16-MM

286 22 0
                                    

Numfashi Mami ta ajje karo na ba adadi zuciyarta na sake cure da fargaban abinda Nasreem zata faɗa mata don ta tabbatar wa kanta akwai wani  abu a kasa.

Gyaɗa kai tayi kafin ta kokarta faɗin.

"Ke nake sauraro Nasreem faɗa mani me ke faruwa na ganki da safiyar nan don na tabbata ba haka kawai za ki kwaso jiki raɓe-raɓe ki zo gida ba".

Numfashi Nasreem ta saki zuciyarta take ji tana sake yamustewa kaico! take yi wa kanta bata san ganganci da ya sanyata dauko jiki ta zo gida ba, ba ta san rashin tunanin da ya hau kanta har ta zo gida ba, to ayi mata me? Shin tace musu Faruoq baya sonta ko mi?.

Girgiza kai ta cigaba da yi ji take kamar ta yi tsintsuwa ta ganta a gidan ta sai yanzu take dana sanin baro gidanta...

Ta sani ko hauka take yi ba yadda za ayi ta buɗe baki ta faɗi abinda ke damun ta ya kamata ace ta koyi juri da dagiya game da Farouq. Bai kamata ace tun yanzu ta fara sare wa ba SO aka ce shi kuma ba a taba samun shi ta dadin rai in dai ba duk zuciyoyin biyu bane suke saukin begen junan su.

Ita kam ta san kaddararta ta fannin so dole tayi kokarin jajircewa ko ta samu abin da take so.

Mikewa take kokarin yi don ita dai bata san abinda zata ce da Mami ba.

"ki koma ki zauna ba cewa nayi ki tashi ba".

Ba ta zauna ba sannna ba ta nufi hanyar fita ba illa idanuwanta da suka kaɗa suyi jjair ta saukewa Mami.

"Mami ki yarda da abin da na faɗa miki shine gaskiya...".

Gyaɗa kai kawai tayi gami da murmushi don bata gasgata Nasreem din ba don ita kanta ba so take yi Nasreem ɗin ta faɗi mata abin da ke faruwa ba.

"Sai an jima Mami in Zaheeda ta fito kin faɗa mata na goɗe da abinda ta yi mani tunda kafafuwan a karye suke ba za ta iya zuwa ta duba ni ba bata ƙewata sai ni kadai nake kewarku".

Ta karashe tana kalato murmushi ta daurawa fuskarta mai cike da damuwa.

Mami ba ta ce da ita komai ba illa gyaɗa kai da tayi har Nasreem ta kai kofa tana kokarin buɗewa wasu hawaye masu zafi taji sun kawo mata farmaki da sauri ta saki kofar tana mai jin zuciyarta na kasuwa gida biyu.

'Shin kin gwanmace ki kashe kan ki sannna ki cigaba da zam ada mutumin da bai kaunar ki ko kadan mutumin da bai san darajar ki da kimar ki ba a matsayinki ta matarsa ta aure an ya kin yiwa kan ki adalci Nasreem rayuwar aure fa so da kyautatawa da tattali ake bukata daga wajan miji amma ke babu ko daya daga ciki illa tarin takaici da ciwon zuciya'.

Runtse idanu tayi tana jin yadda kalaman suke watsewa cikin kanta da gangar jikinta wani irin jiri taji yana kawo mata farmaki da sauri ta kai hannun ta turo kofar tana ficewa.

Sashin zuciyarta na biyu na sake karanton mata nashi zaɓin.

"Shin kin man ce wace ce ke, kon kin manta darajar da ki ke da ita a matsayin na ƊIYA MACE. ke fa kike da wuƙa da nama a hannunki sai yadda ki ka ga dama za kiyi dashi ya kamata ki sani duk rashin son da Farouq zai nuna miki ke ce kika ga dama hakan ta kasance ke ce za ki koya masa son ki kece za ki bi hanyar da zai buɗe zuciyarsa ya koyi son ki".

Hannu ta ka ta riko karfen dake zagaye da harabar falon ta runtse idanunta sosai kwanyar take ji tana kokarin kamawa da wuta ji tayi duniyar gabadaya ta hargitse mata.

MATAR MIJINA...CompletedWhere stories live. Discover now