Chapter Two

1K 56 4
                                    

✨ *MATANA*✨
 

*Mallakar*
       AUTAR MAMA

*FREE BOOK*

*EXQUISITE WRITERS FORUM*

*Wannan labarin ƙirƙirarre ne, banyi shi ɗan cin zarafin wani ko wata ba! Sannan idan yayi shige da labarinka/labarinki coincidence ne Yawwa*

*Comments share and vote dinku yana da matukar mahimmanci idan yayi karanci zan maida abuna ba kudi💃*

*Whatsapp group females only please*

https://chat.whatsapp.com/Ib3gwXORbTB1GxcVr0FdAw

*002*

        Kamar mai bacci amma a zahirin gaskiya ba baccin ya ke ba, tunanin Zara'u kawai yake yi, baisan yadda take ji a zuciyarta ba, duk da cewa shi din bawai yana cikin jin daɗi bane amma zuciyarsa da ta Zara'u ba ɗaya ba, a zaman da sukayi ya gane ita ɗin macece mai rauni abu kaɗan yana jefa cikin damuwa da ƙunci. Buɗe idanunsa yayi a hankali yana cire duvet din dake jikinsa, Wayarsa dake jone a charji ya ciro yana shiga call logs.. *Zahmar❤️* shine sunan daya nemo tare da yin dialing. " _The MTN number u'r trying to call is switch off_"  shine abinda aka faɗa masa, ajiyar zuciya yayi yana sake trying amma still abinda aka sanar masa kenan. Ajiye wayar yayi yana sakkowa daga kan gadonsa ya saka room slippers zuwa kofar bathroom sannan ya cire ya shiga toilet. Be dade ba ya fito ya shirya cikin jallabiya ya dauko makullin motarsa, iyayensa mata ne zaune a falon Maminsa, kansa a ƙasa ya karasa yana tsugunnawa chan ciki ya ce " Ina kwanan ku" "Lafiya ango kasha khamshi" Cewar wata mace dake zaune a ƙasan carpet tana raba IVs din dake hannunta.. bai ce komai ba ya miƙe tsaye ya wuce bedroom dan yasan Maminsa na ciki. A zaune ya ganta a bakin gado ita da Maryam su na lissafin kuɗi.. daga bakin ƙofa ya tsugunna yana fadin " Ina kwana Mami" bata amsa masa ba ta cigaba da lissafinta.. ɗagowa yayi ya kalleta sannan ya kara maimaita abinda ya faɗa, sai a lokacin ta kalleshi ta ce " Isasshe! Jiya a ina ka kwana? Har 1am baka gidan nan? "A gida na kwana Mami! Kwafa tayi tana wurga masa wani kallo ta ce " Ita amaryar haka za'a kawota ba gyaran jiki? Ba kunshi ba gyaran gashi? Sannan Umar be faɗa maka kudin Event ba? Shafa kansa yayi kaɗan yana kallonta ya ce " Ya faɗa min amma bani da 1.2m na Event gaskiya, infact ma ni banda wannan ra'ayin just wedding fatiha is enough! "Tabdijan aikuwa wallahi baka isa ba! Ita Sadiyan zaka bawa kunya? Ƙanwar tawa? Toh wallahi karya kake Allah kaji na rantse, kafin na saba maka kayi min transfer din kudin event din sannan anjima ka shirya kaje wajen Bilki ka bata kudin gyaran jikin idan kuma naji akasin abinda na faɗa sai na saɓa maka wallahi, kuma ka hanzarta a gama gyaran gidan naka ɗan zasu fara jere jibi! "Toh" Ya fada yana fita daga ɗakin.. "Bazai iya fitar da 1.2m akan Event ba kamar wani bikin yar gata, ko bikin soyayya, da ace Zarah ce he can do more than that ma but not Bilkisu itama yarinyar kamar mayya! Tsaki yayi yana ficewa daga falon ko sake kallon kannen Maminsa beyi ba.

