A ranta take jin ta shirya wa dukkan wani kalubalin da zata fuskanta. Za ta jure duk wani yakushi ko cizo gami da duka in har zata samu abin da take muradi.
Tana ji a ranta akwai ganganci mai girma, game da wafutar da soyayyar Farouq daga zuciyarta A tunaninta zata iya shanye duk wani tarnaki da zuciyarta za ta zo mata dashi, don ta yarda da batun son Farouq. Amma sai ta ga rauninta ya yi yawa, zuciyarta ta rigaya tayi zurfi mai girma game da soyayyar Farouq ba ta da wani zaɓi illa ta amshi lamarin da duk yardarta.
Bata taɓa so ba, bata san ma ya ake son ba. Ita kanta ta sha mamaki in ta ga mace ta kamu da son namiji, tana kokarin zautuwa. Ta ɗauki haka a matsayin rashin ciwon kai, ashe abin da bata sani ba, ba wai gangar jiki ko rai bane suke da alhakin kamuwa da so, ZUCIYA ce da wannan martaɓar gami da iko wajan assasa son a cikinta ta yarda da cewa.
'So yana samuwa daga zuciya ba wai gangar jiki ba'.
Ta tabbatar da hakan. Ta yadda ta kasa Ƙwace zuciyarta daga soyayyar Farouq, ta yarda ta kuma yi AMANNA cewa son Farouq take, so mai tsanani wanda take jin sa yana gudana a duk wata jijiyar jikinta zuwa cikin jini.
Numfashi ta sauke tana mai sake yin juyi saman gadon da take, agogo ta kalla ta ga karfe daya har da rabi na dare, amma ji take yi kamar ta na farar safiya karfe takwas sabida rashin jin barci idanunta sun yi kemadagas! alamu ba su da niyyar barci.
Murmushi take yi lokaci lokaci tana kara tabbatar da cewa SO daban yake, ba yadda ba ya zuwa ga mace ko namiji ta yarda da hakan kuma ta amince.
Miƙewa tayi zaune sosai, tana mai lankwashe kafafuwanta kamar mai shirin cin tuwo. hannayenta ta tallabe haɓarta da su idanuwanta na buɗe, fuskarta na bayyanar da wani irin lallausar murmushi zuciyarta take ji tana kara buɗewa tana bayyanar da wani gurbi mai girma, abubuwa ma su zuzuta kwakwalwa da ruhi gami da girmama zuciyata take ji suna saukar mata da wani irin sanyi, mai kama da sanyin sanyayyen lambu mai cike da furane masu kamshi da kyautata jindadin DAN'ADAM wanda ya kasance cikin DUNIYAR SO.
Wayarta ta janyo daga jikin caji ta cire gami da buɗe sashin ma'ajiyar Audio, abubuwan dake ciki take ta dubawa sai dai duk babu abin da take bukata a ciki, kokarin ajje wayar ta yi sai kuma ta fasa bayan tayi dan tunani na dakiƙu. Da hanzari ta buɗe Data gami da nufar sashin Youtube ta shiga Seaching din waƙar fi ɗin SANAM TERI KASAM. tun kwanaki ta ji wasu yan mata na maganar film ɗin bayan ta je wani Bookshop binciko wani littafin INSIDE AREWA wallafar Muhammad Abubakar (KingMoh).
A nan ta jiyo yadda yan matan suke zancen film ɗin da yadda aka zuba soyayya zallar ta mai taɓa zuciya, sai dai abin da ya tsorata ta yadda ta ji suna faɗin ai jarumar mutuwa tayi abin ya yi matuƙar tsaya mata a rai duk da kallace kallace ba damunta ya yi ba, amma sunan Film ɗin ya tsaya mata a rai sosai da sosai.
'Ashe zai min rana'.Ta faɗi a ranta wani murmushi mai girma na kara bayyana saman fuskarta, ta cigaba da Seaching sunan film ɗin nan ta ga wakoƙin film birjinta duk da bata ji take ba, haka ta kunna Videos din daya bayan daya tana bin su da kallo ba waƙar da ta fi burgeta sai wacce Masoyan suke a kasuwa yanayin da yadda suke a waƙar ta ji ya taɓa mata zuciya sosai, sai ta ji DAMA A CE ita da Farouq ɗin ta ne.
juya tayi gami da jawo filo ta rungume a kirjinta, tana mai lumshe idanu. Imagine take da jaruman tamkar ita da Farouq ne suƙe cikin wannan yanayin, za ta so haka ta tabbata yadda ta hango tsantsar kaunarta a idanun Farouq zai nuna mata kulawa fiye da haka.
**
Misalin karfe Bakwai da rabi Barrister Jidda ta fito cikin shiga ta alfarma, sai tashin kamshi take. Hannunta riƙe da babar jakarta sai kuma Rigarta ta lauyoyi da hula da ta riƙe a dayan hannun.Gilashin dake fuskarta ta gyara wa zama, tana mai duban Nusaiba dake Dinner tana faman cakuɗe abinci fuskar nan ta ta cike da fara'a.
Shiru tayi tana kara nazartar yanayin ta, tana jin wani irin abu a zuciyarta game da murmushin fuskar Nusaiba, ta tabbatarwa kanta akwai wani abu a kasa. yaushe rabon da Nusaiba da walwala irin haka tun lokacin fara aikin ta da BKC.
YOU ARE READING
MATAR MIJINA...Completed
General Fiction...Zuciyarta sosai take mikata wani mataki na firgici, ba ta shirya ansar wannan lamarin ba, lamarin da take hango cikin sa ba komai ba illa tashin alkiyamar duniyarta.Tana tsoron sake afkawa tashin hankalin rayuwa sosai take jin zuciyarta bata yi a...