Lokaci guda ta ji wani tunanin ya zo mata, da hanzari ta mike tayi sashin dakinta, ta canzo kayan dake jikinta daga kanana zuwa doguwar riga baƙa sai karamin mayafin ta yane kanta dashi.
Makullin motarta ta dauka gami da wayarta ta fice daga cikin falon ta na isa harabar gidan motar Maami na ficewa laɓɓata ta ciza gami da gyaɗa kai cikin haushi da takaici ta lura kowa baya kaunar Nasreem tunda har za su kasa tsaya su ji halin da take ciki ita kam ba za ta yarda yar uwarta ta kasance cikin uƙubar Ɗa-namiji ba.
Da wannan zantukan ta shiga motar ta ta bayan Maigadi ya buɗe mata get ta finciki motar da karfi kamar wacce za ta tashi sama.
Gudu take yi sosai tunda ta bar Estate din nasu kamar zata tashi sama zuciyarta sai matsewa take yi waje daya da yanayin damuwa da halin da Nasreem din take ciki.
Bata san ya zata tadda ita ba duk da ta ji haushin mata a sheƙaran jiya da ta je gidan nata taƙi biyo ta hakan ba karamin ɓata mata rai ya yi ba sai dai ba za ta iya fushi da halin da yar uwar ta take ciki ba.
Cikin mintina da ba su haura talatin ba ta isa unguwar da Nasreem take tana shanyo kwana ta hangi motar Farouq ta fito daga cikin gidan wata iri dokawa ta ji zuciyarta tayi da karfi har sai da ta runtse idanu kafin ta buɗe tana bin motar tashi da wani irin kallo na tsantsar haushi da takaici.
Taka burki tayi har ya iso inda take ta cikin gilashin motar suka shiga duban juna da wani irin yanayi fudkar Farouq dauke da murmushi mai nuni da cewa na raina hankali kafin ya kau da kai ya figi motar ya bar wajan.
Numfashi ta sauke kafun ta daki sitiyarin tana mai juya kadan ta dubi bayan motar tashi kafun ta ja motar jikinta da wani irin yanayi mai kama da kasala haka kawai take jin ranta da zuciyarta na fargaba da Farouq amma kuma wani sashin yana kara mata jarumta akan tunkarar Farouq din alkawari ta daukarwa kanta sai ta kwatar wa 'yar uwarta 'yancin ta.
Da wannan tunanin ta isa a bakin get din ta ajje motarta ba ta shiga da ita ba gaisawa sukayi da Maigadin kafin ta nufi cikin gidan zuciyarta na dokawa a hankali da kuma fargabar yadda za ta taddo 'yar uwar ta ta.
Da sallama ta tura kofar falon ta shiga ba kowa a cikin sa ya y tsit hakan ya tabbatar mata da Nasreem na sashin dakin ta da hanzari ta miki hanyar da zata kai ta sashin zuciyarta na sanar da ita wannan zuwan da tayi Nasreem ko taƙi ta so sai ta fitar da ita daga wannan gidan.
"Nasreem!".
Ta shiga faɗi tana tura kofar dakin bata tadda ita ba ta shiga bin dakin da kallo kafun ta shiga ciki sosai ta samu waje bakin gadon ta zauna don tunaninta ya bata kila Nasreem din na cikin bandaki ne.
"Zaheera".
Nasreem ta faɗi tana mai binta da kallo kafun ta karasa daga bakin toilet da take tsaye murmushi kwance a fuskarta sai dai kallo daya za kayi mata ka gane halin damuwa da kuncin rayuwar da take ciki.
Bin ta kawai tayi da kallo kafun ta dauke kai ta jin ciwo take yi yana taso mata tun daga zuciyarta ya zo kirji ya tsaya cak! yana sakar mata raɗaɗi da zugi sosai da sosai.
"Heera mana!".
Nasreem ta faɗi tana zama kusa da ita ganin yadda ta nuna halin-ko-in-kula a gareta.
Riko hannunta tayi ta sarƙe da nata tana faman murzawa a hankali ita kuwa Zaheera sai kokarin kwace take amma ta kasa.
"Am so sorry...".
YOU ARE READING
MATAR MIJINA...Completed
General Fiction...Zuciyarta sosai take mikata wani mataki na firgici, ba ta shirya ansar wannan lamarin ba, lamarin da take hango cikin sa ba komai ba illa tashin alkiyamar duniyarta.Tana tsoron sake afkawa tashin hankalin rayuwa sosai take jin zuciyarta bata yi a...