✨ *MATANA*✨
*Mallakar*
AUTAR MAMA*FREE BOOK*
*EXQUISITE WRITERS FORUM*
*Wannan labarin ƙirƙirarre ne, banyi shi ɗan cin zarafin wani ko wata ba! Sannan idan yayi shige da labarinka/labarinki coincidence ne Yawwa*
*Comments share and vote dinku yana da matukar mahimmanci idan yayi karanci zan maida abuna ba kudi💃*
*Whatsapp group females only please*
https://chat.whatsapp.com/Ib3gwXORbTB1GxcVr0FdAw
*005*
"Mami da kin kirani basai kin taso da kanki ba" Ammar ya fada yana kallon ta. "A'a ai yafi dai nazo da kaina, dama akan maganar kudin make-up ne, kaga za'ayi na daurin aure, kuma za'ayi na kamu sannan na dinner" Shafa kansa yayi kaɗan kafin ya ce " Ok nawa? Mami na murmushi jin bai musa mata ba ta ce, " It's 25k each, but don't worry ka bayar da abinda zaka bayar kawai, sauran zan cika" "Ok" Ya fada yana kallonta. "Yawwa dan albarka, tunda kayi min biyayya zaka ga dai-dai, dama Bilki ce tsarar aurenka wallahi tun kafin ta kai haka nayi maka sha'awar aurenta ban dai furta ba nayi nauyin baki, da Allah yayi dai itace matarka sai gashi Sadiya da kanta tayi magana, kaga yadda Allah keyin abunsa, ka dinga cin abincin wannan ramar taka tayi yawa kaji ko Ammar? "Uhm" Ya fada kamar wanda akayi wa dole. "Yawwa toh naga baka son hayaniya dayawa gobe sai ka wuce gidansu Umar ka huta da ihun yara" "Toh Mami" ya kara fada cikin ladabi. Shafa kansa tayi tana tashi ta fita daga ɗakin.. iska ya furzar me dumi tare da lumshe idanunsa. Washegari da safe da wuri ya bar gidan. Ƙarfe 10 saura Umar ya tashi daga bacci, ganin sangameman mutun kwance a gefansa ya sashi matsawa gefe da sauri yana kare masa kallo. Tsaki yayi kadan a fili ya ce, "Kana da matsala wani lokacin! Ammar baisan yana yi ba saboda bacci yake. Duvet din daya rufa dashi ya cire gaba daya, buda idanunsa yayi kadan yana kallon Umar ɗin.. "Tashi zakayi rana tayi wadancan card din daka barmin cikin closet kasan yadda zakai dasu i have no time for them" Nima! Cewar Ammar yana kara jan duvet ya rufe jikinsa. Karamin tsaki Umar yayi ya sauka daga kan gadon ya wuce toilet. Brush kawai yayi ya fito dan yunwa yake ji. Fa'iza ya tarar a kitchen tana wanke². "Ina me aikin? Ya fada yana daukar cup da spoon. "Ai taje hutu gida, ina kwana? Da lafiya lau ya amsa yana fad'in " Me akayi yau dasafe? Naga dining din wayam" "Doya ce kuma ta kare Hajiya tace kar ayi da kai saboda ko ka tashi baka ci" "Ok dafa min indomie idan kin gama" Da ok ta amsa ta cigaba da aikinta sai sauri take dan by 12am sukayi da su Maryam zata zo su tafi gidan kunshi. A nan falon ya zauna yana shan tea, bata dau lokaci ba ta kawo masa indomie.. ko fara ci beyi ba Ammar ya fito daga daki.. bai ce masa komai ba sai zama da yayi a kujerar da yake zaune.. plate din indomie ya dauka Umar sai kallonsa yakeyi.. hankali kwance ya fara ci kamar dama ance masa nashi ne. "U'r not serious! Cewar Umar yana karbe plate din daga hannunsa ya barshi rike da fork. "Me haka?cewar Ammar yana wani hade rai. Karamin tsaki Umar yayi yana mikewa tsaye zai bar falon. "Ka barni naci please tun jiya da rana banci komai ba" "Bashi mana Umari! Suka juyi muryar Hajiya babba daga upstairs. "Haba Hajiya I'm hungry wallahi! "Bana son sakarci ya kuke abu kamar kananan yara? Ta fada tana sakkowa. Ita dai Fa'iza sauri take ta fito daga kitchen din dan bata so a sake cewa ta dafa wani abun. Ajiye plate din Umar yayi suka fara cin abincin tare. Girgiza kai Hajiya babba tayi dan wani zubin dashi da Ammar din kamar yan 5yrs.
