MM-74

144 20 2
                                    

"Farouq".

Nasreem ta faɗi, tana miƙewa saman kafafuwanta, da take jin su wani iri a jikinta kamar za su kayar da ita. Numfashe take ja a hankali har ta isa gabansa tana kallon idanuwansa da suke faman buɗe kansu suna rufewa, wani irin yanayi take ji a zuciyarta bugun ta na sauyawa da wani abu mai kama da tashi hankali, lokaci guda ta ji jikinta na ɗaukar rawa ta ko ina laɓɓanta ta shiga motsawa a hankali.

"Farouq mana...".

Daga mata hannu ya yi yana mai saukewa don ji yake gabaɗaya gaɓoɓinsa sun yi masa wani irin sanyi na ban mamaki, ba don a jikinsa yake jin su ba zai iya rantsewa ba nasa bane yake amfani da su wasu ne aka canza masa.

"Ki bar ni Nasreem...kaina ciwo yake. I need to rest".

Wani irin dokawa taji zuciyarta tayi, har sai da ta kai hannunta ɗaya tana dafe kirjinta, don ji tayi kamar zuciyarta za ta faso kirji ta faɗo kasa. Rufe idanunta ta shiga yi tana buɗewa, gani take kamar ba Farouq ɗin ta ba, gani take kamar a sauya mata shi, idanunsa a cikinsu akwai wani abu da take hangowa, yake sanya zuciyarta matsewa a mazauninta, tsoro gami da fargaba take ji suna dire mata lokaci guda, kwakwalwar ta take ji tana ɗaukar ɗumi sosai.

Gyaɗa kai ta shiga yi kawai tana mai dubansa, har ya karasa shigewa ɗaki yana bugo ƙofar, bugun da taji kamar an ɗauki guduma ne a buga tsakiyar kanta zuwa cikin zuciyarta, runtse idanu tayi tana buɗewa lokaci guda wani irin yanayi take jin kanta a ciki, nauyi na ban mamaki take jin kanta ya ɗauka gaɓoɓinta take ji sun yi mata wani iri, ƙokarin taka kafafuwanta tayi, amma taji sun mata nauyi sosai.

Duban Batool tayi, wacce dukkan abinda suke yi, a idanunta. Wani kwantaccen murmushi ne ke ta safa da marwa a fuskarta, zuciyarta na sake wassafo mata wani abu da ta jima tana maƙale dashi a karkashin zuciyarta, a yanzu take jin cewa lokacin tabbatarsa ya yi, a gangar jikinta da zuciyarta take jin damar ce ta zo a yanzu, kuma tabbas za ta dama ta yadda take so, domin kuwa yanzu lokacinta ne kambun da ta jima tana muradin murɗa shi lokacin murɗashi ɗin ya yi, tabbas za ta shirya domin yanzu za ayi wasan.

"Ban san mi ya yi saura ba, da har kike sanya wa kan ki damuwa game da Farouq. An wuce lokacin da za ki zauna ki damun kan ki, a wuce wannan lokacin Nasreem. Farouq a tafin hannunki yake sai yadda kike so za ki yi dashi, amma gabaɗaya kin ruɗe. Shiyasa tun farko nace wasan nan ba za ki iya shi ba...".

"Batool".

Nasreem ta tare ta da wani irin yanayi a muryarta, kafin ta kaɗa idanuwanta da suka kaɗa sukayi jajir, laɓɓanta ta tura cikin baƙi tana cizawa kamar zata ɗauke su daga mazauninsu, kafi tayi ajiyar zuciya mai ƙwari, tana ƙarasawa ta zauna gami da jingina kanta da kujerar da take kai idanuwanta a lumshe.

"Batool ina jin wani iri a zuciyata, wani abu nake ji mai nauyi yana danne mijin dukkan sassan jikina, da gaske ina son Farouq. Canjin da na hango cikin idanunsa, ina jin yana taɓa min dukkanin jijiyoyin jikina".

Wani irin kallo Batool take mata, kafun ta miƙe kan dogayen takalmar dake ƙafarta, tana mai ɗaukar jaƙarta ta riƙe hannu.

"Ki cigaba da son sa Nasreem, ban hanaki ba, amma kina gaf da komawa gidan jiya in har baki shiga hankalin ki ba".

Buɗe idanunta tayi, ganin Batool tsaye hakan ya sanyata ware idanun nata sosai ta shiga dubanta ɗauke da mamaki a fuskarta.

"Hmm...har yanzu kin kasa fahimta ta Batool...".

Wani murmushi Batool tayi, wanda hakan ya sanya Nasreem tsagaita maganarta, tana mai dubanta da wani irin yanayi murmushin fuskarta take ji yana mata wani iri a zuciya. Lumshe idanu tayi tana buɗewa, ƙafun ta mike tsaye itama.

"Ba karaya nayi ba, sannan ba son sa bane ya takura ni, Mahaifiyarsa...Batool ita nake jin wani iri game da ita".

"Abu mai sauƙi ne ai, in ta kawo miki shamaki, illa iyaka ki yasar da ita gefe guda ƙaramin alhaƙi ce gareki. Domin kice mai wuƙa da nama a hannu sai yadda kika yanka kika baiwa mutum zai amsa ba tare da ƙorafi ba".

MATAR MIJINA...CompletedWhere stories live. Discover now