MM-89

89 14 5
                                    

BAYAN WATANNI BIYAR.

Tunda suka baro gidan su Hayat yake fama da Mashkur game da yadda ya ɓata jikinsa da alawa da yake ta faman sha gaban motar ya yi masa kaca kaca. In ya ɗauki wannan ya tsotsa sai ya ajje ya ɗauko wata ya buɗe ya tsotsa ya sake ajjewa duk lokacin da Jaamal ya yi kokarin ƙwacewa nan zai shiga ihu da kururuwa kamar wanda ake ƙokarin zarewa rai.

"Kasan Allah Mashkur ban sake zuwa da kai tunda ba ka jin magana".

Ya faɗi a karo na ba'adadi hankalin na tukin da yake daidai kwanar da za ta kai su gida.

Amma Mashkur ko a jikinsa sai ma wata alawa mai tsinƙe da ya ɓare bayan ya tsotsa ya nufi bakin Jaamal da ita.

"Buɗe".

Ya faɗi yana turbuɗe fuska. Duk ɗaure fuskar da Jaamal ke yi sai da ya fashe da dariya yana duban fuskarsa yanayin yadda ya ci mur kamar wani babban mutum ga fuska dame dame da ɗankon alawa.

"Ni ba za ka ɓata min jiki ba. Ka matsa min da ita...".

Sai dai kafin ya rufe bakin sa tuni Mashkur ya saki alawar a jikinsa fararen kayansa wata irin zaɓura ya yi saura kaɗan sitiyarin ya ƙwace masa don bai yi tsammanin haka daga Mashkur ɗin ba.

"Sai na faɗawa Ammi ayat gobe".

Ya faɗi yana komawa ya zauna gami da ɗauke kansa shi an masa laifi.

Dubansa Jaamal ya yi kafin ya girgiza kai. Bai san ina ya koyi rigima da fushi ba tunda baƙinsa ya fara buɗewa da iya magana shikenan al'amarin rashin jinsa ya kara buɗe su kamar dama jira suke bakin ya buɗe.

"Ba sai na ƙi ɗaukar ka a motata ba in zan tafi".

Da sauri ya juyo yana ɗage masa gira gami da ware idanu.

"In ce Mami ta kira Anty Ayat ta zo ta ɗauke ni a motar ta".

"Ita ma ba za ta zo ba".

Sake haɗe rai ya yi kamar zai fadhe da kuka. Har maigadi da Jaamal ke wa horn ya buɗe suka shiga ciki. Yana tsaida motar ya shiga kiciniyar buɗewa ya fita shi a dole an ɓata masa rai. Jaamal murmushi kawai yake masa har ya fita ya buɗe masa ya fito ɗauke da ledar alawarsa a hannu ya nufi hanyar falo yana tafiya da kafafuwansa da ba su gama ƙwari ba.

Jaamal na masa magana amma ya ƙi kula sa.

Tura ƙofar falo ya yi Jaamal na biye dashi. Mami suka tadda zaune da yake weekend ne sallamar Jaamal ta ɗauke mata hankali daga littafin da take duba ta dube shi ta cikin madubin idonta kafin ta dubi Mashkur wanda ya je ya raƙume cikin kujera yana faman turo baki gaba.

"Shi wannan akun me akayi masa yake ta faman turo baki gaba?".

"Wai fa Mami daga kawai nace ya daina ɓata jikinsa da alawa shikenan aka ɗau fushi dani aka daina min magana".

Jaamal ya faɗi yana samun waje ya zauna fuskarsa da dariya.

"Eh lallai saraki. Ki da yake ban ga laifinsa kai ka sangarta shi yaron nan ka dube shi kƙ shekaru biyu bai cika ba wai amma ya san ya ɗau fushi da mutane da shaggun idanunsa a tsaye kamar kwan tsaka".

MATAR MIJINA...CompletedWhere stories live. Discover now