MM-54

131 24 3
                                    

"Barka da safiya".

Ta faɗi da wani irin yanayi wanda ta kasa tantace shi. Shin kishi ne ko tausayin Nasreem take yi? Ta kasa gane komai ta kasa fahimtar komai sosai kanta ya kulle duniyar take ji tana cakuɗe mata a dakiƙu.

Ba ta taɓa zaton za ta ga irin wannan al'amarin ba a rayuwar aurenta. Bata taɓa zaton a cikin kwana daya za ta gamu da ɓacin rai ba a gidan aurenta, zaton farinciki za ta ci karo dashi tun ranar da ta tako da sunan matar aure a gidan Farouq, ko kadan bata kawo wa kanta samun matsala ko damuwa nan kurkusa ba a gidan auran ta. Ta san ba zallar farinciki bane, ta san ba ko yaushe ake samun abin da ake muradi ba, amma ba ta kawo a kwana daya zata ga kalar wannan rayuwar a gidan Farouq ba.

'Anya kuwa ba tayi ganganci ba?'.

Ta faɗi a zuciyarta tana mai saurin girgiza kai bata so tun yanzu ta fara kalar tunanin nan, bata so a irin wannan lokacin ta ji a ranta za ta sare ba ta shirya ko kadan bata shirya ba, ko a mafarki bata hangowa kanta kalar rayuwar nan ba.

Nishi tayi tana kara duban Nasreem.wacce take raba kallonta tsakanin ita da Farouq a idanunta take hango wani abu mai girma yana narkewa wanda ta kasa gane menene sai dai zuciyarta ta fi zargin so ne na Farouq wanda bai samu gurbi mai kyau ba.
"Amarya".

Ta ji sautin muryar Nasreem ya dire mata cikin kai da wani irin yanayi da ya sanyata runtse idanu tana buɗwa  tana shiga gyaɗa kai tausayi ne ko kishi ta kasa fahimta yadda take ji a zuciyarta game da Nasreem ɗin.

Murmushi Nasreem ta shiga yi tana mai takowa gaban Nusaiba da wani irin yanayi. Takun Nusaiba take ji yana saukar mata cikin zuciya yana haifar mata da tsoro da fargaba ba wai tsoro ita Nasreem ɗin ba a,a tsoron yanayin da ta ganta a ciki da ku irin abun da ta hango cikin idanuwanta sosai take ji ya samu gurbin zama cikin zuciyarta.

Gabanta ta iso sosai tana mai gyara zaman jakar dake kafaɗarta a rataye. Atamfa ce a jikinta mai kalar ja da baki anyi mata dinkin riga da siket sosai ɗinkin ya amshi jikinta ya nuna tsantsar dirin da Allah ya yi mata.

'Ta fi ki komai'.

Nusaiba ta ji wani sashi na zuciyarta na faɗin haka. Gyaɗa kai tayi domin ita kanta ta san haka ɗin Nasreem kyankyawa ce ta ko wani sashi ita kuma baƙa ce, sai dai hakan ba ya nuni da ta na jin ta karaya bane don hakan ko kadan ba zai razana ta ba.

"Amarya...ban san mi zan ce miki ba, amma ina miki albishir da cewa kin yi gangancin auren mutum irin Farouq".

Ta faɗi da wani kwantaccen murmushi a fuskarta, wanda take ji yana haifar mata da ciwo mai girma cikin zuciya kawai juriya ce ta riƙe ts amma ba don haka ba, ba abin da zai hanata rushewa da kuka.

Dafa kafaɗar Nusaiba tayi tana mai kokarin kara bayyanar da murmushin ta, kafin ta mai da kallonta ga Farouq da yake ta faman huci kamar zai ci babu tsantsar ɓacin rai da takaici sun bayyana fuskarsa karara, kallon Nasreem yake ji yake kamar ya cafki wuyanta ya makure ta har sai ta daina numfashi ya watsar da ita tsakiyar falon nan.

Ko kadan bai son ko ganin fuskarta wani irin ciwo yake ji yana kokarin kekketa masa zuciya, tsanarta yake ji na kara girma da faɗi a zuciyarsa ko kadan bai jin akwai kalar tsanar da ya yiwa Nasreem a filin duniyar nan don a ransa yake ji zai iya soƙe ta da mashi ya turbuɗata cikin garwashi wuta mai tartsatsin.

"Ban hango miki farinciki a rayuwarki dashi ba, ban hango miki wani kalar jindadi ko da kamar da kwayar zarra ba a tare dashi..."

Takun sa da ta ji ya sanyata tsagaita furucinta, wani irin tsoro ne mai girma take ji yana danne mata duk wani kuzarinta duk wani yunkuri da take ji za tayi amfani dashi wajan nuna wa Nusaiba iyakarta game da Farouq lokaci guda ta ji yana rushewa, zallar son sa dake daskare a zuciyarta take ji yana hudowa. Runtse idanu tayi don ba ta jin za ta iya ko tsayuwa ne in har ya iso inda take.

MATAR MIJINA...CompletedWhere stories live. Discover now