Page Forty Five

393 53 11
                                    

👨‍✈️ *CAPTAIN MUZAMMIL* 👨‍✈️

Written by *Zeeneert*💕

Zeeneert@wattpad

*Page Forty Five*

Duk wannan bidirin Khadija batanan akayi su,tanacan gida haryanzu ba agama watsewa ba as people are still preparing for the event. bakin ciki kamar tayi yawa danta so ta cusa kanta ga Muzammil din yau suyi dan having moment. Se around 6pm tasamu kowa ya watse takirasu tasanar dasu suka fara preparing yanda zasuyi sushigo gidan inda ita kuma tatafi wurin event dinda tun hudu da rabi akafara gudanar dashi.

Da addu'a aka fara gudanar da taron sannan MC yayi honouring zuwan manya manyan yan kasuwa(bussiness tycoons) irinsu Aliko Dangote,Isyaka rabiu,the Dantatas dadai sauransu. Abangaren Mami kuma chefs and food book authors dasukayi suna sukayi fice anan kasarmu Nigeria dama wasu kasashe daban daban irin su Hilda Baci,Chefhalimaz and Maaryamaa da has always been Mamis role model and source of inspiration tun tana yarinya sekuma manya manyan Malaman mu na addini kama daga kan nanan kasarmu Nigeria da na waje irinsu Sheikh Aminu Daurawa,Guruntum,Imam Omarsulaiman da Mufti menk da Abban ya gayyato dansuyi tafsiri akan kasuwanci a musulunci (bussiness in Islam) dakuma irin abincin da musulunci ya halalta aci as Mami is working on different dishes from different countries,culture and traditions,akuma irin hakane in bakada masaniya akan abun sekaje kana ciyar da wasu haram kaima kana karban haram and when they did mutane dadama sunkaru sosai.

Karfe shida da yan mintuna waiters suka fara shigowa da variety of fruits da aka gyara aka sassaka a bowl akayi sealing bakin bowl din da clim film gwanin ban sha'awa suna ajiyewa akowani table. Dashi aka bude baki da lokacin shan ruwa yayi sannan aka dunguma babban masallacin dake cikin M.M TUMBIDO akayi sallar maghrib. Ana tasowa daga masallacin kuma restaurant din Mami aka wuce yin iftaar. Gurin atsare gwanin ban sha'awa waiters da caterers nata kai kawo cikin uniform dinsu kamar dama anfara aiki a restaurant dinne.

Kowani table da takardar menu a ajiye gakuma waiters uku uku akowani table dake tsaye already suna jira kufadi me kukeso akawo muku cikin lokaci kankani. Inkuma kanaso ma zaka iya zuwa inda abincin yake kayi serving kanka dakanka dankuwa abinci ne kala kala agurin sewanda kazaba dankuwa babu ne kawai babu agurin dukdama some of the dignitaries dasuka halarci taron anyi musu tanadi na musamman awani daki inda suka shiga sukayi nasu iftar din aciki.

Asibitocin garin,gidan marayu da tsangayoyin almajirai suma ba abarsu abayaba dan musamman Abba yasa akaje akakaimusu sadakan lafiyayyyun abinci masu rai da motsi sukayi bude baki dashi.

Mami dai tunda aka fara program din takesaka ran ganin Sadiq yashigo anma babu shi babu labarin shi har akaje akayi sallah akazo nan restaurant dinta ba taga koda glimpse of him baneba. Hankalinta sosai yatashi,ina yashiga haka? Inma bazaizo yaga programme dinba da lokacin shan ruwa yayi aise yashigo yasha. tasandai zaiyi wuya ace yakoma gida tunda bashi yayi driving kanshi yazo nan dinba moreover she don't even think yasan sunan unguwarsu bare har ya iya kwatantawa amaida shi.

Dukda how extremely busy she's with the guests haka tasamu ta sulale taje tadauki tray tadauko bowl tamai mixing fruits dinda tasan yanaso sannan tahada mai favourite abincin shi. Fita tayi a hall din tanufi hanyar da taga yabi dazu da yanma tana dube dube kozata hangoshi tawani barin. Acan bayan fire service na companyn tasamoshi zaune ya kurawa sararin samaniya idanu. ba tasan sanda tasaki wani nannauyar ajiyar zuciya ba ayayinda takarasa inda yake ta ajiye tray din kafin tasamu guri tazauna gefenshi.

He was deep in thought dabaimasan tazo gurinba seda yaji karar ajiye tray dinda tayi,dagowa yayi yakalle ta suka hada idanu na sakanni kafin yashiga kokarin tashi agurin batareda yace da ita komaiba. Mami saurin riko hannun riganshi tayi kanta na kasa cikin sigar roko tace

CAPTAIN MUZAMMILWhere stories live. Discover now