25-MM.

220 16 0
                                    

Ƙwaba tayi tana mai dauke kata daga Nusaiba din zuciyarta take ji tana sake curewa waje daya da wani irin bacin rai mai girma gaske.

Komai take ji ya jagule mata duniyar gabadaya take ji ta hargitse mata lokaci guda.

Me Nusaiba take nufi? Shin da gaske abin da ya faru akan idanunta gaskiya ne Yaa Rabbi ita kam! tana cikin yanayi yau she har tayi SAKANI haka komai ke shirin dagule mata yaushe Nusaiba ta koma har haka ba tare da ta sani ba.

Mikewa tayi tana kai kawo tsakiyar kwanyarta take ji tana kokarin kamawa da wuta ga zuciyarta da take ta faman tsalle tsoro sosai ya bayyana a gareta wanda take jin sa har kasan ruhinta.

Numfashi ta ja ta fesar tana mai duban sashin Nusaib zuciyarta take ji tana sake hautsinewa ji take yi kamar ta taka har dakin Nusaiba din ta sake tadda ita taji dalilin ta nayin haka bayan...

Dafe kai tayi tunawa da tayi Nusaiba bata san halin da take ciki ba bata sai komai ke wakana ba ita kadai take kiɗinta tana rawar ta.

Yanzu me ya kamata tayi, me ya dace ace tayi? Tun kafin komai ya dakule mata.

Shiru tayi tana faman cizon laɓɓanta kafun ta buɗe baki tana huro iska waje cikin hanzari tana nufi dakinta cikin yanayi na rashin Tsammanin abin da zai ke ya dawo.

***

Sosai hawaye wanke mata fuska sai faman ɗauke su take amma kamar kara buɗe su ake yi da wani irin karfi.

Me Mami take nufi da ita ne, mai yas atake zarginta gane da Farouq ita ba komai yake tsakanin su ba...ta lura sosai Mami ranta ya baci ɓacin ran da bata taba ganin a ciki yadda ta girmama lamarin zuciyarta take ji kamar zata yo tsalle ta fito waje.

Ta rasa madafa ta rasa mi ma ya dace tayi al'amarin Mami sosai ya daure mata kai har ta kasa gane inda ta dosa.

Idan har Mami zarginta take da aikaita daidai ba a gaskiya tana cikin matsala ami girm awanda ta tabbatar Allah kawai zai fidda ita don ta lura da Mami in shekara zata yi tana karanta mata abinda ke tsakaninta da Farouq ba yarda zata yi ba.

Runtse idanu tayi tana jin maganganun Mami na sake samun gurbin zama cikin kwamyarta ji take yi kamar zata tarwatse..

'Me Mami ta gani cikin idanuwan Farouq?'.

Ta faɗi can kasar zuciyarta maganar tayi matukar tsaya mata a rai me take nufi da haka wasu irin abubuwa ta gani a idanunsa...ko da yake ita ma ta ga haka din don zuciyarta sosai ta shiga bugun sauri -sauri.

'Akwai abinda ke shirun faruwa tabbas akwai'.

Ta shiga girgiza kai yatsunta biyu ta tura cikin baki tana cizawa a hankali idanuwanta a runtse a hankali ta ja jikinta da ya gama yin sanyi sosai ta isa bakin gado ta zauna tana ma ajje numfashi mai kwari.

Wayarta ce ta fara rurin shigowar sako kallon wayar tayi kafun ta dauke kai sai dai kuma yadda zuciyarta take tunzura ta akan ta dauka taga me ne ne hakan ya danne duk wani halin-ko-in-kula da take ta kokarin nuna wa wayar.

Daukar wayar tayi ta buɗe sakon ɗan waye idanu tayi don dama tayin zaton ganin haka din rubutu take bi da kallo a hankali tana faman ya tsine fuska.

'Bana tunanin zuciyata zata iya hakuri game dake, bana tunanin rayuwa zata kasance cikin farinciki, ba tare dake ba. Burina a kullum ki amshi bukatata ki zame mani abokiyar rayuwa har gaban abada..don Allah Nusaiba'.
_FMK.

MATAR MIJINA...CompletedWhere stories live. Discover now