Page Twenty Six

463 50 8
                                    

👨‍✈️ *CAPTAIN MUZAMMIL* 👨‍✈️

Written by *Zeeneert*

*Zeeneert*@wattpad

*Page Twenty Six*

*Two Weeks Later*

Tafiya suke atsakiyar tsungurmun daji,babu karar dakakeji a motar sena taka ciyayi da buge bishiyoyin karage da Mallam Hashimu driver ketayi and he couldn't think of anything than yayi resigning aikinsa gun oga insuka samu suka koma gida lafiya. In ada da kasa take zaune Lafiya Lau yayima Hajiya wannan aikin toh yanzu bazai iyaba dan baishirya jefa rayuwarsa cikin garari ba yabar iyalinsa cikin damuwa. Yanda yanzu ake yayin kidnapping da kashe kashen mutane inbanda rashin Imani da rashin sanin ciwon kai mezaisa Hajiya tasasu shigo wannan tsungurmun dajin dazumar zuwa gun boka.

Shidai sanda tasameshi da zancen dandai kawai bashida yanda zaiyi ne sannan dashi kadai tasaba zuwa gun wannan harkar seyanzu daya gansu a tsakiyar dokar dajin yake sake ganin wautarsa,what if besamu komawa gida bafah? Yazaiyi da rayuwarsa? Yazaiyi da iyalinsa? And most importantly mezaije yaceda ubangijinsa tunda bawai besan inda suke zuwan bane kuma yake kaisu which clearly means shima yanada nashi kwamason. Haka dai yacigaba da driving din yana sake sake aransa tareda addu'ar Allah yakaisu lafiya yamaido dasu lafiya yayi bankwana dawannan aiki hakanan yanaji Khadija dake zaune bayan motar kanta nata gwaruwa da kofofin motar tana masifar yarage gudu itaduk jikinta yafara ciwo sabida buguwan datayi dakuma sama da kasa dataketayi.

Mahaifiyar ta tace "Babu laifin Mallam Hashimu anan,haka hanyar take kuma tunda kika dage sekin auri Sojan nan dole kiyi enduring,ni shekara da shekaru nayi inazuwa gurinnan kuma bantaba daga hankalina ba dan na bugu tunda Inna koma gida duk wasu bukatuna innasamu in biya so kema haka zakiyi hakuri" Khadija dai batace komai ba sema tura baki gaba datayi aranta tana ayyana aiduk Muzammil ne yajaza mata. Da ace yadaga wayarta peacefully bezo yayi blocking dintaba daga karshe daduk bata gamu dawannan walahar ba anma bakomai,yabari burinta yacika yashigo hannunta. Duk seta fanshe wulakancin daya mata.

Seda sukayi tafiyar kusan awa guda kafin suka iso gaban wani dan dutse marar tsayi sosai, parking Mallam Hashimu yayi yayinda Hajiya da Khadija suka sauka a motar suka fara tafiya da kafa,dutsen sukaje suka hau dakyar dan kafafun Khadija seda suka zame kusan sau uku kafin tasamu ta iya hawa dutsin duk jikinta yayi butu butu me Mallam Hashimu zaiyi inba dariya ba dukda halin tsoro dayake ciki aransa yana fadin "Allah shikara".

Koda su Khadija sukahau kan dutsen hango NAKAN TUDU tayi zaune karkashin wata yar bishiya me duhuwa dakekan dutsen. Batasan sanda takawar dakai gefe ta tsirtar da yawu ba tana yatsine fuska,daman wannan ne NAKAN TUDUN? Lallai jinsa yafi ganinsa dan ita wallahi bata taba kawowa ranta haka yakeba dayake bata taba zuwa gurinsaba,sede suji Hajiyarsu na hirarsa da irin aikin dayake Mata sekuma suma suka samu,insuna da damuwa kowata Yar matsalarsu dagudu zasuzo su sanar da Uwartasu kan taje musu gun NAKAN TUDU. Yanzuma abunda yasa tabiyo mahaifiyar tata gani take kamar za'asamu wani alternative din anma mahaifiyar taki fada Mata sabida batason alakarta da Muzammil ashema babban kazamine,kallo daya zakama muhallin dayake zaune,kayan jikinsa dakuma yanda hakwaransa sukayi ka gane hakan.

Dukda dajine wasu Yan tsirarrun kudaje take gani suna yawo kusa dashi da kayansa,Dakyar ta seseta fuskarta suka karasa gaban bishiyar. Bude baki tayi zatayi sallama Hajiya tayi sauri ta damke hannunta alamar karta yi kafin tajata suka zube gaban NAKAN TUDU kamar wasu masu neman gafara tana fadin "Allah yaja da tsahon rai NAKAN TUDU" NAKAN TUDU yace "Amin Meke tafe daku?kuma wace bakuwace kika tahomin da batareda kin sanar dani ba?" Hajiya dake damke da hannun Khadija harlokacin suna zube gabansa tace "Ya'ta ce ayimin afuwa" NAKAN TUDU yace "Wacce aciki?" Hajiya tace "Khadija,wanda nazo nasameka da batun tanason Sojan can kwanaki" NAKAN TUDU yajinjinakai yana kallon Khadija cikeda gamsuwa yace "oh wanda mukace takawo Mana sautin muryarsa lokacin da baya cikin tsarki?" Hajiya tace "Eh itace NAKAN TUDU" NAKAN TUDU yace "Toh Yaya akeciki? Muryar takawo Mana?" Khadija dakejinsu girgizakai tayi ahankali tace "Bansamu nadauki muryartasa ba NAKAN TUDU. Baya daukan wayana Inna kira daga baya ma yazo yayi blocking dina gaba daya" NAKAN TUDU yace "Kicanza layi kikirashi mana" Khadija tace "Nayi harsau uku amma duka baya dagawa NAKAN TUDU. Ina tunanin yana amfani da Truecaller ne kawai in akwai wata dubarar bayan wannan ataimaka ayi shi inaga zaifi sauki" NAKAN TUDU yace "Babu,ai na fada ma mahaifiyar ki tun lokacin datazo wannan ne kadai hanyar dazamu iya samu muyi nasara akanshi inkuma bahakaba sede a hakura. Yarone me matukar addini,kullum cikin tsarki yake hakanan iyayensa ma basuzauna haka kawai ba so samun galaba akan irin wadannan mutanen yanada matukar wuya gaskiya" Khadija kamar zatayi kuka tace "Yanzu yazanyi?" NAKAN TUDU yace "zuwa zakiyi kicigaba da jaraba wancan din watakila ayi sa'a yadaga wayar a irin wannan lokacin wataran inyaso seki kawo Mana muryarsa muyi aikin dashi" gyadakai Khadija tayi jiki sanyaye ayayinda Hajiya taciro damin kudi cikin Jakarta ta ajiye agaban NAKAN TUDU,take yashiga washe hakwaransa dasuka gama canza kala zuwa brown yahau godiya.

CAPTAIN MUZAMMILWhere stories live. Discover now