👨✈️ *CAPTAIN MUZAMMIL* 👨✈️
Written by *Zeeneert*💕
Zeeneert@wattpad
*Page Thirty Eight*
Hajiya Naja'atu tace "Wallahi kuwa" Hajiya Sarah cikeda jimamin abun tace "Ikon Allah. Nikuma kinga koda wasa bantaba tunanin zai iya zama shine ba bare inmiki maganar" Hajiya Naja'atu tace "aidayake ma bamu taba zancen sunanshi dakuma inda yake aikiba shiyasa bazaki taba wannan tunaniba" Hajiya Sarah tace "Aikam dai. toh yanzu yaza ai?ashe mukam da suruki muketa adawa bamu saniba?" Hajiya Naja'atu tayi dariya tace "Mekuwa za'ayi Sarah? Aibabu abunda za'a fasa sedema hada hannu dazamuyi mu taimaki juna inkowa tashi ta gagareshi shikadai dukdama bahakan muke fataba" Hajiya Sarah tace "kinko kawo shawara mekyau Hajiya. anmadai mugwada jaraba shawara damuka yanke din tukun suma su Alhajin suyi nasu. In ba asamu mafita ba se anemi wani alternative dinda zaiyi benefiting dinmu duka"
Hajiya Naja'atu tace "toshikenan"
****
Muzammil tunda yafita wurin aiki yaketa tsumayin kiran Chief of Army dayake yau za'ayi meeting da high ranking officers kamar yanda suka tsara anma sede dayake ranar bashida wasu ayyuka sosai harya tashi agun aikin chief of Armyn be kirashiba. Shikuma seyake gani kamar bedace shi yakirashi yahau yimashi tambayoyiba donhaka ya hakura yacigabada anticipating sanda chief of Armyn zekirashi.
Mota yasa driver yakawo mishi daga gida ayayinda yaceda escorts dinsa suyi wucewarsu gida kawai shizai zaga gidan Kakanninsa da Yan uwa yayimusu gaisuwar azumi seda yanma zaikoma gida.
Acan Abuja kuwa tun karfe goman safe Chief of Army yashiga meeting da high ranking officers hakanan cikin su babu wanda bai halarci taron ba se Muzammil. Koda akayi acknowledging absence dinsa chief of Armyn dakansa yace yana sane shine yaturashi yimasa wani aiki mai mahimmanci shiyasa baisamu daman zuwa ba. Awanni uku cur sukayi suna tattaunawa kafin aka rufe taron da addua aka tashi. Haka suka fito wasu na murnar sabon canji da Chief of Armyn yace zaikawo sabida asamu cigaba a fannin tsaro na kasar ayayinda dayawansu kuma tsarin sam baiyimusuba sabida selfish reasons dinsu nayau da kullum. Tun ana cikin meeting dinma dayawansu sukaita kawo korafi anma Chief of Armyn ya katse su tahanyar cewa command ne yabayar ba tarasu yayi yaji ra'ayinsuba. Wannan dalilin yasa suna fitowa suka cigaba da korafin,wasu na jajen rage musu jin dadi daza'ayi sabida irin garabasar dasuke kwasa adadin tahanyar haram,wasu na kumfar baki ayayinda wasu kuma abu bewani daga musu hankali ba. Ganin abun suke kamar wasa,gani kawai suke kamar chief of Armyn yafada a fatar bakine kawai bawai zai iya aiwatarda abunda yacedinba barinma da sukasan shi mutum ne mesanyi darashin son hayaniya and moreover bafa tunyau ake abunnan ba? Renowned Soldiers da suka fishi suka kuma kafa tarihi tunma alokacin military regime basu kawo wadannan changes dinba seshi yau rana daya yazo da kabli da ba'adi? Aishimadai yasan wasa yake.
Cikin wanda hankalinsu yatashi kuwa harda Alhaji Yusuf abokin RTP party chairman. Tun sanda Chief of Army yafara jero sabbin rules dinda suka fitar shida Muzammil yaji hankalinshi yatashi kuma shine mutum na farko da yafara kawo korafi agurin dukwai dan yasamu masu mara mai baya ayi againsing maganar amma chief of Armyn yaturje sam. Bakin ciki kamar yayi yaya,yaji kamar yatashi yafice daga gun taron midway. dakyar dai danne zuciyarsa yazauna har aka kai karshe.
Yanzu dama abunda Muzammil da Chief of Armyn suka shirya musu kenan da Oliver yace Alh. Auwal party chairman spy dinsu na gidan Chief of Armyn tace taji suna zancen meeting da za'ayi cikin sati? Miyasa basuyi tunanin wata makarkashiya suke shirya musu ba bare suyi bincike? dayanzu duk haka bata faruba because atleast they would've done something before hand. Yana fitowa a conference room din Alhaji Auwal Party chairmam yafara kira yasanarda shi halin da akeciki inda daga karshe yakarada
"Ninasan wannan idean duk na algungumin can ne dan Chief bazai taba zama yayi wannan tunanin shikadai ba. Gabadaya Yaro yazo cikin shekaru kankani yasa anata juyamu kamar wasu waina bamu da say akan aikinmu. Toh wallahi mukayi wasa gaba gaba basawa zaiyi adinga juyamuba shida kanshi zai dinga juyamu koma yarabamu da gurin aikin munaji muna gani bayanda muka iya" Alhaji Auwal from the other side cikeda takaici yace "Gaskiya he's becoming an obstacle. Toh yanzu kai miye plan dinka?"
