chapter thirty eight

518 46 4
                                    

✨ *MATANA* ✨

*Mallakar*
       AUTAR MAMA

*FREE BOOK*

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*Comments*
*Vote &*
*Share fisabilillah*

*038*

           A hankali Zarah ta fara knocking ƙofar gidan su Bilkisu, me gadi ne ya buɗe yana kallonta da kyau ya ce, "Lafiya dai Hajiya? "Wajen Saude nazo" Bai ce komai ba ya ƙarasa buɗe ƙofar ta shigo yana bin ta da kallo. Ajiyar zuciya ta sauke tare da karanto addu'a a zuciyarta sannan ta shiga ƙofar data tabbatar nance hanya. Bakinta ɗauke da sallama ta ƙaraso cikin falo, gabanta ne ya faɗi lokacin da sukayi ido huɗu da Aunty Sadiya, ga Raihan a cinyarta tana bashi tuwo. Kallon kashi tayi mata tana ɗauke kanta ta cigaba da abinda take yi. Xarah bata yi give up ba ta ƙarasa in da take tana tsugunnawa ta ce, "Ina yini? "Kin baro shi chan gidan biki! Tsabar gulma wai ni zaki cewa ina yini, dallah tashi ki ban waje sha³, wato zaman gidan miji yayi daɗi gashi nan har anyi ƙiba, yo ba dole ma ayi ƙiba ba ana samu aci adequate diet wanda a gida babu" Sunkuyar da kai Zarah taji tana jin maganganun suna mata zafi a zuciya. "Mayya kawai! Banda sakarci ma irin na ɗa namiji ka nanewa ƴar talakawa ita ba komai ba, da ace ma tana da kyau ko haske sai a ce kyanta ko farinta ne ya ruɗe shi, amma ba ko ɗaya daga gani kasan aikin asiri ne kuma zamu gamu dake wallahi, Bilkisu bazata cigaba da zama dake ba dan ita kaɗai aka yi Ammar! Ke dai Mayun danginki sai kun haƙura kun bar min ɗa wallahi wato uwarku ta miƙe ƙafa ƴaƴan ta sun samu gidan Hutu ko? "Aunty wai meyasa bakya kama girman ki? Ko da yake babu girman ne sai na jiki, na tabbata Innar mu ta haifeki! Kawai sai ki kama gaya mata magana yadda ranki yake so? Ni idan wani naki yazo gidan nan ina masa wulakanci ne? Ina ƙoƙarin danne fushina da zafin zuciyata dan duk na girmama ki kamar yadda nayi wa Alhajina alkhawa... "Ke dallah rufe min baki sakarya kawai! Ganin na miki shuru bafa shine zai sa ki ɗauka sanyi nayi ba! Yan Iskan yara! Daga haka Aunty Sadiya ta ɗauki Raihan suka wuce ɗaki. A jiyar zuciya Zarah ta sauke tana kallon Saude ta ce, "Ya kike? "Taso muje ɗaki dan Allah, ni duk ta ɓata min rai wallahi" Cewar Saude tana kallonta. Tashi Zarah tayi tabi bayan Saude, bayan sun shiga ɗaki a kan Couch ta zauna tana kallon ƴar uwarta ta ce, "Ashe haka kikai ƙiba Masha Allah" "Bari na ɗauko Abdallah" Ta faɗa tana shiga bedroom.. bata daɗe ba ta fito da Abdallah dake bacci, karɓar shi Zarah tayi tana kallon kyakkyawan yaron ya ce, "Masha Allah, gaskiya ɗan lukuti ne, Ni dana haifi Hydar baki ganshi dan firit ba" Dariya Saude tayi tana zama kusa da ita ta ce, "Kun sha Turai ae, ya jikin nashi? "Da sauƙi alhmdll" Zarah ta bata amsa. "Masha Allah, Allah ya bashi lafiya, Kema sai fresh kike Aunty" Cewar Saude tana dariya. "Ke ai naga ba shi kike yi ba" dariya Saude ta kuma yi tana tashi tsaye ta ce, "Bari na kawo miki abin taɓawa akwai maganar da zamuyi" da ok Zarah ta amsa ita kuma Saude ta fita. Ta ɗan ɗau lokaci sannan ta dawo, abinci ta ajiye a gaban Zarah tana fad'in " gashi nan" Da ok tnx" Zarah ta amsa tana ɗaukar plate ɗin abincin. "Aunty ciki ne fa dani" Ajiye cokalin hannunta tayi tana zaro idanuwanta a kan Saude sannan ta ɗora da faɗin " Ciki kuma? "Eh, dan babu wanda ya sani, da nace zubarwa zanyi ki rubuta min magani na siyo wallahi Aunty haihuwa da wuya kuma ni bansa yadda akayi ba, na dai fara jin sauyi a jikina sai nayi PT kuma ya nuna min akwai ciki"  Cewar Saude cike da damuwa. "A'a karki zubar, kyauta ne fa Allah yayi miki, wasu suna ta nema da miliyoyin kuɗi basu samu ba ke kuma Allah ya baki sai kice bakya so? Ba wani abun wahala a ciki, ki samu kina bawa Abdallah madara kina haɗa masa da breastfeeding, ki raini abinki kuma ki sanar da mijinki karki yarda dai ki zubar ni dai na faɗa miki, idan yaso Abdallah ya ƙara kwari sai ki  yaye shi  a kai wa inna ko kuma na riƙeshi har ɗan da kika haifa yayi kwari" Gyaɗa kai Saude tayi tana ɗorawa da faɗin " Ai Shikanan, kwanaki da Ammar yazo baki ga kayan barka ba wai injiku, na manta ma ban sanar dake ba" "Kinga nima be faɗan ba wallahi, Allah dai ya raya mana Abdallah"  "Amin Aunty, yaushe wai zakiyi wa Hydar ƙani? Dariya Xarah tayi tana kallonta ta ce, "Ai maybe sai nan da 2yrs ko fi ban dai san lokacin da Allah zai kawo ba" "kai haba? Ko dai planning kikayi sbd school? "Ko ɗaya wallahi" Cewar Zarah tana cigaba da cin abincinta. "Ok, Allah ya kawo masu albarka, kishiyarki tayi bari uwarta tayi ta hauka a gidan nan wai asiri ne! Ni kuwa nace dama duk me yin abu gani yake kowa ma yi yake yi, shiyasa masu kyayyawar zuciya suke saurin yarda da mutun sai kuma kiga an cuceshi toh zasu ɗauka kowa yana da kirki! To haka itama asirin take yi shiyasa ta ɗauka asirin akayi cikin ƴarta ya zube, Ni dai ko uffan bance mata ba har tayi ta gama" " Gwada, ki dai na tanka mata ai ba fitowa zaiyi a jikinki ba" 

MATANA ✓Where stories live. Discover now