Ciwon da take ji cikin zuciyarta, har bata san ya za ta kwantanta shi ba. Duniyar take ji kamar tana matsewa da ita cikin yanayi na azaba da raɗaɗin dake fitowa daga karkashin zuciyarta.
Ta rasa mi za ta yi, ta rasa me ya kamata tayi. Kwakwalwarta da zuciyarta gabaɗaya jin su take fayau kamar takarda. Ba abinda yake nukurkusarta illa ciwo mai girma da yake kara samun gurbin zama a ko wani sashi na zuciyarta.
Wani numfashi mai tsananin zafi ta ajje kafin ta dago hannunta tana goge fusƙarta da take ji kamar gumi ne yake tsantsafo mata.
"Da gaske ban shirya ba, ba yanzu ba Nusaiba don Allah".
Wani sashi na kalaman Farouq taji sun sake dire mata cikin kai lokaci guda suna sake rikita mata guntun lissafin da take ta faman kokwawa dashi.
Hawaye taji suna jiƙa mata fuska, ba sabbi bane don ba yanzu suka fara bayyanar mata ba, a da tayi alkawarin cewa ba za ta fara zubda hawaye a gidan auren ta da wuri haka ba amma ta lura hakan ganganci da rashin lissafi tayi wa kanta, a zaton ta za ta iya jurewa zata iya shanye duk wani kalubale amma sai ta ga abin ba mai yuwuwa bane dole ta canza lissafi ta fara karyata kanta.
Hannunta ta kai tana shafar matashin cikinta ɗan wata hudu wanda ta ke jin ƙauna da son sa na ratsa duk wani magudanan jini da ke gudana a jikinta wata irin kauna ce zalla wanda bata taɓa jin kalarta ba tana saukar mata game da cikin tana son shi har ƙasar ranta.
Gyaɗa kai tayi hawayen na sake ɓalle mata. Wai ita ce zata haihu, ita ce zata zama uwa, ita ce ɗa zai tsaga jikinta ya fito ta shayar dashi a matsayin mahaifiya gareshi.
Murmushi ya ƙwace mata ta lumshe idanu wani irin so na sake sarƙe mata zuciya sai dai wani sashin cinkushe yake da takaici da baƙin ciki.
Gyaɗa kai kawai take tana jin rigimar Farouq na dawo mata game da cikin dake jikinta.
"Nusaiba ki dube ni ki bani amsa".
Dago kai tayi da wani irin yanayi wanda ta kasa tantace shi bata san mi zata ce da Farouq ba, bata san ya zata ɗauki kalamansa ta ɗaura su a mizanin hankali har suyi wani tasiri ba sosai take jin ciwo mai tsanani a zuciyarta kalamansa da ya furta mata take jinsu suna ƙekƙeta mata zuciya.
"Bana son shirun nan Nusaiba".
Ya faɗi yana mai takowa inda take zaune bakin gado sai faman gumi take kamar wacce ta haɗiyi kunama ita kadai take jin tashin hankalin da take ciki, ita kadai ta san yadda duniyar ke cakuɗe mata a cikin wannan mintin da ba su fi biyu ba.
Hannunta ya riƙo cikin nashi duk da yana jin wani iri cikin kansa ga wani irin abu mai kama da harbin kunama yana dire masa a hannu wanda yake ji kamar daga tafin hannun Nusaiba ya ke fitowa runtse idanu kawai yake zuciyarsa na faman turiri da wani irin kuncin wanda shi kansa ba zai ce ga dalili ba.
Tunda Likita ya furta masa kalmar juna biyu ya ji gabadaya duniyar ta hautsi ne masa ya rasa me ke yi masa dadi a duniya daga lokacin ya rasa duk wani hope da yake zaton yana dashi da zai miƙe ya je ya sami Nusaiba ya rungumeta a jikinsa ya nuna mata tattali da kulawa ita da abinda ke cikinta wanda ya ke jin zai zamo gudan jininsa na farko a duniya.
Sai dai hakan ya garara wani irin ihu yake ji cikin kansa har ma da zuciyarsa ana nuna masa ƙin wannan halittar da ya kasance shi da Nusaiba suka kasance silar samuwarsa wanda ya kamata ace sun nuna masa kauna amma sam ba ya jin haka.
Numfashi ya fesar mai zafi, kafin ya dago ya dubi Nusaiba.
"A zubar...Don Allah kar ki ce min a,a".
Ya sake maimaitawa. A karo na biyu yana jin kalaman na masa ɗaci a saman harshensa amma ya rasa dalilin da ya sanya ya kasa ƙwatar kansa daga barin aikata hakan.
YOU ARE READING
MATAR MIJINA...Completed
General Fiction...Zuciyarta sosai take mikata wani mataki na firgici, ba ta shirya ansar wannan lamarin ba, lamarin da take hango cikin sa ba komai ba illa tashin alkiyamar duniyarta.Tana tsoron sake afkawa tashin hankalin rayuwa sosai take jin zuciyarta bata yi a...