Sai wajajen Sha biyun rana ta ji sassauci ya fara zuwa mata haka ta miƙe ta shiga toilet ta sake yin wanka ta dawo doguwar jallabiya kawai ta zira jikinta ta yane kanta da gyalen jallabiyar kafun ta isa gaban MADUBI tana duban kanta hannunta guda saman fuskarta tana shafa lokaci guda ta ga duk ta rame tayi wata firga-firga da ita kamar wacce ta tashi daga cuta.
Numfashi ta sake kafu ta dubi kayan kwalliyar dake ajje reras kamar Shagon Cosmetic's wani irin abu ta ji ya tsirgar mata a zuciya kafu ta juya ta fara takawa a hankali ta fice daga cikin dakin.
Falo ta sanko ba kowa a cikin sa illa Tv dake ta faman aiki samun waje tayi ta zauna tana lumshe idanu tana mai sakin numfashi kadan-kadan kafun komai ya shiga dawo mata fuskar Farouq sai faman gizo take yi mata da wani irin yanayi mai tattare da damuwa a gareshi.
Da sauri ta buɗe idanuwanta sosai ta na mai bin falon da kallo ganin komai take kamar zai faru da gaske ba wai cikin baɗinan ce bane ba wata irin dokawa taji zuciyarta tayi da sauri ta kai hannunta ta dafe kirjinta tana mai runtse idanu tana buɗewa duk a lokaci guda.
Meke faruwa da ita har haka, me ya sanya al'amarin Farouq ke neman dakula mata lissafi mutumin da ya ci mata mutunci, ya faɗi mata kalamai masu zafi amma kuma ta kasa jin haushinsa yadda take jin sa a RAI DA ZUCIYA baya da alaƙa da fishi ko jin haushi.
Dube-dube ta shiga alamun tana neman wani abu kafun tayi shiro na dakiƙu dan ya tsanta guda cikin baƙinta cikin hanzari ta miƙe tayi hanyar ficewa daga falon
Motar ta ta nufa da sauri sai dai kuma an dauke ta daga in da tayi parking dafe kai tayi tana furta 'Yaa Rabbi!'.
Kafun ta dubi wajen dakin maigadi tana shiga kiransa da hanzari ya fito ya nufo gareta.
"Baba Sada..jiya na dawo bana jin dadi waye ya dauke mota ta daga nan?".
Gyaɗa kai ya yi cikin laɗabi ya sanya hannu cikin aljihunsa ya zaro Ƙey din motar ta ta yana mai faɗin.
"Subhnallah Hajiya Rabbi ya karo afuwa...ni na dauke ganin yanayin da kike ciki ya tabbatar mani ba lafiya ba".
"Ameen Yaa Rabbi Nagode sosai Baba Sada".
Ta faɗi tana mai amsar Ƙey din ta nufi wajan motar buɗewa tayi ta dauko jakar lapton dinta da wayarta sannna ta mai da ta rufe jin gina tayi da motar jin kanta ya fara sarawa kanta kadan-kadan sai da ta shafe daƙiƙu kafun ta buɗe idanuwanta ta nufi falon.
Zama tayi sosai tana mai duba wayarta Sakonnine rututu bayan kira buɗe bangaren kira tayi New-number ta gani sai number din Yaa jamaal shiru tayi tana mai duba lambobin biyu kafun ta fice ta koma akwatin sakwanni.
Nan ma dai sakonnine kamar yadda aka saba turo mata da boyayyiyar Number sai Yaa Jamaal da yake ta bata hakuri murmushi kawai tayi don ita kam tuni ta yafe masa.
'Ban san ta ina zan soma baki hakuri ba, ban san da wasu irin kalmomin zan fuskance ki ba, abu guda na sani nayi miki ba daidai ba wanda hakan ya faru sanadin KISHINA ina neman afuwa gareki ko zan samu sassaucin ciwu mai tsanani da ya kama zuciya da ruhina Da gaske nake son ki Ms Kutigi don Allah kar ki ce ba za ki dube ni ba' ki amshi bukata ta b....
Tun kafin ta karasa karanta sakon zuciyarta tayi wani irin tsalle da sauri ta mike idanuwanta awarwaje kanta taji ya yi mata wani gingirin gim kamar an daura mata dala da goron dutse runtse idanu tayi ta buɗe su tana mai sake duban sakon.
ESTÁS LEYENDO
MATAR MIJINA...Completed
Ficción General...Zuciyarta sosai take mikata wani mataki na firgici, ba ta shirya ansar wannan lamarin ba, lamarin da take hango cikin sa ba komai ba illa tashin alkiyamar duniyarta.Tana tsoron sake afkawa tashin hankalin rayuwa sosai take jin zuciyarta bata yi a...