MM-60

129 18 7
                                    

Da wani irin yanayi take kallonsa a idanunta, zuciyarta take ji tana kara curewa waje ɗaya gami da bayyanar da wani rikitaccen ciwo mai kokarin danne duk wani kuzari da ya yi sauran a jikinta. Tana jin gangar jikinta kamar ba ta ta ba,ta rasa ya za ta kwatanta ciwon da take ji a zuciyarta, tana fatan Allah ya sauƙaƙa wa duk wasu bayi nasa masu ɗauke da ciwon zuciya don ta tabbata ciwon zuciya ba karamin tashin hankali da fita hayyaci yake saka mai shi ba. Nata ba za ta kirashi da ciwon zuciya ba, zata bashi suna a matsayin kuncin zuciya wanda yake samuwa ta sanadin cutuwa ko samun kai a damuwa ba tare da shiryawa ba.

Gyaɗa kai kawai take tana jin yadda zuciyarta, ke kara nakewa da ciwon da take jin sa a ko ina cikinta. A hankali ta kai hannunta tana ɗauke gumin da take ji yana tsantsafo mata a goshi duk da yanayin sanyi ne amma ita gumi take yi wanda ta rasa gane da ga ina yake fitowa kuma na menene.

Numfashi ta sauke so take yi ta ce dashi wani abu amma ta kasa laɓɓanta sun yi mata nauyi sosai, a hankali ta juya tana kokarin barin wajan kafafuwanta take ji sun mata wani irin nauyi wanda ta tabbatar ba wai sun mata hakan bane ta sanadin cikin dake jikinta ba.

"Me haka ke nufi, ba magana za ki gasa min ba, ki faɗi mana ina sauraron ki".

Ya faɗi da wata irin murya mai cike da tsana da fushi, yana mai zura hannayensa cikin aljihun wandon sa laɓɓansa yake turawa cikin bakinsa yana cizawa a hankali yana saki, fuskar nan tashi tayi kicin-kicin kamar hadarin dake kokarin zubda ruwa a ko wani lokaci.

Taji zafin maganarsa musamman yadda take jin sautin muryarsa na haifar mata da kasala mai tafe da ciwon kai, bata son kula shi a yadda take jin kanta a yanzu in har tace za ta ce dashi wani abu to tabbas ba za ta musu dakyau ba su duka.

"Ki faɗi abinda ke tsakanin laɓɓanki, nusaiba ki faɗi".

Ya sake maimaitawa cike da tsawa a muryarsa hakan ya sanyata kai hannunta tana toshe kunnuwanta da take ji kamar suna barazanar fashewa

"Bana so Farouq, ka daina min ihu a kai, muryarka zata fasa min kai".

Ta faɗi ko ina na jikinta na rawa hannunta sai yawo suke tsakanin kunnuwanta da kanta da take jin suna wani irin yanayi wanda ke kokarin firgita mata komai da komai nata.

Kallonta yake yi yana jin wani abu mai kama da tsana na ratse masa cikin rai ji yake kamar ya shaƙo ta ya murɗe mata bakin dake faɗa masa magana cikin daga murya.

"Ni kike dagawa murya, Nusaiba ni?".

Ya faɗi yana mai takowa inda take tsaye cikin karkarwa. Hannu ya kai ya shaƙo wuyan doguwar rigar dake jikinta ya cukuikuyeta waje ɗaya idanunsa cikin nata da suka kaɗa sukayi jajir.

"Sake daga mun murya Nusaiba, nace ki sake daga mun murya zan baki mamaki sosai za ki sha mamaki akaina".

Kiciniyar kwatar kanta tayi don a cikin idanunsa take hangowa zai iya rabata da numfashinta ba imani a zuciyarsa ko kadan, ba ta shirya barin duniyar nan ba so take ta kalli Farouq da idanunta hannunta ɗauke da jaririn da zai tsaga jikinta ya fito ta kalle shi ya kalle ta faɗa masa magana za ta so haka burinta kenan ta tabbatarwa Farouq rai da numfashi nata da na abinda ke cikinta za su rayuwa ko ba saka hannunsa za ta nuna masa cewa bai isa ba ya yi kadan ya tarwatsa mata rayuwa ya yi kadan ya rabata da GUDAN JINInta dake kwance a cikinta.

Wurgi da ya yi da ita ne gefe guda har tana buguwa da kujerar dake kusa da ita hakan ya sanyata katse tunanin da take dubansa tayi zuciyarta take ji tana dakewa bata bukatar kuka don bata bukatar Farouq ya ga rauninta jarumta take buƙata a yanzu. Don haka ta miƙe duk da amsawar da bayanta yake amma bata bari ya gane tana jin ciwo ba. Kallo ɗaya tayi masa ta ɗauke kai ta nufi sashinta tana cogala kafarta da ta ji ta rike.

MATAR MIJINA...CompletedWhere stories live. Discover now