       Ya daɗe a kofar gidansu yana neman yaron da zai aika amma kamar anyi yasar yara a unguwar tun zuwansa bega ko ɗaya ba, fitowa yayi daga motarsa ya jingina tare da crossing legs.. Saude ce ta fito daga cikin gida tana sanye da uniform na boko sai sauri take Cox ta makara sosai dan 10 har ta kusa kuma 10 din suke da exams. Ko lura dashi batayi ba, ganin zata wuce yayi saurin kiran sunanta.. Juyowa tayi tana ƙare masa kallo daga sama har ƙasa sai kuma ta tsuke fuska tana karasowa inda ya ke ta ce " Wai me kazo yi? Murmushi yayi kadan yana tunawa da lokacin da yake biyosu gida idan sun dawo daga school, ita take tilastawa Zara'u ta saurareshi. "Wallahi idan na kara ganinka a kofar gidanmu sai na saka yara sun bika suna watsa maka ruwan kwata! Dama chan karya kake yi ba son Aunty Zara'u kake ba! Idan ita bata ganin laifinka saboda soyayya, toh ni tas nake ganinka wallahi! Wai wallahi aure zasu min! Ta karashe maganar tana kwaikwayon yadda ya fada lokacin daya zowa Zara'u da zancen. "Gansameme da kai! Balagaggen namiji irinka za'a yi wa auren dole saboda ka maida mu illiterate? Shi dai kallonta kawai yake yi dan masifa take sosai.. gyara hijabinta tayi tana fad'in " Kuma Allah ya isan Aunty wallahi duk hawayen da take zubarwa a kanka! Daga haka ta tafi ta barshi. Numfashi yaja da karfi yana saukewa a hankali. Ya kai kusan 10mins a tsaye har yayi deciding ya tafi sai yaji motsi a soran gidansu, karasowa yayi wajen kofar gidan, Zara'u ce ta zubar da sharar data kwaso har ta juya baya zata koma ciki ya ce " Zarah! Turus tayi jin muryarsa, toh kodai gizo muryar tashi take ma ta? Me zaizo ya ma ta da sassafe haka? "Zarah! Ya kara kiranta.. kin juyowa tayi dan yanzu kam ta tabbatar shi dinne dagaske, ko second bata kara ba ta shige cikin gida tana jin zuciyarta na wani irin suya. Shafa kansa yayi yana ji kamar ya kurma ihu, tako ina baya samun wani sassauci. Cikin mota ya koma. Gidansu Umar ya wuce dan sam yanzu baya son zuwa gida tunda aka fara zancen auren nan. A wajen gidan yayi parking, karamar kofar jikin gate ya tura, bakinsa dauke da sallama ya shiga falon gidan, babu kowa sai khamshin turaren wuta kawai da falon yake yi.. kwanciya yayi a kujera yana relaxing.. har ya lumshe idanunsa yaji Hajiya Babba ta ce " Ammaru! A kasalance ya buɗe idanunsa yana tashi zaune ya ce " Hajiya Babba ina kwana" cup din hannunta ta ajiye a Centre table tana fad'in " Lafiya lau! Da sassafe haka ince dai lafiya ko? "Alhamdulillah Hajiya babba, ina Fa'iza? "Ta wuce makaranta wai Test ne da ita tun 8 amma ko 30 mins batayi da fita ba. Murmushi yayi kadan ya ce " Sarkin bacci ce ai" Hajiya babba bata dora da zancen ba ta ce " Kaƙi kwantar da hankalinka ko? Shafa kansa yayi kadan ba tare da yace komai ba. " Kayi haƙuri su iyaye hakuri ake yi dasu, kuma zaka sota insha Allah, itama da uwarka ai ba son ƙanina take ba, sai daga baya gashi har an haifeka, an haifi Fatima da Maryam! "Hajiya! Era dinku da namu ba daya bane, wallahi ni nafi tausayin yarinyar, banyi ma ta adalci ba, ba kowane zai yarda da cewa ba yaudararta nayi ba, bansan adadin mutanen da zasuke zugata ba, ko wajenta naje bata sonyi min mgana, kuma nasan tana sona, Hajiya Dan Allah kiyii wani abu akan lamarin nan" shafa kansa tayi tana murmushi ta ce " Kayi biyayya Ammar! Mahaifiyarka ta fini iko da kai, kuma waliyanka ma suna son abun nan kayi hakuri kawai ayi kaji ko? "Amma Hajiya ai kamar uwa kike a wajensu Baffa, zasuji abinda kika ce, Dan Allah Hajiya" Ajiyar zuciya Hajiya tayi tana kallon sa ta ce " Shikenan zansan yadda zanyi, ka tashi kaje wajen Umar din yana daki zan aiko maka da breakfast dan nasan ko karyawa bakayi ba" Gyaɗa kai yayi yana wucewa upstairs.. a kwance ya tarar da dan uwansa kuma abokinsa sannan Yayansa yana danna waya, a kan bedside drawer ya zauna yana fad'in " Hi! "Yanzu Mami ta kirani akan kudin event dinann! Tace ta kira wayarka a kashe! "Na bar wayar a gida ne banyi ma ta transfer din ba, Please taimaka kamin idan na koma gidan zan maka! Wani kallo Umar yayi masa kafin ya fashe da wani dariya ya ce " U'r not serious! Nidin zan biya maka kudin Event? Ai ba yau aka haifeni ba, nasan Tabbas idan na tura kudin nan toh tasha ruwa ba bani zakayi ba" Ammar bai ce komai ba ya dawo gefansa ya zauna. Hajiya Babba ce ta shigo da tray wanda ta jero abinci a kai, godiya yayi ma ta tana masa murmushi ta fita.  