👨✈️ *CAPTAIN MUZAMMIL* 👨✈️
Written by *Zeeneert*
*Zeeneert*@wattpad
*You might not be able to understand somethings indai baki/baka karanta Rayuwar bintu ba. This's the continuation of that book though a different story line somehow. Abunda kadai zan iya fada muku shine this book is connected to Rayuwar bintu. To get a better glimpse of what I'm writing currently I advise you read Rayuwar Bintu first. Thannk you and happy reading*. 😍
*Page Twenty Four*
Itanma yanda Abban yamasa haka tayi kuma baiyi mamaki ba because he expect as much. Bebar gurin ba kamar yanda Mummy tace seda yaji jirginsu yadaga sannan yabar airport din yakoma gida.
***
Abba tunda suka isa DTR yayi wanka yayi sallar la'asar ko Lunch dinda Nany Ngozi ta jere musu kan dinning tun kafin su iso gari bebi takaiba yawuce study room dinsa yafara bincike kan social media accounts na Mami and he was able to restore all the chats a computersa,around 9pm na dare yagama recording komai cikin wayarsa yama Daddy forwarding on WhatsApp yakuma kirashi yasanar dashi yatura masa sannan yabar study room din yakoma can dakinsa. Samun Mummy yayi sanye cikin one of nighties dinta tana lailaye musu gado dawani hadadden bedsheetJin shigowar mutum ne yasata dagowa,suna hada idanu suka sakar ma juna murmushi, Mummy tace "Kasamu kagama aikin kenan?" gyada matakai yayi ahankali yace "Uhmmm and I'm able to restore all the chats" barin shimfida bedsheet dinda Mummy keyi tayi tatashi tsaye zatayi magana Abba yakatseta tahanyar tambayarta ina Mami.
Mummy tace "A parlour nabar ta tareda Sagiru suna hira bayan mungama cin dinner,baka gansu bane sanda kawuto?" Abba yace "Bakowa a Parlour,inaga yagaji da surutun yatafi yakwanta" Mummy tayi dariya tace "Sagirun ne zaigaji da magana? Aisede in Mamin ne bata bashi hadin kai ba" Abba na murmurshi yace "Abunda nake nufi din kenan,awannan yanayin da Daughter take ciki bana tunanin yasamu hadin kan shiyasa yahakura yatafi" jinjinakai Mummy tayi ahankali.
Abba yace "Kikarasa gyaran gadon kikiramin Mami kusameni a parlour akwai maganar danakeson muyi"
Mummy cewa tayi toh ayayinda tacigaba da shimfidar bedsheet din shikuma Abba yafice a dakin.
***
Acan Bangaren Daddy kuwa zaune suke a parlour shida Ummi sanda Abba yakirashi yasanar dashi taturamai evidences din,ba karamin sanyi yaji jikinsa yayi ba lokaci guda, ya kunna datarsa yashiga downloading video records uku da Abban ya turo masa.Shortest one dinne yafara gama downloading don haka Daddy yabude,chats ne tsakanin Mami dawani dayake claiming to be Muzammil dan kallo daya Daddy yama username din yasan bana Muzammil dayake using currently baneba. The chats are not much kuma on and off ne daya lura da date na distance din conversation dinnasu,yana gamawa next video din yashiga which is their conversation on IG and date dinda suka fara magana was exactly 8days bayan tafiyar Muzammil.
Bin chats din yayi yana gani haryakai karshe and conversation dinsu anan yanada yawa fiyeda na Facebook din,last one din yafi kowanne yawa and it's their WhatsApp conversation. Sanda Daddy yabude video din idanunsa kan contact din yasauka and he's shocked to see the digits,yayi sauri yamikama Ummi wayar yana fadin "Wannan ba tsohon layin Muzammil bane Yusra?" Karbar wayar Ummi tayi tana kare ma layin kallo in shock tace "wallahi shine Daddynsu Ameera but he's not using it anymore ai,betafi dashi ba katuna?" Daddy yace "Natuna mana,ba mantashi yayi anan gida ba seda mukaje Abuja yatuna shine muka saya masa sabon layi" Ummi ta jinjinakai tace "Sure but if that's the case waye yadinga using layin yana blackmailing Mami haka?" Daddy yace "Someone close to us or Someone that knows Muzammil yabar layinnan agida betafi dashi South Africa ba" Ummi tace "But bakowa yasani ba Daddynsu Ameera,koranar aimukadai yafada ma" Daddy yace "Alokacin da yabar layin ba. But the moment he started using his new line dole along the way yabama wani labarin dalilin canza layin nasa" jinjinakai Ummi tayi tace "Dawannan ma kuma" daganan tamaida dubanta kan wayar tashiga duba sauran videos din tana ganin abun al'ajabi tace "Ikon Allah sauran kuma duk different user names ne banasa dayake using ba" Daddy yace "Eh. Phone numbersa akayi using sekuma aka bude other social media accounts da sunansa"
![](https://img.wattpad.com/cover/302177252-288-k647401.jpg)