33-MM.

279 22 2
                                    

Kallon kallo suka shiga yi wa junansu, yanayin fuskar Mami kawai zaka kalla ka gane kunci da takaicin da take ciki.

Laɓɓanta ta tura cikin baki tana cizawa kafin ta buɗe murfin motar ta fito ta tun karo in da Farouq yake tsaye kamar butum-butumi.

Zuciyarsa wata irin dokawa take yi kar zata fito daga mazauninta duk taku daya na Mami jin sa yake yi har cikin kwanyarsa runtse idanu ya yi ya buɗe su a lokaci guda yana kokarin kwato jarumta yana bayyanar da ita a fuskarsa don baya bukatar Mami ta lura da firgici da tsoron da yake ciki.

Numfashi kawai yake yi wanda yake jinsa kamar zai kwace masa.

Gabansa ta iso sai faman huci take kamar wacce za ta ci babu, Farouq da Maigadi gabadaya zuciyoyinsu zillo suke yi musamman mai gadi da firgicinsa ya bayyana karara a fuskarsa sai kyarma yake yi yana faman riƙe wandon sa.

Cikin tsananin ɓacin rai ta daga hannunta tanuna mai gadi dashi wanda ya sadakar zabga masa mari za tayi har ya hango kalar tashin hankalin da zai shi da sauri ya runtse idanunsa sai dai kuma maimakon ya ji saukar hannunta a fuskarsa sai yaji muryarsa taci ɗaci ta fara zazzaga masa faɗa.

"Hala idanunka sun daina gani ne, ko kuwa kunnuwanka sun kurumce da ba kasan abin da ya dace kayi ba in mutum ya dosa inda kake?".

Cikin ɓarin jiki da karkarwa baki ya shiga cewa.

"Kiyi hakuri Hajiya...".

Da sauri ta daga masa hannu tayi masa nuni da Get, kafin ta juyo cikin takun dake kara hargitsa duniyar Farouq. Bin ta kawai da idanu yake yi bai taba zaton za ta iso wajansa. A yadda take ba tare da ta yanke masa hukunci mai tsauri ba. Gyaɗa kai kawao yake yi zuciyarsa na sake narkewa da wani irin yanayi wanda ba zai ce ga kalarsa ba.

"Maigida dan matsa".

Maigadi ya katse masa tunanin da yake ta faman yi shi da zuciyarsa, da dan hazari ya dube shi kafun ya dubi Mami da take hakinmce cikin mota idanuwanta zube saitin Farouq sai faman numfarfashi take haka kawai take jin rashin dadi game dashi tun ranar da ta fara ganinsa IDO DA IDO take jin zuciyarta na ciwo.

Da hanzari Farouq ya matsa gefe ji da ya yi Maigadi ya fara tura Get din ita kuma Mami ta danno kan motar zuwa cikin gidan ta na zuwa saitin Farouq ta watsa masa wani irin kallo mai nuni da bana bukatarka a kofar gidana sannna tayi kwaɓa ta karasa shigewa cikin gidan maigadi ya maida get din ya rufe gami da yiwa Farouq Sallama don har lokacin jikinsa bai dawo daidai ba kuma ya fuskanci yanayin bacin ran Mmai yana da alaƙa dashi Farouq din.

Runtse idanu ya yi wani jiri yaji yana kokarin kwasar sa ya watsar  da sauri ya jingina da Get din hannayensa duk biyun dafe da kansa sai faman sakin wani numfashi mai ciwo a zuciya ykae duniyar gabadaya yake jin ta sake yamutse masa da ciwo mai tsanani wanda yake jin sa yana tsaga ko wani lungu da sako na cikin jikinsa yana gudana cikin jikinsa.

Ji yake yi kamar ya kurma ihu ko zai samu saukin daurin huhun goron da zuciyarsa tayi masa.

Baya jin zai iya barin kofar gidan nan ba tare da ya ga Nusaiba ba, baya jin zuciyaesa zata iya cigaba da motsawa a kirjinsa in har ba ganinta ya yi duniyar ciwo take haifar masa a duk wani abu na jikinsa ya rasa ya zai yi ya rasa me ya kamata ya yi?.

Bai san ya shafe lokaci mai tsayi a wajan ba sai da yaji buɗewa Get ya ga Maigadi ya fito da buta a hannunsa alamun Sallah zai yi bin sa ya yi da kallo kamar yadda shi yake bin sa da kallon mamaki.

MATAR MIJINA...CompletedWhere stories live. Discover now