Tea kawai ya haɗa dan bashi da wani appetite da zai iya cin abinci. "I'm advising you ka cire komai ka rungumi auren nan, Allah yayi dama itace matarka, wannan ramar da kakeyi banga amfaninta ba" Kallon Umar yayi yana dan sipping tea yace " Da zakaga Zarah kai kanka sai ka tausaya ma ta, at her early 20 ta hadu da heartbroken, kuma kasan yadda take so silent kuma damuwa tafiyiwa irinsu illa they can't outer their pains" "Ai kaidin mijin mace hudu ne, Ni Banga abinda tada hankali ba! Bayan ka auri Bilki sai ka aureta! Girgiza kai Ammar yayi kafin ya ce " Bazaka gane zafi ko ciwan abun ba, saboda wadda kake so take sonka ita zaka aura, let's end the conversation here! Umar be kara cewa komai ba ya cigaba da latsa wayarsa. Har bayan la'asar Ammar yana gidan elder sister din babansa. Wayar Umar ya karba yana saka number Zarah a ciki, badly yake sonyi magana da ita. Luckily ta fara ringing, yana kwance amma ya tashi zaune da sauri.. shi dai Umar kallonsa kawai yake yi.. harta tsinke bata dauka ba. Sake kira yayi shima no answer.. zai sake dialing Umar ya kwace Wayarsa yana fad'in " Toh natau! Karamin tsaki Ammar yayi yana tashi ya fita daga dakin, bai daɗe ba ya dawo rike da wayar Fa'iza.. Zama yayi a kan sofa ya shiga kiran layin Zarah kamar wanda aka turo.. karo na biyar kenan yana kira har ta kusa tsinkewa yaji an dauka tare da yin shuri.. "Hello Zarah! "Ba ita bace, Saude ce" Runtsa ido yayi kadan dan yasan ya shiga uku da bala'in yarinyar. "Waye? Yaji ta faɗa. "Ammar ne! Ya bata amsa. Yana ji ta danyi tsaki kafin ta ce "Toh dan anaci, Inna ta kwace wayar kuma yanzu ma me siyanta zaizo Inna zata siyar kuma Aunty Zara'un ma Abuja zata koma wajen ƙanwar mamanta! Daga haka ta katse wayar. Kallon wayar yatsaya yi kafin ya mike ya fice daga ɗakin... Shaf ya manta da Mami ta ce yaje gidansu Bilkisu.. babu wanda yasan ya shigo gidan, wanka yayi ya shirya cikin farin yadi mara nauyi sannan ya fito.. kusan karo sukayi da Mami wadda take son shigowa falo shi kuma ya sako kai zai fito.. kallonsa tayi daga sama har ƙasa sai kuma ta saki murmushi dan duk tunaninta wajen Bilkisu zaije.. "Ashe haryanzu baka tafi ba? "Eh! Ya amsa dan bai ma gane me take nufi ba.. "toh takalma ne kawai ya rage ba'a zuba ba, kuma gobe zamuje kasuwa idan kuma tafi so a bata kuɗin ta je ta sissiyo ka tambayeta dan na tambayi uwarta ta ce kai ka tambayeta da kanka" sai a lokacin ya gane zancen Bilkisu take masa.. da ok ya amsa yana bata hanya ta shigo sannan ya fice... A kofar gidansu Zara'u yayi parking, yayi mamakin ganin Toyota Prado a kofar gidan ga Saude tana zuba kaya a ciki.. hakan yana nufin da yamman nan zasu kama hanyar Abuja? Ƙanwar mamanta da ba wani sonta take ba? Da sauri ya sakko yana isa inda motar take,matashi ne kamar shi dan zai  ma iya finsa gayu da kwalisa.. "ASSalamu alaikum! Ya faɗa yana miƙa masa hannu.. tas Mustapha ya ganeshi hakan yasa be miƙa masa hannun ba sai kokarin rufe murfin motarsa da yayi. Baya Ammar ya matsa yana kallonsa. Inna ce ta fito tana gyara dankwalin kanta, ganin Ammar a tsaye ya saka ta dage kirji tana fad'in " Munshiga uku, me kazo yi? Uban waye ya faɗa maka zatayi tafiya daka diro mana da yamma haka? Shafa kansa yayi yana tsugunnawa ya gaida ita.. bata amsa ba ta cigaba da fadin " Zara'u dai tafiya zatayi Allah Ubangiji ya bata dan Habuja! Zara'u dake tsaye a kofar gidansu ta kasa karasowa ganin Ammar a wajen. Hangojta yayi ya miƙe tsaye yana karasawa inda take.. "Zarah dan Allah karki tafi" Ɗauke kanta tayi daga kallonsa tana kokarin barinsa a wajen. A gabanta ya tsaya yana marairaice fuska ya ce " Dan Allah Zarah! "Yau naga iya shege! Cewar Inna tana tureshi da duka hannu biyu.. jan hannun Zarah tayi zuwa mota.. "Ke saude buɗe! Ta fada tana kallon Saude dake hararar Ammar. Bude wa Zarah front seat tayi ta shiga tana hawaye sannan ta rufo murfin motar. Ammar na gani Mustapha ya ja motar suka bar wajen da gudu...

*Barka da sallah, Allah y maimaita mana Ameen*

08142904255

Autarmama ce.

MATANA ✓Where stories live. Discover now