan shawarar tana ji a ranta fushin Mami na ɗan lokaci in har ta fayyace mata komai game da halayen Farouq za ta so shi.
'Kin manta yana shan sigari'.
Wani sashin zuciyarta ya sake tunatar da ita ji tayi kwakwalwar da duk jikinta sun shiga rawa. Lokaci guda ta ji haduwar ta dashi a rana ta farko tabbas ta gani yana shan sigari.
Tabbas yana shan sigari, amma wanda ba matsala ba tunda sigari kadai yake sha, zata iya canza shi kafin bikin nasu tana jin haka a ranta.
Miƙewa tayi daƙyar ta nufi hanyar fita, har ta kai bakin kofa ta juyo da sauri jin takun tafiya, wanda ta tabbatar na Mami ne
YOU ARE READING
MATAR MIJINA...Completed
General Fiction...Zuciyarta sosai take mikata wani mataki na firgici, ba ta shirya ansar wannan lamarin ba, lamarin da take hango cikin sa ba komai ba illa tashin alkiyamar duniyarta.Tana tsoron sake afkawa tashin hankalin rayuwa sosai take jin zuciyarta bata yi a...