MM-42.

110 17 2
                                    

Sun jima cikin shiru, an rasa wa zan yiwa wani magana. Dr. Bukar abubuwa da yawa sun ɗaure masa kai game da al'amarin Nusaiba, sannan yanayin da ya ga Mami a ciki abin ya kara shigar dashi cikin duhu.

Gyaɗa kai kawai yake yi yana faman shafar kan Nusaiba cikin alamun rarrashi. Ita kau sai kara narkewa take yi a jikinsa, nishin ta na kuka na kara bayyana.

"Ya isa haka".

Ya faɗi yana mai sanya hannu ya ɗago haɓarta idanuwanta yake duba, sosai abubuwan da yake gani a cikinsu ya tabbatar masa akwai matsala.

Tun kwanakin baya yake lura da abubuwan gidan sun canza game da Nusaiba. Sai dai a waccen lokacin ya ta'allaka hakan ne da zazzaɓin da ta yi fama dashi, da kuma Sa'insar da yaji suna yi game da aikin na Nusaiba bai ɗauki abin da girma ba.
Sai dai a yanzu ya lura akwai wani boyayyen al'amari da bai sani ba a gidan nashi, wanda yake kokarin cinsa da yaƙi ba tare da  ya sani ba.

Lokaci guda ya ji zuciyarsa ta ɗau dumi sosai. Ya shiga girgiza kai ya tabbata komai ke faruwa to mai girma ne, musamman yanayin da ya ga Nusaiba a ciki. Don abin da bai taɓa faruwa bane a gareta bayyana damuwa.

Tana da ZURFIN CIKI sosai komai zai faru da ita har tayi ta gama damuwarta ba a sani, in ba wai abun ya yi tsamari bane ko kuma Jamaal wanda ya kasance shaƙiƙi wanda Shaƙuwa mai girma take a tsakaninsu, har yake iya karantar ta a duk lokacin da wani abu yake faruwa da ita kamar yadda ya faru a yanzu.

Miƙewa ya yi gami da riko hannun Nusaiba ya nufi cikin falon da su, kujera daya suka zauna kafin ya dubi Jamaal dake tsaya kamar wanda aka dasa sai faman bin Nusaiba yake yi da idanu.

"Haɗa mata wani Tea, naga alamar wannan ya yi sanyi".

Ba musu ya ɗauki baban Mug dake jere akan Table ɗin, ya shiga haɗa Tea mai kauri kafin ya buɗe flast ya zuba mata soyayyan dankalin turawa da kwai ya ɗauko ya nufo in da suke har lokacin idanunsa ba su bar kan Nusaiba ba.

Dr. da kan shi ya amshi Mug din da farantin dankalin, ya dubi Nusaiba fuskarsa da murmushi da kansa ya shiga ɗiba zai bata, dauri ta kau da kai tana mai yin kasa dashi hakan da ya gani ya sanya shi murmusawa.

"Yanzu kunya kike ji Nusaiba?. wato kin girma kenan yanzu ba za ki iya zama na baki abinci ba".

"Abba kawo ka gani".

Jamaal ya faɗi yana mai amsa ya zauna gefen ta, yana mai dubanta itama dubansa take yi. Da idanu take masa alamu ya daina bata so kunyar Abbanta take ji, amma yadda ya haɗe rai ta tabbata korafinta bai amsu ba.

Haka ya shiga debo dankalin da cokali yana bata ba yadda ta iya, haka ta buɗe baki yana saka mata tana taunawa a hankali. taunawa take amma ji take kamar tana tauna maɗaci sai sai ba yadda za tayi dole taci, in ba haka b kuma laifi ne mai girma zai shiga tsakaninta da Yaa Jamaal ɗinta, ita kuma abin da ba za ta yarda ba kenan ya faru don sai abun ya yi mata yawa shege da hauka.

Haka ya cigaba da bata, tun tana ci har taji bata da in da za ta saka abincin a cikin ta. rau-rau tayi da idanu kamar za ta yi kuka hakan ya sanya shi barinta, amma ya tabbatar mata sai ta shanye Tea ɗin da ya haɗa mata tas! in bata son ganin fushinsa haka kau tayi.

Dr.Bukar dake gefe su faman gyaɗa kai yake yana faman murmushin jindadi, yadda ya ga Jamaal na kula da ƙanwar tashi ya tabbata ko ba su raye shi da Jidda,  tabbas Nusaiba ba za ta yi kuka akan rashin iyaye ba, ba za ta yi korafi akan rashin jigon rayuwa matallafi ba.

"Nusaiba".

Dr.Bukar ya kirata cikin yanayi na rashin wasa a muryarsa, hakan da Nusaiba ta ji ya sanya kirjinta bugawa ta dube shi da sauri. kamar yadda shima Jamaal ya dube shi don ya tabbata akwai muhimmin abu da zai faɗi.

MATAR MIJINA...CompletedWhere stories live. Discover now