Page Thirty Seven

359 39 5
                                    

👨‍✈️ *CAPTAIN MUZAMMIL* 👨‍✈️

Written by *Zeeneert*💕

Zeeneert@wattpad

*JUMA'ATU MUBARAQ CM FAMILY* ❤

*Page Thirty Seven*

Sallama yayi suka amsa duka ayayinda Mummy dake ta kokarin making call awayarta tadago tana kallonsa fuska daukeda murmushi  ayayinda tashiga fadin "Kaji dan halak. Yanzu naketa kokarin kirarka awayafa" murmushi Muzammil yasaki ayayinda yakaraso cikin parlourn yasamu guri kasan carpet din yazauna yashiga gaisheda Mummyn ta amsa sannan yagyaida Mata biyun dayasamu tareda Mummyn suma,sukayi ma juna farin ciki tareda fatan alheri kan sabuwar wata mai alfarma da aka shiga sannan Mummy tace "Har anyi shirin fita kenan?" Muzammil yayi murmushi yace "Insha Allah Mummy" Mummy tace "gashi nikuma akwai wata magana danakeson muyi sede bansani ba ko sauri kakeyi?" Muzammil yace "Just go ahead Mummy. Aikin can wait ai" Mummy tagyara zamn ta tace "Dama akan sadakar abincin bude baki damuke bayarwa kowani shekara kafin mukoma Sweden ne mukeso mucigaba tunda Allah yasa mundawo" tadaga jotter dinda ke hannunta tana nunawa Muzammil tace "I'm making a list of adadin abincin daza'a dinga fitarwa kowani rana shine nakeson inji yakukeyi da mutanenka? should we include them on the list koyaya?" Muzammil curiously yace "You mean my Soldiers Mummy?" Mummy tace "Eh" Muzammil yace "Daman yanda mukeyi every year akwai specific Restaurant danakesawa aje abiya na bude bakin for the whole Month sesuna zuwa kowa yakarbi abunda yakeso" Mummy tace "Toh yanzu kabiyana wannan watanne?" Muzammil yace "A'a yanzune innafita nakeso inbayar aje abiya" Mummy tace "Toh aishikenan. You don't need to do that kabari se anacire musu anan duk sanda kuke gari harma dana sahoor inyaso kai sekayi fama danacan Maidugurin" Muzammil yace "Toshikenan Mummy. Thank you,Allah yasaka a mizani" Mummy tace "Amin ya rabbi" Muzammil yashiga looking around crevices na parlourn wai ko Allah zaisa yaga koda wulgawan tane dukdama yana jin kunyar next haduwarsu,besan dawani idanu zaikalleta ba bayan abunda yafaru jiya amma shiru,ko wulgawan su Ammi beganiba barena gimbiyar tasa.

Yadawo da dubansa ga Mummy cikin wayancewar kar Mummy taganosa yace "Mummy Abba fah?"  Mummy tace "Abban ku da Yaran duk  basu tashi ba tukunnan" Muzammil yace "Okay toshikenan nizan fita Mummy. In Abban yatashi kwa gaisheshi" Mummy tace "To adawo lafiya Son" har Muzammil yatashi zefita zancen  Uche yafado mata arai,tayi sauri tace "Auuu kaga namanta koh? Nikam kunyi magana da Uche awayane tunbayan tafiyarsa?" Aida sauri Muzammil yadawo yazauna jin  Mummy tayi maganar Uche yace "Bamuyi magana ba Mummy and tafiya kuma? Ina yatafi?" Mummy tace "Besameka awayanba kenan harya isa garinsu" ta numfasa tace "Nine na sallame shi nace yatafi gida ganin balallai kabukace shiba tunda Allah yadawo damu. He called to inform you ranardazai wucen wayarka bata tafiya shine yace don Allah insanardakai incase besamu kunyi communicating ba dan garin su ba network once ya isa can he can't get access to you"

In Muzammil yace decision din Mummy yamai dadi yayi karya . Ta sallami Uche? The one and only Uche that was always beside him through all his difficult times?The one and only Uche that knows every single thing about him kama daga kan likes dinshi,dislikes dinshi,kinds of meals he wants,the clothes he wears dadai Sauran su. Yaukadai dayaci meal daya not table settled by Uche yaga jafa'i bare ace yarasashi har abada. Ama ajiye wannan agefe aiko Uche baya mishi aikin komai zamanshi agidan alone means alot to him,koba komai there's someone breathing beside him acikin gidan which helps in reducing his loneliness. Toh anma yazaiyi? Mummy ce fa tayanke wannan hukunci?Mummyn da bayida kamarta yakekuma ganinta amatsayin uwa bayan Ummi? Mummyn data haifa masa abunda yafi komai so aduniya,Mummyn Maminsa,Mamin dayafi komai so aduniyarnan bayan iyayensa da yan Kanninsa.

Moreover he's sure Mummyn tayi hakanne amatsayin gwaninta bawai don ta kuntata mai ba and so he'll only pray Allah yasa hakan shine mafi alheri.

Mummy kamar tasan tunanin da Muzammil yakeyi seta karada "dukdama nacemai yadawo after sallah incase you still want him around for wasu ayyunkam inkuma baka bukatanshima Mami can hire him yamata aiki a restaurant dinta tunda naga Yaron yanada kwazo sosai wurin harkar girke girke" Muzammil  besan sanda yasauke wani nannauyar ajiyar zuciya ba jin abunda Mummyn tace dukda kuwa bayajin bayan Ramadan din zai bukaci Uchen

CAPTAIN MUZAMMILWhere stories live. Discover now