31-MM

243 19 0
                                    

Wani irin nauyi taji zuciyarta tayi, numfashin ta sai yayyakewa yake yi amma duk da hakan bai hana ta cigaba da kukan ba kukan da take jin sa kamar na fitar rai ciwo,zugi, raɗaɗi ba wanda ba ta ji yadda zuciyarta ke ya mutsewa ji take yi kamar duniyar gabadaya ake kokarin rabata da ita.

Kafarta da ta zauna akai taji ta amsa da wani irin kara kamar ta karye runtse idanu kawai tayi hawaye na sake sintiri a fuskarta.

Komai taji ya dakule mata, ta rasa me ma ya kamata tayi, zata iya cewa ta fi kaunar mutuwar da rayuwa a filin duniyar nan don jin kanta take tamkar GAWA DA RAI.

So take yi ta rasa komai nata so takeyi ta ko yanayin da kowa zai raɓu da ita ko za ta samu sassacin ciwukan da suke ta yayyage mata filin ZUCIYA DA RUHI.

Shafe fuskarta tayi ba wai don ta tsayar hawayen ba don ta tabbata sunn fara zuwa kenan sun kulla ABOTA kenan wanda bata san ranar kwance ta ba.

Miƙewa tayi jikinta ko ina rawa yake yi kanta jin sa take kamar dai raɓe gida hudu ga zafi da ko wani lungu da saƙo na jikinta ya dauka karasa tayi sosai cikin toilet ta cire duk kayan dake jikinta ta isa gaban shawa ta sakar wakanta ruwa.

A hankali ta shiga ajjiyar zuciya zuciyar da har zuwa lokacin bata sassauta daga nauyin da tayi ba saukar ruwan kawai take ji a fatar jikinta sanyin na zama a nan kawai ba wai yana ratsa mata cikin jiki ba yadda ta bukata amma ko hakan ta samu sassauci na fatar jiki amma bana gurbin zucciya ba.

'A dalilin son ki Nusaiba'.

Dafe kunnuwanta tayi jin yadda kalaman ke amsa kuwa cikin kanta da ma toilet din gabadaya ji take yi kamar tai ta kurma ihu amma ta kasa harshenta ji take yi kamar an saka ƙwaɗo an datse haka laɓɓanta wani irin mugun nauyi taji sun mata wanda ta kasa motsa kawai rawa suke yi kamar wadanda aka jonawa shock na wuta.

Jiri taji yana kokarin kwasar a hankalin ta durkushe wajan tana mai riƙe kanta sosai duniyar take ji tana juya mata gabadaya furucin Farouq sai kara hauhawar sauti yake yi zuciyarta kuwa sai tsalle take duk da nauyin da ta yi mata sosai da sosai.

Sai ta shafe mintina masu dama kafun taji komai ya fara sassauci miƙewa tayi ta dauki Tawul ta daura a jikinta kafun ta dauki wani ta lullube kanta dashi.

A hankali ta shiga taka kafafuwan da take jin su kamar roba ta nufi hanyar fita bakinta dauke da addu'o'in neman sauki daga Rabbi shi kadai ne dai iya kawo mata waraka a rayuwarta shi kadai yake kallon matsalolin da jarbatar dake filin rayuwarta ta sani rayuwarta kace kam tana cikin jarabawa mai girma ALƘAMIN ƘADDARA shine ke zano mata komai wanda ya kasance TUN FIL'AZAL sai kasance cikin haka.

Da wannan yanayin ta fito gefen gado ta zauna ta zagba tagumi tana duban kanta saitin Mirrow dake gabanta yanayi da ta ga kanta a ciki ta tabbatar ba karamin yanayi mane maras dadi take ciki.

"Hasbulallahu wa ni'imal wakeeel!!'.

Abinda take ta furtawa kenan tsakanin laɓɓanta hawayen na sake kwaranyo mata.

Kwankwaso kofar taji an yi duban kofar tayi kafun ta dauke kamta na yan daƙiku sannan ta mike ta nufi ma'ajiyar kayan ta bude ido ta kurewa wajan kafun ta ja wani numfashi tana mai jin ranta na kara jagulewa Hijab ta janyo ta zare tawul din dake kanta ta zura sannan ta koma ta zauna bayan tayi kokarin danne hawayen da suke zubo mata ta goge fuskarta.

MATAR MIJINA...CompletedWhere stories live. Discover now