*Abuja*
Throughout yau Ammar bai kirata ba, duk da cewa wani lokacin ma idan ya kira ba dauka take ba amma tana jin sanyi a zuciyarta, yau kam duk ta zama wani iri ko missed call daya beyi mata ba, Ummi na lura da yanayinta tun safe.. tana zaune a daki bayan tayi sallar magriba Farida ta shigo fuska a sake ta ce " Zarah ki fito kiyi kallo inji Ummi" Kai kawai ta gyada mata alamar toh. Farida bata dade da fitowa ba Zarah ta fito, a ƙasan carpet ta zauna ba tare da ta kalli kowa ba. "Ke kullum zaman daki bakya gajiya ne? Cewar Ummi tana kallonta. Murmushin dole tayi tana pretending as kallo take amma a zuciyarta tafiso ta koma ɗaki. "Ummi sai nake ganin a samar mata admission yafi zaman gidan nan da takeyi" Ba ta dauka Yaya Musty na falon ba sai a time ɗin, sau daya ta kaalleshi ta ɗauke kanta. "Tace maka tana sone? Dubansa ya mayar ga Zarah ganin kamar hankalinta baya kansu ya saka shi kiran sunanta. "Na'am! Ta amsa a sanyaye. "Kinason cigaba da karatu? "Eh! Ta amsa masa. "Toh kingani, zuwa karshen shekara za'a fara bada admission tunda bata da jamb sai a nema mata makarantar da ba'a shiga da jamb" "Ok Allah ya bada Sa'a" Ummi ta sake fada idanunta akan TV. "But we can't build her for someone else you know right? Shafa kansa yayi yana murmushi ya ce " I didn't get you Mom! Bata sake ce masa komai ba ta cigaba da kallonta. Zainab ce ta kalli Farida da ke kallon Ummi dan tasan magana Ummin ta fada amma ta kasa gane me take nufi.. Mustapha ne tayi breaking silence din da faɗin " Zanne muku admission keda Zainab sai ku dage da karatu, saboda bangaren health ne dukanku! Ko bazaku iya ba? Da sauri Zainab ta ce " I can't gaskiya bana son stressful work! "Idan na nema muku karkiyi! Daga haka ya tashi ya basu waje. Zarah bata dade a zaune ba ta ce Bacci take ji. Tana komawa daki ta tarar da kiran Ammar har uku. Cikin takaici ta ajiye wayar, amma zuciyarta ta danyi dadi.Washegari ta kama Thursday, gidansu Ammar ya kachame da jama'a yan uwa na nesa dana kusa, yan uwan Abbansa duk sunzo kowa dokin bikin yake yi saboda shine babban ɗa namiji wanda za'a fara aurarwa, har baƙin Aunty Sadiya duk suna gidan su Ammar, amarya da ya'yan kannen mahaifinta da su Maryam sune a chan gidan Aunty Sadiya suna shagalinsu. Ammar tun safe babu inda yaje yana gidansu Umar, har rabon katin da ba'a karasa ba duk Umar ne ya karasa komai. Bayan sallar la'asar Ammar na zaune yana game a wayarsa, kiran Zarah ya gani.. zaro ido yayi sai kuma ya goge idanunsa da kyau dan tabbarwa.. murmushi ya saki kafin ya dauka ta katse, kiranta yayi shima har ta gama ringing bata dauka ba.. "Toh kodai bata san ta kira ba? Ya fada a fili yana kara kallon wayar. Sake dialing number yayi, Shima har ta katse bata dauka ba. Text ya tura mata kamar haka. _I'm so sorry hubby kafin na daga kiran ya katse, i will call you now please pick my call ok?_ ko ajiye wayar beyi ba yaga reply dinta. _Ya shirye-shiryen biki?_ ya karanta sakon ya kai sau uku kafin ya kirata. Kin dauka tayi har ta katse, iska ya furzar da karfi ya kuma yi mata text. _Dan Allah Zarah ki ɗauka_ sake kiranta yayi bayan mintina da tafiyar sakon, har ya fidda ran zata dauka, sai kuma yaji ta dauka amma bata ce dashi komai ba. "Na gode" "Akan me? Ta fada daga ɗaya bangare. "Ƙin daukar wayata mana" da uhm kawai ta amsa masa. " Ya kike? Ya fada yana saurarenta as if his life depends on the phone call. "I'm ok! "Really? Ya fada cike da mamakin amsar data bashi. "Oh so kake ince naka I'm not ok?! Murmushi yayi me sauti kafin ya ce " I like your attitude! Tsuke fuska tayi kamar yana kallonta. "Zarah! Ya kira sunanta cikin cool voice. " Uhmmm! Ta amsa chan ciki. "I love you! Shuru