Not edited
*****
Tafiyar Hayat daga gidan Nasreem, hakan ya bata damar zama domin tunano abin da take zaton ya kamata tayi akan zaman su da Farouq.Ita dai ta san bata taba kama Farouq da laifin waya da wata mace ba, balle tace kila wata ce ta ɗauke masa hankali. Sannan ita ko da suke kafun aure bata tunanin yana irin kule-kulen yan matan nan ba...amma kuma ta rasa gane mai yasa yake mata haka? ta rasa mai ya kawo rashin so a tsakanin su. Tayi zaton ko bai son ta, ai ya kamata ace ya nuna alkunya akan zumuncin dake tsakaninsu ya riƙeta. Amma ina! darajar zumunci ya kasa tasiri a tsakani.
Miƙewa tayi ta shiga kai kawo tana duban duk wani sashi na jikinta ita dai akaran kan ta bata ga wata maƙusa da take da ita da za ki sonta ba bata ga wani aibu a tattare da ita ba amma ta rasa mai yasa Farouq bai son ta ba.
****
'Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un' abin da tayi kokarin faɗi kenan can kasar makoshin ta runtse idanu tayi tana jin yadda zuciyarta ke buga cikin sauri-sauri sai da ta shafe sakanni a haka kafun tayi koƙarin buɗe idanu gami da juya tana duban saitin da Ya Jaamal ya domin kuwa gida kafun ta juyo ta dubi cikin harabawar wajan a hankali ta shiga taka kafafuwan tana jin yadda jikin ta ke amsa gajiya sosai.Kamshin da bata kaunar taji shi wanda ya kasa barin kofafin hancinta a ko yaushe tana jin sa.
Ji tayi zuciyarta ta sake matsewa waje daya a sa'ilin da taji kamshin na sake hauhawa gareta lokaci guda ta ayyanar da cewa 'Yana kuwa da ita' don haka tayi kokarin kau da fargabarta daga zahirin kan fuskarta ta bari cikin zuciya.
"Kutigi".
Sautin sunan jin sa tayi har cikin kwakwalwarta ya amsa amo duk da ta tabbatar da cewa ita ace ake kira amma ba ta bari hakan ya nuna kulawa a zahiri ba sai ma cigaba da tafiyar ta da take yi a cikin natsuwa da bugun zuciyarta dake sake likkawa.
Ba ta san yaushe zuciyarta zata daina damuwa da wannan al'amarin ba, ba ta san yaushe zuciyarta zata daina kwaso mata ko wani abu tana dauke mata a rayuwa ba, bata san wacce irin zuciya gareta ma kishin abu mai muhimmancin ba, komai nata ne wanda ya dace da wanda bai dace ba.
Ta kasa sanin yadda zata yi, ta kasa gane inda zuciyarta ta sanya alkibila.
Kallon yake yi sosai yanayinta na kara shagalar dashi har yana kokarin manta a ina yake zuciyarsa gabadaya ta gama tafiya a fannin ta bai san mai ya saka haka ba cikin awannin da ba fi su a lissafa da yatsun hannu ba su ba da kwanaki biyu zuwa uku komai ya kwance masa.
A duniyar sa daidai da tunanin sakan daya bai taba kawo wa kansa zuciyarsa zata rinjaye akan wata mace ba macen ma wacce ta zo aiki a karkashin sa irin Nusaiba Bukar Kutigi.
"Nusaiba ke nake ta faman zuba idanu na gani, ko alkawarin da kika yi mani ba zaki canza ba.".
Ya karashe yana sake buɗe idanuwansa sosai a inda take bai dan laɓɓansa sun yi masa wannan riga malama masallacin ba sai da yaji dirar kalaman nasa sannan ya fuskanci a halin da yake da sauri ya shiga gyarar murya mai kama da tari.
Kafun ya mike sosai daga jinginar da ya yi wa motarsa tasa.
Cak! Ta tsaya duk da bata so hakan ba, amma bata san mai yasa gangar jikinta suka tsaya da motsawa ba kafafuwanta suka kafe waje guda zuciyarta ta cigaba da motsawa da sautin kalaman da ta ji.
YOU ARE READING
MATAR MIJINA...Completed
General Fiction...Zuciyarta sosai take mikata wani mataki na firgici, ba ta shirya ansar wannan lamarin ba, lamarin da take hango cikin sa ba komai ba illa tashin alkiyamar duniyarta.Tana tsoron sake afkawa tashin hankalin rayuwa sosai take jin zuciyarta bata yi a...