✨ *MATANA* ✨
*Mallakar*
AUTAR MAMA*FREE BOOK*
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*
*Comments*
*Vote &*
*Share fisabilillah**043*
Fatima na zaune gaban Mami sai rusa kuka take yi. "Wannan ai sakarci ne da wauta! Wani irin kazamar magana kika faɗa min ne haka Fatima? Ina iliminki da karatun islamiyyar ki ya tafi? Ina tunaninki da imaninki ya tafi? "Dan Allah Mami kiyi haƙuri wallahi Allah na gane kuskurena shiyasa ma har na faɗa miki ko zaki dawo da Aunty Sadiya kan hanya" "Ai Shikanan, shi Hafiz ɗin yace ya sake ki ne? Girgiza kanta tayi sannan ta ce, "A'a cewa yayi kawai na dawo gida sai na haihu na koma gidan shi" "Ina zuwa" Cewar Mami tana ɗaukar wayarta tayi dialing number Ammar. Bugu ɗaya ya ɗauka.. "Kazo gida ka same ni yanzu idan kasan baka wajen aiki" da toh ya amsa sannan ta kashe wayar. Sosai Mami ta yi wa Fatima faɗa da nasiha me shiga jiki, zuwa yanzu ta sa re da lamarin Sadiya gaba ɗaya. Ammar bai ɗau lokaci ba ya zo gidan. Ɗakin Mami ya shigo bakin shi ɗauke da sallama. Mami ce ta amsa sannan ya ƙaraso ya zauna a kan Couch idanun shi a kan Fatima dan bai san ma ta baro gidan shi ba. "Yaushe kika dawo? Kasa bashi amsa tayi sai hawaye da take yi. "Mijinta ne ya ce ta dawo gida" "Eh na sani Bilkisu ta sanar dani ya ce ta zauna a gida wani aikin gaggawa ya taso masa ya tafi UK" "Toh karya suke maka, Hafiz dai yace ta dawo gida wai har sai haihu tukunna saboda ta fiye tsirfa kasan dama Fatima da kwaɗayi ballantana kuma ace ga ɗanyen ciki" "What nonsense! Saboda wannan zai ce ta dawo gida? Bashi da hankali ko me? Haka aka yi wa ƙanwarshi dake aure a wani gidan? Ammar ya faɗa ransa a ɓace. ", Shi ne ai, nima banji daɗi ba kuma ban tsanmaci hakan daga gareshi ba, be kyauta ba sam, yanzu so nake ka sameshi kaji idan ma wani abun take masa wanda taƙi faɗa sai aji ko? Nunfashi ya sauke yana amsawa da "Shikenan toh" "Yawwa, kuma ku dage da addu'a kai da matarka Zarah kaji ko? Shafa kanshi yayi sannan ya amsa da " In sha Allah" "Naji Umar yace bata da lafiya, hope dai ba jikin bane? Mami ta kuma faɗa tana kallon shi. "Eh Mami" "Ok, Allah ya bata lafiya, ya maganar makarantar Raihan? Kaga dai Maryam tana zuwa dashi kuma yana so duk da baya magana" "Hakane ni rashin maganar shi ma ta fara damu na, yaro shekara biyu ace ko sunan Umman shi baya faɗa sai dai yaji abinda ake cewa? Cewar Ammar cike da damuwa. "Babu wata matsala wani lokacin ai yana furta wasu kalmomin, mu dai tunda yazo gidan nan yana dan yi magana irin su uwaki da bani, ganin ya fara iya zagi ya saka nace gwanda Maryam ta dinga zuwa dashi Islamiyya" ƙaramin tsaki Ammar yayi yana fad'in "Laifin Bilkisu ne abu kaɗan ta zageshi ba dole ya koya ba" "Ai yanzu dai ya bar hannunta har sai yayi wayo in sha Allah" dubanta ta mayar kan Fatima dake hawaye ta ce, "Ki tashi ki wuce dakin ku" A hankali tashi ta wuce jikinta duk ba kwari. Shima Ammar miƙewa yayi yana kallon Mami ya ce, "Shikanan? "Eh shikenan ka gai she da Zaran" Da tohm ya amsa sannan ya fito ya wuce gida dan ko isa gidan beyi ba Mami ta kirashi. Bilkisu ya gani a falo tana yanka cabbage kuma tana kallo. "Ki yanke hannu kizo kina kallona idan ban kara yanka ki b" Ya faɗa yana haɗe mata rai. Murmushi tayi tana ajiye wuƙar hannunta ta ce, "Wallahi series ɗinne bana so ya wuce ni