👨✈️ *CAPTAIN MUZAMMIL* 👨✈️
Written by *Zeeneert*
*Zeeneert*@wattpad
*You might not be able to understand somethings indai baki/baka karanta Rayuwar bintu ba. This's the continuation of that book though a different story line somehow. Abunda kadai zan iya fada muku shine this book is connected to Rayuwar bintu. To get a better glimpse of what I'm writing currently I advise you read Rayuwar Bintu first. Thannk you and happy reading*. 😍
*Page Twenty Nine*
Hadadden katoton office ne dake dauke da furnitures na zamani hakanan jikin bangon office din kusan tako Ina kajuya zakaga frame na award or certificate din mamallakiyar office din. Wani irin kamshin turare mai shegen dadi da kwantar da hankali ne gauraye da sanyin AC daketa aiki office din yake fitarwa. Maryam Aliyu Tumbido da akafi sani da Mami na zaune kan kujerarta looking so regal,kamar gurin dominta akayi daman.
Gabadaya hankalinta nakan wani katoton hardcover book dake ajiye gabanta kan table din. Karanta littafin takeyi carefully hannunta rike da pen inda akai akai kuma zakaga tana saka pen din tana underlining wasu gurare. Da alamadai editing content din dake cikin littafin takeyi.
Sanye take da wata Sandy brown abaya da akayi masa kwalliya da ratsin ratsin kalar blue and Ash,karkuso kuga yanda abayar ta makukar ansar jikinta takuma sake fidda asalin kyaunta. Fuskarnan babu kwalliya,just her natural face sekuma wet lips data shafa kan lallausar lips dinta daya taimaka wurin sake kayata fuskar tata. Acikin shekaru shidan dasuka wuce bata wani kara tsayi ko jikiba se wasu halittu najikin mutum dasuke nuna ya balaga dasuka sake girma da bayyana.
Knocking kofar office din akayi tana cikin karance karance da editing,batareda tabar abunda takeyiba tace "Yes come in" tanaji aka bude kofar akashigo anma sedai ba ayi magana ba instead seji tayi anja daya daga cikin chairs dinda suke opposite to her chair,akakuma ajiye Mata bouquet of yellow flowers dake daukeda card jikinsa gabanta.
dagowa tayi da mamaki sanin cewa mekawo Mata irin wannan flowers din baya kasar gabadaya takuma tabbata da turowa yayi akawo mata baza azo azauna without saying a word hakaba. Idanunta dasuka fada cikin nashine ya sake tabbatar Mata dacewa tabbas shidinne,wara idanu tayi batareda ta shiryaba tace "You!" Fuskarta cikeda tsantsar mamaki. Hadadden saurayin da kallo daya nayi masa na alakanta shi da jinsin larabawa sabida tsananin kama dayakeyi dasu yana kallonta,with a smile on his face yace "Yes me!" Mami removing herself from the shock of seeing him ta ajiye pen din hannunta kan opened hardcover book dinda ke ajiye gabanta takoma tajingina da kujerar datake zaune kai tareda fadin "Yaushe kadawo?" Saurayin yace "This morning" Mami in disbelief tace "But you said you'll be spending two weeks there Sadiq" Sadiq dahar lokacin murmurshi yakeyi yace "Gimbiya tana fushi dani ta Ina zan iya cika two weeks din?" Mami curiously tace "Baro Ummin kayi acan kenan?" girgizakai yayi yace "Nop,we came back together" wani kallo Mami tama Sadiq cikeda tuhuma tace "Takuramata kayi baku gama hutunku ba kace kudawo koh?" cikin sauri Sadiq yace "Aa wallahi! Niban takura mata ba. She was the one that saw me acting weirdly for the past few days shine tatambayeni meyake faruwa nikuna na fada Mata,kinsan dai I can't lie to her and then she suggested mudawo muyi rarrashi" Mami dake hararanshi tun sanda yake magana tace "what's the difference between abunda kayi da takura Mata danace kayi din?" Sadiq trying to defend himself yace "Ita tatambayeni bani nasameta directly nafada mataba faah....secondly I was not the one that suggested we should come back kafin hutun mu yakare ita dakanta tace mudawo" Sadiq yayi maganar cikin son defending kanshi koma yayane.
Mami tace "Bawani nan,aiko bata tambayeka ba ninasan daman kanada niyar fada Mata. Nafasan halinka Sadiq" Sadiq in surrender yace "Shikenan naji nakuma amshi laifina but inban fada Mata damuwata ba wazan fadama Maryam? she's my Mother and the only thing I've in this world sabida haka karkiga laifina and let's talk about main issue dinmu. This's not really important seriously...."