tayi dan bata san me zata ce masa ba. "Kinyi Shuru? Bata kara ce masa komai ba tayi disconnecting din kiran. Kallon wayar yayi yana danyin murmushi ya ce " Zarah! Lumshe ido yayi kadan ya buɗe yana shafa sajen fuskarsa ya kara cewa " U will be mine inshallah! "Wannan murmushi haka kamar kaga Bilkisu? Cewar Umar yana taɓashi.. Tsaki Ammar yayi yana gyara zamansa a kan gadon ba tare da yace da Umar komai ba, ko yaushe y shigo dakin! Umar bai so zancen ya kare a haka ba, ya dauka zai fara fadan nasa. Murmushi yayi yana shiga banɗaki. The next day ta kama wedding day. Za'a daura auren bayan an sakko daga sallar juma'a. Ammar bai tashi ba sai 11am. Umar baya dakin, bathroom ya wuce yayo wanka sannan ya fito ya shirya cikin farin yadi me kyau... Yana cikin fesa turare Umar ya shigo yana ajiye jakunnan hannunsa akan gado tare da sauke numfashi yana kallon Ammar ya ce " Kai fa ba yaro bane da zan dinga binka da kaya, na kai maka kayanka chan gida daka tashi tahowa sai ka ɗebo few daga cikin kayanka ka manta da wadannan! "Tunda ka kawo korafi ya kare! Kwafa Umar yayi, shi kam Ammar fita yayi daga ɗakin dan samarwa cikinsa abinci. Hajiya Babba ce tayi serving dinsa yaci ya koshi. Karshe 12 suka wuce masjid. Sai da suka dawo gida ya canza kaya sannan suka wuce wajen daurin auren wanda aka daura karfe 2 da yan minti.. Sai bayan 4 sannan Ammar da Umar suka dawo gida saboda reception din da akayi. A kan gado ya kwanta bayan ya cire babbar rigarsa yana jin kansa ya dan sarawa. Babu kowa a gidan dan Hajiya babba ma ta wuce chan gidansu Ammar din, Fa'iza dama tun jiya data tafi bata dawo ba. Bayan isha'i aka fara shirin tafiya dinner, cikin golden yellow Ammar ya shirya yayi matukar yin kyau, sam besan kalar da kayan da BILKISU zata saka ba kenan.. har ya kammala shirinsa suka fito tare da Umar, abokan Umar ne yawanci dan shi bai wani tara friends cox yana da wuyar sabo. A harabar gidansu Ammar, Umar yayi parking saboda amarya na ciki.. kin fitowa yayi daga motar har amarya ta fito tare dasu Maryam.. Masha Allah tasha kyau kam sai kyalli take tun daga kan fuskarta har zuwa kayan jikinta.. doguwace, fara duk da cewa anyi mata makeup hakan bazai saka a kasa gane kalar fatarta ba idanunta a ƙasa she looks so innocent Maryam a side ɗinta na hagu Fa'iza kuma a side dinta na dama, ko wacce fuska cikin annuri.. back seat Umar ya bude mata tashiga sannan ya rufe yana dan taba baki.. kallonsa ya mayar kansu Farida ya ce " Ga motar su Auwal ku shiga kuma ku dawo a ciki, akasin hakan kunsan sauran! Bai jira cewarsu ba ya shiga mota. The journey was silent gaba daya khamshinta ya cika motar.. tunda ya kalleta sau daya be kara mata wani kallon ba.. kusan a tare suka iso tare da su Fa'iza, hotuna kam an zuba su kafin a shiga cikin hall ɗin.. cool music ne ke tashi lokacin da amarya da ango suka shigo. Fatima na kallon Fa'iza ta ce " Kin tura? "Of course yes! Da me zan jira? Dariya Fatima tayi ta ce " Good! Daga haka suka cigaba da takewa amarya da ango baya har zuwa wajen zamansu. Har lokacin word daya be shiga tsakaninsu ba. Anyi dinner Wanda ya amsa sunan dinner Mami Aunty Sadiya da kuma autarsu Aunty Khadija an bude bakin aljihu anyi wa yara liki masu rawa, ko da aka bukaci amarya da ango a filin Ammar beyi musu ba dan baya son kunyata family dinsa, duk abinda akayi ya bada hadin kai 100% kai kace dama chan yana son abun a ransa. Fa'iza vd kawai takeyi kamar dama shine aikinta. Sai 1pm sannan aka watse. Har suka koma gida ko kala bai ce mata ba. Gidan Mami ta kwana shi kuma wajen Umar. Washe garisu Fa'iza suka je gidanta akayi yan share² da goge² dan anjima da yamma za'a kaita dakin mijinta.......
Autarmama ce