Yanayin ta ka dai in ka kalla zai tabbatar maka a firgice take idanuwanta sai faman yawo suke yi cikin mazaunan su hannayenta harɗe waje daya kamar mai neman alfarma zuciyarsa na faman lugudan duka ji kawai take ta ji hukuncin da Yaa Jaamal zai yanke a kanta don ta tabbatar ba zai yafe ba dole sai ya yi hukunci.
Fuskarsa...yanayin da take gani a fuskarsa hakan ya tabbatar mata komai zai mata ba sauki bane tunda take zata iya rantsewa Yaa Jaamal bai taba yi mata kallo mai dauke da hukunci ba kamar na yau zuciyarta taji ta sake tsinkewa.
Ji tayi Duniyar ta sake ya mutse mata sosai kai kawo ta cigaba da yi cikin dakin motsi kadan in taji sai gabanta ya yi mummunar bugawa don tunaninta shine ya shigo.
Bai iya ɓacin rai ita ta sani, sosai yake da zafi tun kafin ma ya fara aikin Soja balle yanzu da yake da wannan aikin wanda ta tabbatar komai zai karu ba raguwa zai yi domin soja ba imani gare shi ba...
"Nusee!"..
'Innalillahi wa inna ilaihir raji'un'.
Abin da ta ji zuciyarta na faɗi kenan lokaci guda duk wani sashi na jikinta ya tsaya cak! da aiki jira kawai take ji me zai faru da ita.
"Waye shi ban san shi ba, ban taba ganinsa ba?".
Ya faɗi cikin wata kwantacciyar murya mai amo a hankali yake takowa har ya iso gaf! da ita ya harɗe murɗaɗɗun hannayensa a kirji idanuwansa a kanta.
Mutsu mutsu ta fara kamar wacce tayiwa sarki karya ake tuhum gabadaya ta kasa idanu dashi wani irin nauyinsa take ji ya lullubeta.
"Kawai amsa nake so Nusee ba komai zan miki ba".
Ta gefen idanu ta dube shi caraf! ya kamata da nashi idanun da sauri tayi kasa da kai.
"Farouq Ma'arouf Kutigi".
Shiru ya yi yana jujjuyawa sunan da ta faɗi a kwanyarsa haka kawai yaji wani irin abu mai nauyi ya dire masa akai girgiza ki ya shiga yi kafun ya numfasa.
"Waye shi?".
"Yaa Jaamal mana".
Ta faɗi da muryar rigima don bata san yadda zata sanar dashi waye Farouq ba ta tabbata duk yadda zata nuna masa waye shi ba zai yarda ba.
Haka kawai taji tana zargin kanta ba wai Ya Jaamal kadai yake zargi ba har da ita ma.
"Ina kika san shi mana Nusee amsa nake so".
Dago idanunta tayi da ƙyar ta dube shi kafun ta nisa.
"Am...acan wajan da nake aiki yake...wai dama...".
"Enought!!".
Yana faɗin haka ya juya ya fice daga cikin dakin ba tare da ya sake kokarin cewa da ita komai ba. Wani goron numfashi ta ajje tana mai zama bakin gadon nata ta tallaɓe haba.
'Kar ki manta dani!'.
Ihun kalaman Farouq taji lokaci guda sun yi mata dirar miƙiya akai runtse idanu tayi wani irin sarawa taji kanta ya yi da sauri ta dafe goshin nata tana furta.
YOU ARE READING
MATAR MIJINA...Completed
General Fiction...Zuciyarta sosai take mikata wani mataki na firgici, ba ta shirya ansar wannan lamarin ba, lamarin da take hango cikin sa ba komai ba illa tashin alkiyamar duniyarta.Tana tsoron sake afkawa tashin hankalin rayuwa sosai take jin zuciyarta bata yi a...