'Matar Mijina'.
Sunan take ji yana sake, shayar da ita ruwan mamaki, gyaɗa kai ta cigaba yi kafin ta saukewa hannunta daga tagumin da ta zabga har zuwa lokacin idanunta na saitin Nusaiba. Ganin ta take yi kamar ba ƴar ta ta ba gani take kamar an canza mata ita, komai nata ya sauya yanayin ta halittar ta duk sun sauya.
Wani ɗaci take ji yana taso mata tun daga ƙasar zuciyarta har saman harshenta yana bada wani ɗanɗano da take jin sa kamar zai ƙekketa mata harshen.
"Matar Mijinki?".
Mamai ta faɗi da wani irin yanayi a fuskarta. Kafin ta gyara zamanta fuskarta na bayyanar da wani fushi mai girma fatar goshinta har kara tattarewa take idanunta na ƙanƙancewa.
Gyaɗa kai Nusaiba tayi kirjinta cigaba da bugu da sauri-sauri yanayin fuskar Mami ya tabbatar mata komai zai iya faruwa fushin ta mai girma ne a duk lokacin da tayi sa abubuwa sosai marasa dadi ke faruwa rayuwa na ɓaci.
"Kina Nufin Kishiyarki ce, kina nufin ita ce Matar Farouq ɗin kuke zaman kishi da ita, kina nufin kalar wannan zaman kuke tun da kika shigo, kina nufin Daraja da ƙima duk baki da ita a idanunta, kina nufin bora kika koma a gidan?".
Tsoro ya sake ziyartar Nusaiba, yadda sautin muryar Mami ke fita da zurfi gami da ɓacin rai ji take yi ko ina na jikinta na rawa, wata fargaba mai girma da abinda zai faru take shakka, ta tabbata Mami sai tayi yunkurin ɗaukar mataki akan haka kata kau ba za ta so haka ba, idanunta ta ji sun tara kwalla a hankali tayi kokarin mai da su kafin ta dubi Mami kallon da take mata ya tabbatar cewa nama ya dahu romo ɗanye, amma duk da haka ba ta fasa neman mafita ba.
Hannayenta ta shiha haɗewa waje daya tana murzawa a hankali laɓɓanta suka shiga motsawa so take yi ta ce wani abu amma ta rasa ta ina za ta fara, bata so Mami ta fahimci komai bata so ta gane akwai wani abu a ƙasar zuciyarta da take boye mata. Numfashi ta ja ta sauke.
"Ba da gangan tayi ba Mami, kuskure...".
Wani mugun kallo Mami da yi mata da hakan ya sanyata yin shiru da baƙinta ba shiri tana mai kau da kanta daga kallonta.
"Kuskure fa kika ce?. Ta ya ya kuskure ya fito a nan ɗin. Faɗa min ta yadda kuskure ya fito. Shin bangajeki da tayi ta so ki faɗi ki karye ko kuwa rashin kunyar da ta yi min. Faɗa min cikin abubuwan nan wanne ne kuskure sannan wanne ne ta aikata da gangan?".
Hucin numfashinta da ke bugun fuskarta ya taɓɓatar mata Mami ta ɗau zafi da lamarin, don haka ta tsuke bakinta dom ta tabbata ta sake yinƙurin faɗin wani abu tsaf! Mami zata kai mata bugu duk da yanayin tausayi da ta hango cikin idanunta.
Miƙewa Mami tayi tana duban Nusaiba fuska ɗaure.
"Tashi mu je?".
Miƙewa tayi ba shiru duk da bata jin in wani abu Mami zata aikata za ta biye mata dole ta nuna mata ƙi akan hakan.
"Mami kiyi hakuri da gaske na faɗa miki kuskure ne".
"Ai ba ce miki nayi ban yarda ba, so nake na tabbatar da kuskuren, kisan ni bana ɗaukar zance daga sama sai naji yadda aka haihu a ragaya".
Numfashi ta ja ta sauke idanunta a rufe, kafin ta buɗe tana mai bin bayan Mami da kallo wacce har ta kai ƙofar fita daga ɗakin.
Wani Tsoro ta ji ya dire mata zuciya lokaci guda, kafafuwanta taji suna koƙarin yasar da ita. In har ta bari Mami ta fice daga ɗaƙin hakan na nufin tonuwan asirinta, ita kuma ba za ta so haka ba, ba za ta so ko kadan Mami ta fuskanci kalar zaman da take cikin gidan Aurenta ba.
Wata jarumta ce ta ji ta zo mata, da saurin ta ja kafafuwanta da suka yi mata nauyi ta nufi ƙofar ɗakin da sauri.
Gaban Mami ta sha idanunta da yanayi na kwalla.
YOU ARE READING
MATAR MIJINA...Completed
General Fiction...Zuciyarta sosai take mikata wani mataki na firgici, ba ta shirya ansar wannan lamarin ba, lamarin da take hango cikin sa ba komai ba illa tashin alkiyamar duniyarta.Tana tsoron sake afkawa tashin hankalin rayuwa sosai take jin zuciyarta bata yi a...