Ba ta ce mata uffan! ba har suka isa parking space Mami ta buɗe motar ta shiga ta zauna tana mai ajje numfashi mai kwari.
Ita kam Nusaiba gabadaya a firgice take bata cikin hayyacinta kirjinta luguɗen bugu kawai yake yi kallo da Mami take watsa mata jinsa take yi a cikin tsokkar jikinta.
Fargaba sosai ta samu gurbin zama a zuciyarta shiga motar ma tsoro take yi don bata san me Mami zata dube ta dashi ba don ta fuskanci ta zo wuya sosai ranta ya yi mugun ɓaci ba kadan ba.
Numfashi ta sauke hannun rike da marikin kofar motar amma ta kasa buɗewa ta shiga tana ji Mami ta tada motar tayi mata giya amma har xuw lokacin bata yankewa kanta hukucin shiga motar ba.
"In ba za ki shigo ba naja mota ta nayi gaba".
Mami ta faɗi muryarta da alamun ɓacin rai sosai. Da sauri ta bude ta shiga ta zauna jin ta take kamar ta zauna kan ƙaya gabadaya a takure take.
A jikin ta take jin kalar kallon da Mami take yi mata kasa ta sake yi da kai don bata son ma su haɗa idanu.
Ƙwaɓa Mami tayi kafun tayi w amotar giya ta ja suka fice daga cikin wajan.
Duk abind ake faruwa Farouq na tsaye yana kallon su zuciyarsa na sake hargitse masa ji yake yi kamar ya yi tsuntsuwa ya ji shi cikin motar zaune kusa da Nusaiba amma yasan hakan ba zai taba yuwuwa ba bata ya son abinda zai aikata wanda zai sanya Nusaiba cikin matsala musamman kallon da yake hangowa Mami nayi mata kuma fuskarta ba alamun fara'a ko kaɗan kamar hadadden hadarin dake kokarin zuɓda ruwa.
Numfashi ya ja yana fesar da huci mai zafi kafun cikin yanayi na sanyi jiki ya ja kafafuwan sa ya isa ind aya ajje motarsa.
Bai taba zaton zai tadda Nusaiba a irin wajan nan ba zuciyars ace kawai ta janyo shi da kawo shi don ya kasa samun sukuni a cikin gidan tun da garin Allah ya waye yake jin komai ba ya yi masa dadi shiyasa ya fito a tunanin in ya zo wajan shaƙatawar nan zai samu saukin tension din da yake ci sai gashi sun yin GAM-DA-KATAR tare da abin da rashin sa ya hana shi sukuni da walwalar zuciya.
Remote Control ya danna haske ya bayyana a fitilun motar tasa kafun tayi wani tsuwwa mai dadin sauraro.
Buɗewa ya yi ya shig yana mai haɗe kansa da sitiyarin motar numfashin yake fitar sannu-sannu zuciyarwa yake ji gabadaya ta ki dawowa mazauninta sai faman safah-da-marwa take yi.
Kalar kallon da Nusaiba take masa y kasa barin kwanyarsa ji yake yi tana hautsinewa tana dauko fuskar Nusaiba tana kawo masa idanuwanta yake kallo masu kalar fari fat! da wani kalar ruwa mai kama da na Rose wand suke kara ƙawata idanun nata zuciyarsa fizge take yi a duk lokacin da idanuwanta suka kasance sarke da na shi tun RANAR FARKO hakan ta faru wanda zuciyarsa ta ajje komai take kara buɗe shi a duk wani sashi na zuciyarsa.
Ya sani yana son Nusaib wanda y akas ama kwatanta yadda zai furta kalar son ji yake yi kamar shi kawai so ya zo masa da kalar wannan salon na daban.
So yake yi ya furta mata son ta hanya mai sauki mai sai ya biyo ta hanyar amfani da ZUCIYA DA KWANJI ba kamar yadda yake jin wani sashi na zuciyarsa na karanta masa hakan sai dai falsafarsa bata yarda da wannan tsarin ba mai cike da ganganci da wauta.
***
Kai kawo kawai take yi tsakar dakinta gabadaya ta gama shiga cikin RUƊANI wanda ya rasa yadda zata kwatantashi tunda take da Mami bata taba nuna mata fuskar kalar shanu irin haka ko da kuwa laifin da tayi mai girma a take a wajan zata hukunta ta ba tare da jinkiri ba.
YOU ARE READING
MATAR MIJINA...Completed
General Fiction...Zuciyarta sosai take mikata wani mataki na firgici, ba ta shirya ansar wannan lamarin ba, lamarin da take hango cikin sa ba komai ba illa tashin alkiyamar duniyarta.Tana tsoron sake afkawa tashin hankalin rayuwa sosai take jin zuciyarta bata yi a...