Page Forty Eight

437 61 13
                                    

👨‍✈️ *CAPTAIN MUZAMMIL* 👨‍✈️

Written by *Zeeneert*💕

Zeeneert@wattpad

*Page Forty Eight*

Darana Khadija tayi wanka tahau cancanda kwalliya zata tafi wurin Muzammil a office. Tun jiya taso takai mai ziyara dadare a sashin shi unfortunately for her Al'amin da Fa'iz nanan as Fa'iz was still in town shiyasa Al'amin din bekoma sashinsu ba seyau. dazu kafin sutafi Maiduguri taga yana shigowa da yan komatsensa da alamadai yadawo nan din kenan.

Itakuma she's too excited tajira harsai Muzammil din yadawo daga office kafin taganshi,Allah kadai yasan daya takawo har iwarhakama. Burinta taganta agabanshi taga how far the laya has worked on him. Har imagining reaction dinsa and how he would be carried away by her looks once he sets his eyes on her takeyi danko tantama batayi tasan ya tsallake layarnan by now as she makes sure tasaka agurinda takeda tabbacin koda ace daga tashinshi a bacci beyi setting foots dinsa agurin ba toh babu yanda za'ayi yayi roaming about adakin batareda yabi takaiba. Haka tacigaba da cancada kwalliyarta kamar me zuwa gidan biki harta gama taciro kayan da zata saka. wani matsatsen riga da skirt na atamfa ne da gabadaya yay revealing surar jikinta tasaka.

Ammi dake kwance kan gado tana kallon episode din yau from Ramadan Series din Dr. Imam Omarsulaiman titled "JANNAH HOME AT LAST" ganin yanda Khadijar keta faman nishi tsabar yanda kayan ya matseta batasan sanda ta tabe baki ba. Sekace dole? da lafiyarka da hankalinka da komai amma kabi ka takura kanka duk asunan gayu?itadai Allah yagani bazata iya wannan wahalar da kanba. Sam bata kawowa ranta cewa Khadijar gurin Muzammil zataba bare tayi yunkurin sanin yanda zatayi tahanata. tasandai wannan shigar tabbas has to do with harka da samarinta.

Khadija nagama shiri dakin Mummy tawuce. zaune tasame ta kan gado tana kallon Sunnah TV,dayake sunriga sun gaisa tun safe seta tsuguna kamar mutumiyar kirki tace "Sannu da rana Mummy" Mummy fuska daukeda murmushi tace "Yauwa sannu Khadija" Khadija tace "Daman inadan so inje kasuwa ne Mummy" Mummy tace "toh anma zaki gane gurin ne?gashi daga Mallam Shu'aibu har Al'amin bawanda yakenan bare akaiki" Khadija tace "Badamuwa Mummy. Ai kasuwane bazan bataba" Mummy tace "Toh ko zakice Ammi da Naanaa sushirya sekuje tare?" Khadija seda zuciyarta tayi raaasss jin abunda Mummyn tace,dakyar tasaki murmushin yake aranta tana addu'ar Allah yasa kar Mummyn tayi insisting tace "Insha Allah bazan bata badai Mummy" Mummy tayi murmushi tace "Toshikenan tunda kindage anmadai kicewa Ammi nace tabaki key din motar Abbanku da Mami keja sekije dashi. Aikin iya driving koh?" gyadakai Khadija tayi aranta tanaji kamar tatashi tayi tsalle dan murna. Dama se tunanin yanda zatayi tahau napep dawannan uwar gayun dataci takeyi. gashi batada wani saurayi agarinnan bare takira yazo yakaita

Tace "Toh Mummy. Nagode" Mummy tace "Bakomai. Adawo lafiya koh?"

Koda tatashi zata fita kurawa yanayin shigarta idanu Mummy tayi,dafari kamar tayi mata magana kan kayan beyiba sekuma tayi la akari da aizata je daki tadau gyale tayafa may be shiyasa batadamu da matseta da kayan yayi sosai ba.

Khadija nakomawa dakin kan Ammi taje tatsaya,adakile tace "ina key din motar bakar Yayarkincan?" Wani kallo Ammi tawatsa ma Khadijar in disbelief tace "Bansani ba! Kije kinemi farar Yayata irinki tabaki" Khadija tace "Unfortunately you don't have one" Khadija tace "Ahaka kuma ita bakar Yayartawa da kika raina tahana ki rawar gaban hantsi ba!dakuma bakin nata da komai shi wanda kike mutuwar so din yadage se ita" Ammi tashiga yiwa Khadijar kallon kare dangi from head to toe tana nunata da hannu tace "kodayake miyema marabar kwado da gaya? Dabadan Allah ya taimakeki kinsamu kinshiga kantiba kedinma harwani ganuwa zakiyine? Ko ayanzu dakike artificial baki isa ki goga kafada da Bakar Yayartawa bare da dakike duna baleru.....!"

Sosai maganar Ammi tadaki Khadija anma data tuna anytime from now Muzammil zaidawo tafin hannunta seta saki murmushin mugunta tace

"Daina cika baki dan nan bada jimawaba zannuna miki karantar matsayin Yayar taki agunshi"

CAPTAIN MUZAMMILWhere stories live. Discover now