shiyasa" "Ok ai sai ki danna pause tunda naga DVD ne kar kije ki yanke hannu" "Ok" Ta amsa tana sakar masa murmushi. "So yanzu har wani exchanging ɗin murmushi suke yi? Ko dai ya fara sonta? Zarah dake bakin ƙofar ɗaki ta ke ayyanawa a zuciyarta. Ammar na ganinta murmushi shi ya faɗaɗa. "Ya jikin? Ya faɗa yana kallonta. Da lafiya ta amsa ta ƙarasa fitowa, da sauri Bilkisu ta miƙe tana kallonta ta ce, "Me kike so? Da kin kira ni ai" Banza Zarah tayi mata ta wuce kitchen, a nan falon ta bar su ita da Ammar. Jikin bilkisu a sanyaye ta kalli Ammar ta ce, "Ban san meyasa take haka ba, I'm trying my best wallahi, kuma ko abinci na kai mata na lura bata ci ashe Rabi'u take bawa a leda ya kai wa karnuka" Bilki ta ƙarashe maganar tana goge kwallar data zubo mata. "Ita Zaran? Ammar ya faɗa cike da mamaki" "Eh amma dan Allah kar kayi mata zancen dan Allah " bai ce komai ba ya nufi ɗakin Zarah, ita kuma murmushi tayi tana goge idanunta da kyau ta ce, "Zaki gane! Ni kuwa nace ina fatan plan ɗin ku bazai zama sukar rushewar farincikin kowa ba. A hankali take cin taliyar data dafa ko miya bata saka mata ba amma mugun daɗinta take ji. "Kin kyauta kenan? Ammar da shigowar shi kenan ya faɗa yana kallonta. "Dan Allah Ammar ka kyaleni da drama ɗin matarka, bani da lafiya a barni naji kai na" "Na sani ai, abinda kika yi baki kyauta ba, meyasa zaki dinga bawa Kare abincin data kawo miki? Sai a lokacin ta kalle shi ta ce, " Saboda me zanci abinda ta bani? Ko so kake a zubar min da ciki ko a kashe ni? "Wai meyasa kika kasa fahimta ne? Yarinyar nan fa ta sauya hali dan Allah Zarah kar ki dinga sakawa muna samun sabani ni da ke! Cike da masifa ta ce, "Dole ka daina ganin lefinta tunda ka fara sonta! Ni dai babu abinda zai rufe min idanu na! "Ok da na ce miki bana sonta? She's my sister after al... "Kaga ya isheni! Dama nasan kana sonta kawai kana pretending ne, halinku na maza kuma sai dai na bawai wata labari, kaje kayi ta sonta! Daga haka ta dungurar da plate ɗin taliyar a kasan rug. "OMG! Zarah! Ya kira sunanta da karfi dan sosai yarinyar take son hargitsa masa tunanin shi. "Ƙarya nayi? Meyasa kake irritating ɗina? After all I'm not feeling well, Dan Allah ka kyaleni da abinda nake ji" Cewar Zarah kamar zatayi kuka. Iska ya furzar yana kallonta da kyau ya ce, "Yes i do love her but as my sister, babu yadda za'ayi in ce bana sonta kwata² amma ki gane my love for you is far far different than my love for her, Xarah ke kaɗai ce macen da zuciyata ta aminta da ita kuma take ƙauna bansan me kike son mayar dani ba, please Zarah ki bani kwanciyar hankali" "Oh! Ni ce nake baka tashin hankali dama? Duk rashin kwanciyar hankalin da Bilkisu da Aunty Sadiya suke saka ka baka gani ba sai ni zaka ce ina baka tashin hankali? Bai ce ita komai ba ya fice ya barta dan idan ya tsaya biye mata yanzu zasu iya yin faɗa wanda be shiryawa faruwar hakan ba. Yana zaune lamarin Zarah ya ishehi Bilkisu ta na kallon shi ta ce, "Ya dai? "Nothing kawo min tea kar ki saka komai including sugar" "Ta yaya zaka sha shayi ba sugar ba madara ba Milo? "Lipton ɗin kawai nake so, idan kuma zaki tsaya yi min musu go ahead! Ajiyar zuciya ta sauke tana fita. Bata ɗau lokaci sosai ba ta dawo da kofi da mini tray a hannunta. Karɓa yayi yana fad'in "Tnx" Zama tayi a gefanshi tana sassauta