"La'ilaha Illa'anta Subhanaka Inni kuttu minal Zalumin".
Kalaman dake ta faman yawo tsakanin laɓɓanta kenan, idanuwanta da suka bayyanar da yanayin tsoro da razana sai faman yawatawa suke cikin ɗakin ta ko ina, numfashi take ja a hankali tana ajje wa ga wani gumi na rashin dalili dake ta faman tsantsafo mata a goshi hannunta guda ta sanya tana gogewa kafin ta fesar da huci tana mai sake buɗe idanunta sosai cikin ɗakin.
Wani tsoro mai girma take jin yana sake samun gurbin zama cikin zuciyarta, a idanunta take hango mafarkin da tayi na faman dawo mata a hankali kamar yanzu take yin shi, tsoron ne dai ke sake nunnukuwa fiye da wanda taji a lokacin da ta farka a firgice daga barcin da take.
Hannunta ta kai gefen gadon wayarta zaro daga caji ta lalubo lambar Nusaiba tana kokarin kira sai kuma ta tsaya tana kallon agogon wayar wanda ya nuna karfe biyar da rabi. Numfashe ta ajje, bata jin za ta yi barin gari ya waye abinda take ji a zuciyarta da mafarkin da tayi a barcin ya yi matukar tsaya mata a rai sosai take tsoron abin da ta gani ya tabbata duk da ta san mafarki ba gaskiya bane amma yadda zuciyarta ke kara bawa mafarkin wajan zama a cikinta hakan ya yi mugun tsorata ta.
Bata san me yasa ba, a da tayi kokarin danne zuciyarta game da auren Nusaiba, ta daina damun kanta akan abinda take jin akan auren, tayi hakuri ta ɗauki auren Nusaiba da Farouq a matsayin Muƙaddari daga Allah wanda tuntuni Alkalamin ƙaddara ya rubuce auren sai ya tabbata a tsakanin su bata da iko ko wata dama na hanawa. Amma a cikin watannin nan tana yawan mafarkin Nusaiba na rashin dadi tana kokarin danne komai ta boye ba tare da ta nuna wa Dr ba don ta tabbata ba abinda zai ce da ita illa saka abin a rai da tayi bayan kuma ta masa alkawarin dai na damun kanta.
Tayi iya bakin kokarin ta wajan danne wa amma abin ya gagara har sai da ta same shi da zancen yawan mafarkin da take yi game da Nusaiba ɗin.
"Ai in har za ki kasance mai saka abu a ranki, ki kwanta dashi dole ya kasance sahun farko wajan zuwa miki cikin barci, mafarki da kike gani mutum nayinsa mafi yawanci mutum na kwanciya da abin ne a ransa sai ya kasance ya yi tasiri cikin barcin sa. jidda ya kamata ki daina damun kan ki game da al'amarin Nusaiba ko tambayar ki akayi akan mi kike Shakka akan auren nan ba ki da dalili, ya kamata ki cigaba da yi mata addu'a...shiyasa ki ga naƙi yarda ki je gidan don bana son zuciyarki ta kasance cikin shakka a ko yaushe don na tabbata ki ka je ko ya kika ga wani abu da bai gamsar dake ba zaki ɗauke shi ki saka a ranki a matsayin makami wajan kara rura wutar abin da kike ji tun farko game da auren nan".
Kau da kai tayi, don ba haka ta so ba. ta so ace ya fahimce ta amma ya ƙi so tayi ya bata damar zuwa ta dubi yar ta ko ta samu sauƙin shakkar da ta ke ita kanta tayi tun da ta fara mafarkin nan. Ta san mafarki ba gaskiya bane amma akwai wanda yake tabbata a zahiri.
"Dr. Ba wai nace ka bar ni naje gidan auren Nusaiba bane. Nima ba zan fara ba in ba da wani kwanƙwarar dalili ba, yau watan ta ɗaya a gidan miji ya kamata ace ka bani dama ko gaisuwa ne naje muyi ko na samu sauƙin abinda nake ji a zuciyata".
Kallon ta ya yi sosai yana faman gyaɗa kai kafin ya murmusa idanunsa na kara buɗewa a kanta. ya fuskanci Jidda akwai tsoro a tattare da ita kuma har da shakka da take akan auren Nusaiba tun farko ya haifar mata da haka yasa ko ya ya ne ya fahimtar da ita amma zata fahimta ba.
"Jidda mana. Ya kamata ki cigaba da yi wa ƴar ki addu'a ba ki yi ta sanya shakka a zuciyarki ba, ban so zuciyarki ta tabbatar miki da cewa jindadi Nusaiba ta je yi a gidan auran ta ke kan ki kin sani auren gabaɗayarsa ba jindadi bane duk wanda yace aure jindadi ne to ya yi masa muguwar fahimta kiyi hakuri ki cigaba da yi mata addu'a".
Miƙewa tayi tana kokarin barin ɗakin nasa, ya riƙo hannunta don yadda damuwa ta bayyana a fuskarta ya tabbata zuwa zata yi ta tai zabga tunani.
"Bari na kira miki ita a waya. In kika ji muryarta na san zuciyarki zata samu natsuwa".
YOU ARE READING
MATAR MIJINA...Completed
General Fiction...Zuciyarta sosai take mikata wani mataki na firgici, ba ta shirya ansar wannan lamarin ba, lamarin da take hango cikin sa ba komai ba illa tashin alkiyamar duniyarta.Tana tsoron sake afkawa tashin hankalin rayuwa sosai take jin zuciyarta bata yi a...