"Nusaiba..".Tun kafin ya dasa aya taga masa hannu ta kama hanyar ficewa daga cikin Office din cikin yanayi na zafin rai muryarta a buɗe take faɗi,
"Tunda yin maganar ta zama dole a gareka to ni a wajena ba dole bane ba, bari n abar maka Office na san aɓin da kake so kenan".
Ta karashe tana murɗa Handle kofar tana ficewa da hanzari.
Binta ya yi da idanu yana fesar da wani zazzafar huci kafun ya haɗe hannayensa waje daya yana mai dukan iskan.Runtse idanu ya yi kafun ya buɗe su ya juya yana kokarin ficewa...kamar wanda aka kai ma idanu saman Table din ta ya hango phone dinta ajje wani murmushi ya saki kafun ya juya ya kalli kofar sannan ya maido da hankalin sa zuwa wajan table din ya doshi wajan gadan-gadan ya sanya hannu ya dauki wayar.
Wata irin ajiyar zuciya ya yi gami da lumshe idanu gabadaya jikinsa yake ji ya yi wani irin dadi zuciyarsa na buɗewa da wani irin abu mai girma.
Idanuwansa ya shiga yawatawa saman wayar wani murmushi na cigaba da samun gurbin zama.
Sreen din wayar ya taɓa haske ya bayyana murna ya yi sosai da ya ganta a buɗe ba tare da key ba.
Contant din ya nufa yana bincike sai kuma ya fice ba nan yake muraɗin shiga ba wajan Call ya nufa ya yi dailing din Number ɗinsa nan da nan yaji alamun t ashiga ta Ringing ba a dauka ba domin ya baro ta a Office din sa.
Katsewa ya yi gami da goge number dinsa daga wayar don kar ma ta gane anyi amfanu da ita ya maida ita mazauninta ya ajje sannan ya juya cikin hanzari ya fuce daga office.
Har ya bar wajan bai ga mai kama da ita direct office dinsa ya nufa yana shiga ya saki wata ajiyar zuciya da hanzari ya nufi inda wayarsa take ajje ya dauka tare da cire Key din ta Missed call din da ya gani ya sanya shi sakin dariyar da bai shirya ba yana bin number din da kallo.
Wani dadi da farinciki ne yaji sun samu gurbin zama a zuciyarsa ko ba komai ya samu Makamin da zai yi amfani dashi ta bayan fage wajan yaɗa al'amuransa yadda yake so ba tare da wani Shamaki ba.
Cilla wayar ya yi sama ya caɓe kafun ya ja kujera daya ya zauna yana mai yin baya da ita fuskarsa na kara bayyana murmushi mai girman gaske.
Haka kawai yake jin wani canji mai girma na samun sa a jikinsa yake jin komai kamar ya kasance yadda yake so zuciyarsa yake ji tana kara buɗewa da al'amarin tana kara bashi muhimmanci.
Mikewa ya yi ya nufi dan karamin firij din dake girke gefe guda ya buɗe Coke ya dauko mai rangomin sanyi sannan ya isa can gefe guda wajan loka din Table dinsa ya buɗe kwalin sigari ne da leta ya dauko sannan ya dawo ya zauna bayan ya ajje Coke din saman table din dake gabansa ya buɗe kwalin sigarin ya zaro kara daya ya zira tsakanin laɓɓansa yana rikewa da su.
Letar dake hannunsa yake bi da kallo kafun ya kyasta wuta ta kawo ya kai saitin bakinsa yana kokarin doɗawa sigarin yaji motsin taɓa kofarsa idanuwansa ya juyar da su zuwa wajan yana bin kofar da kallon haka kawai yake jin wani iri a zuciyarsa da sauri ya janye letar daga saitin sigarin ba tare da ya dora mata ba.
Sigarin na maƙale a laɓɓansa ya shiga wasa da ita har zuwa lokacin idanuwansa na saitin kofar jira yake yi ya ga mai shigowar amma har tsayin dakiƙu hakan bai kasance ba.
YOU ARE READING
MATAR MIJINA...Completed
General Fiction...Zuciyarta sosai take mikata wani mataki na firgici, ba ta shirya ansar wannan lamarin ba, lamarin da take hango cikin sa ba komai ba illa tashin alkiyamar duniyarta.Tana tsoron sake afkawa tashin hankalin rayuwa sosai take jin zuciyarta bata yi a...