MURFI!

299 18 2
                                    

MURFI!
BAYAN SHEKARU BIYU.

Tunda ta fito daga office ɗin DR. SARAKI. gabaɗaya ta jin zuciyarta na kara tsinkewa har zuwa wannan lokaci da komai ya zo ƙarshe ta kasa gasgata abin da Dr. Ya tabbatar mata game da lalurarta wai ita da ke da Cancer how come's tana mamakin abin har zuwa wannan lokaci.

Ko da yake in har bata son wahalar da kwakwalwarta ai amsa a hannunta take kamar yadda Dr ya yi mata fashin baki akan komai.

"Maganar gaskiya Nasreem cutar nan tayi matuƙar tasiri a jikinki wanda in har  ba ki gaggwar fidda solution to komai zai  iya faruwa da rayuwarki".

Yadda yake mata bayanin jin sa take kamar saukar aradu a tsakiyarka. Kallonsa kawai ta dinga yi har zuwa lokacin da ya gama kora mata jawabi ya miƙo ta test result ɗinta. Wanda ya tabbatar da cewa tana ɗauke da cutar kansar mahaifa.

Bata  san lokacin da hawaye suka ƙwace mata duk a tsayin shekaru biyun nan da tayi cikin ƙunci da takaicin rayuwa bata taɓa kawo kanta cewa akwai wata mummunar ƙaddara da zata same ba bayan ta rabuwa da masoyinta tilo ɗaya tak! da zuciyarta ta fara so kuma ta ke jin har abada zuciyarta ba za ta sake son wani namiji a duniyar nan ba bayan FAROUQ MA'AROUF KUTIGI...Namiji tilo ɗaya da ta tsara rayuwarta dashi duk mafarkanta sun ƙare akansa sai dai kuma tayi wa kamta giɓi giɓi na musamman wanda yake bibiyar ta har wannan lokaci tare da taimakon mahaifiyarta.

In ba don UWA UWA CE ba ai ba abin da zai sanya ko duban Maami ta sake yi a idanunta kawai ba yadda za tayi ƙaddarar tana tafe a haka kuma ta ɗauki hakan ta saka a ranta duk da ita kanta ta san akwai SAKACINTA da kuma SHARRI ƘAWA. Ƙawarta har abada ba za ta manta da ita a duniyarta ba ƙawar da ta kassara mata rayuwa ta gurɓata mata duk wani fata da burinta.

Tafe take a hankali kamar mai ciwo a tafukan kafar ta hawaye take ɗauke wa wasu na bin wasu gabanta ba ganinsa take sosai ba har ta isa farfarjin asibitin. Jiri ta ji yana kokarin yasar da ita da sauri ta dafe bango tana mai runtse idanu da wani irin yanayi mai ciwo a zuci.

Waje ta samu gefe guda ta zauna tana haɗe kanta da guiwa wani irin raɗaɗi da zafin zuci take ji yana ta so mata yana naɗe mata gangar jiki gabaɗaya yana haifar mata da wata irin nadama wacce har abada take jin da ita zata koma ga mahaliccin ta.

"In da zan baki shawara as a Doctor da na ce ki daure ki ɗauki ƙaddarar ki a yadda take ki bari a cire mahaifar nan gabaɗaya don duk wani Doctor a ƙasar nan ko wata ƙasar daban da yace miki a barta a jikinki to tabbas ya yi don wani buri nashi amma ba don lafiyarki ba. Cutar ta rigaya ta cinye kaso casa'in da biyar ta mahaifarki Nasreem. Maganguna ba za su iya fin karfin ta har a samu abin da ake so ba. Jinin da kike zubdawa ma kaɗai ya isa ki kasa rayuwa a natse... Allurai da ƙwayoyin hana haihu da kika yi amfani da su sannan ga Abortion da aka miki a farkon cikin ki tun ana kika samu matsala sannan ga abin da na lissafo na ƙwayoyi da allurai suka karasa karya garguwar mahaifarki gami da kamuwa da cancer".

Kuka ne mai ƙarfi ya kwace mata gabaɗaya ta manta a inda ma take sai da taji alamun mutane kusa da ita ana bata haƙuri sannan ta dago fuskarta da hawaye tana dubansu kafin ta toshe bakinta tana miƙawa da hanzari.
Ta shiga haɗa step din benen tana sauka. Sai dai bata kai ga isa karshe taji kafarta ta turguɗe lokaci guda zuciyarta tayi bugun bugawa bisa mugun gani da idanuwanta suka yi mata. Kamar wacce ake tunzarawa haka ta karasa sauka tana isa inda wata mace take zaune kan keken guragu kallo ɗaya zaka yi mata ka gane tana cikin mugun yanayi. Musamman in ka santa a da yanzu ka ganta ko WUƘA A MAƘOSHI za a ɗaura maka zaka karyata ce wa ita ce

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jun 24, 2021 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

MATAR MIJINA...CompletedWhere stories live. Discover now