Daƙyar ta isa gida. Tun kafin ta kai wajan parking space ta kashe motar, tana haɗe kanta da sitiyarin motar wani irin yanayi take jin kanta komai take ji ya yi mata shiru kwakwalwarta ta tsaya cak! da tunani. Zuciyarta sai bugawa take da sauri-sauri kamar wacce tayi gudun ceton rai.
Sai da ta share mintina biyar kafin ta buɗe motar ta fito bayan ta kashe ta rufe, ta shiga taka kafafuwanta a hankali kamar kazar da kwai ya fashe mata a ciki.
Sosai take jin ciwo a zuciyarta, sosai take ji wani kalar tausayi game da ƴarta na danne mata duk wani gurbi na zuciyarta.
Anya tayi wa kanta adalci, anya tayi wa ƴarta adalci? Gani take kamar ta so kanta yanayin da ta ga Nusaiba aciki bai kamata ace ta barta haka ba, tana buƙatar taimako sosai tana buƙatar mai dubanta ya rarrashe ta domin ta tabbatar ba jindadin zaman auren take ba. Amma ya za ta yi ita bata so ace tana matsayin uwa ta kashe wa ƴarta aure ko ba a zage ta ba dole ta fuskanci fushi wajan Dr. Daɗin daɗawa ma Nusaiba ba ta bata karfin yin komai ba ta nuna mata ba komai ba kenan bata buƙatar ta san ko wani hali take ciki.
Gyaɗa kai tayi tana mai karasawa cikin falon. Lokaci guda ta ji zuciyarta ta doka tsalle ta dire Dr. ta gani zaune hannunsa riƙe da kofi mai ɗauke da Coffee a hankali yake kurba.
Kallon shi take cike da mamaki don bai sanar da ita yau zai dawo ba, wani irin abu ta ji ya sake danne mata jiki ta ko ina har kafarta take ji ta kasa ɗagawa. Kalar kallon da yake mata ya tabbatar mata tuhumarta yake yi wanda dama ta san a rina wai an saci zanim mahaukaciya.
Numfashi ta ja ta fesar kafin ta kau da kai daga kallon da yake yi mata. Ta kokarta ta ja kafafunta da sukayi mata nauyi ta isa cikin falon sosai ta samu waje ta zauna tana mai kwantar da kanta jikin kujerar idanunta a lumshe. Zuciyarta sai faman kai koma take tana hasko mata fuskar Nusaiba yanayin da ta ganta a ciki yana kara karyar mata zuciya.
"Jidda".
Kamar daga sama ta ji muryar Dr. cikin wani irin yanayi, buɗe idanunta tayi a daidai lokacin hawaye suka zubo mata zaune ta tashi sosai tana duban sa sam ba ta lura da hawayen da take ba wanda Dr. ya gansu tun kafin ta buɗe idanunta shiyasa ya yi mata kalar kiran da ya yi mata.
"Me ke faruwa ne haka, hawaye fa kike yi?".
Ya faɗi. Fuskarsa na kara bayyanar da maɗaukakin mamaki. A razane ta kai hannunta tana taɓa fuskarta jin ɗumin hawayen da gaske ya sanyata saurin goge fuskarta jikinta har rawa yake.
'Yaa Ilahi'.
Ta shiga nanatawa a zuciyarta tana mai kokarin saita kanta, kukan ya zo mata a bazata, bata taɓa zaton su ba amma yadda zuciyarta tayi rauni game da Nusaiba fiye da kuka ta san za ta yi Duka biyu ya haɗe mata ga rashin kirkin Farouq ga kuma yanayin da Nusaiba ta ke ciki. Girgiza kai ta shiga yi a hankali tana mai kokarin ɗaura murmushi mai kalar yaƙe a fuskarta.
"Jidda".
Ya sake furtawa izuwa lokacin muryarsa ta buɗe sosai idanunsa a saitin ta da kallon tuhuma.
"Dr. Ban san mi zance maka ba, amma da farko dai ina baka hakurin fitar da nayi ba tare da na kira ka na sanar maka ba".
Ta faɗi tana mai jan hanci, kafin ta fesar da huci mai zafi ɓacin ran da take dannewa yana bayyana kansa a fuskarta muryarta na kara buɗewa sosai da ciwon da take ji tun daga kasan zuciyarta.
Laɓɓanta ta tura cikin baki tana cizawa a hankali, mamaki gami da al'ajabi duk sun danne ta ta rasa ta ina za ta ɗauki zance ta sanar dashi ko mi ke faruwa.
"Gidan Nusaiba naje bata da lafiya, hankali na ne ya tashi sosai har ban samu kiranka ba na tafi".
Kallon da yake mata ta tabbatar nama ya dahu romo ɗanye, kasa tayi da kanta zuciyarta na sake ɗaukar zafi na ban mamaki sai yanzu take jin wautar ta na rashin ɗaukar mataki tun a gidan Nusaiba dama ta sani ta taho da ita. Amma kuma in da ta taho da ita ɗin a yadda ta tadda Dr. a gidan nan za ta sha mamaki wanda ba ta taba sha ba.
YOU ARE READING
MATAR MIJINA...Completed
General Fiction...Zuciyarta sosai take mikata wani mataki na firgici, ba ta shirya ansar wannan lamarin ba, lamarin da take hango cikin sa ba komai ba illa tashin alkiyamar duniyarta.Tana tsoron sake afkawa tashin hankalin rayuwa sosai take jin zuciyarta bata yi a...