murya ta ce, " Ya naga kamar ranka a ɓace? Shuru yayi yana sipping ɗin tea ɗin. Kwanciya tayi a kafaɗar shi tana fad'in " Bana so kacewa Zarah komai a kan abinda na faɗa maka Saboda bana son muyi faɗa Nima ban so na faɗa maka ba kawai dai abun yana damu nane, Nasan matsayina da Zarah a wajenka akwai bambanc... "Is true but kar na sake ji, dukan ku Matana ne, You both have equal right on me" "Ok" Ta faɗa tana tashi ta barshi a wajen. Ita kaɗai tasan yadda take daurewa take cijewa a kan abinda take yi, for sure so take Ammar ya kori Zarah da kanshi tunda ta sanadiyyar ta ne ya saka baya sonta kuma be damu da ita sosai ba, soon komai zai zama labari wannan shegen cikin jikin nata ma sai ya zube dan bazata yarda wata ta haihu ba bayan ita. Ɗakinta ta wuce tana ciro wayarta a charji tare da yin dialing number Aunty Sadiya. Bugu uku ta ɗauka tana fad'in " Bilki?' "Na'am Umma, dama kiranki nayi naji ya kuka yi da kangarau? "Anya kuwa Bilki? Nifa bana son harka da ƴan daba dan basu da alkawari sam" "Tunda Fahad ne ya haɗaki da su kuma ya tabbatar miki basu da matsala meyasa kike damuwa ne? "Shikenan Bilkisu, ki dai cigaba da yin yadda na faɗa miki ko banza zaki dinga haɗa su faɗa, in sha Allah watarana zaki wayi gari ki ganki ke kaɗai a matsayin matar Ammar! Bana kaunar zarah sam wallahi amma dai shikenan" "Toh shikenan sai anjima" daga haka ta katse wayar tana ɗan murmushi ta ce, " Shi da kan shi zai tsaneki wallahi kuma ke kanki zaki zaɓi rabuwa dashi, banso ma rayuwar tayi miki daɗi har haka ba, naso ace mun zame miki bala'i ni da ƴan uwan Ammar! Amma kash kannen shi duk zuciyar uwarsu suka ɗauko amma yanzu zata yi abinda kowa ma zai huta! Kwanciya tayi a kan gado tana tunanin abinda suka shirya ɗin wanda tana da tabbacin baza'a samu matsala b. Zarah kuwa rasa me ke mata daɗi tayi gaba ɗaya ta rasa in da zata saka kanta taji daɗi tayi har dare tana kwance a kan gado ga ciwan kai. Abinci Ammar ya shigo mata dashi, calmly ya ce, "Ki tashi kici abinci" "Bana jin yunwa" Ta amsa masa tana backing ɗinshi. "Bana wasa fa! Ki tashi kici if not for your sake toh for the Unborn baby" Shuru tayi tana tunanin abinda ya faɗa mata a kan Bilki ɗazu. Hawaye ne suka fara zubo ta gefan idanuwanta tana jin wani irin kishi. "Zarah! Ya kira sunanta. Duvet taja ta rufe jikinta tana share hawayenta. Yaye duvet ɗin yayi yana fad'in " Meyasa kike son yi min gardama? Tashi zaune tayi tana kallon shi tare da goge hawayenta. Taliyar ta ɗauka ta zuba mata idanu kamar yau ta taɓa ganin taliya. "Kiyi haƙuri kici" Cewar Ammar so Calm. A hankali ta miƙe ta bar shi a bedroom ɗin ta fita tare da plate ɗin taliyar ta. "Zarah! Cewar Bilkisu tana kallonta. Ko kulata Xarah bata yi ba ta nufi kitchen, wake ta auno a store ta tsince sannan ta ɗora. Fitowa tayi daga kitchen ɗin still Bilki na falon. Dariya Bilkisu tayi tana fad'in "A juri zuwa rafi Zarah! Kinsan idan baki iya kama ɓarawo ba shi zai kama ki! Nan ma Zarah bata kulata ba ta wuce dan already tasan hakan zai iya faruwa batayi mamakin Bilkisu ba ko ƙadan. Har lokacin Ammar na zaune. Ko uffan bata ce masa ba ta nemi waje ta zauna. "Allah ya baki haƙuri" Ammar ya kuma faɗa idanunwan shi a kanta. "Haƙurin me zaka bani? Ai ba laifi kayi min ba kawai ka fad'i abinda ke cikin zuciyarka ne, kuma meyasa zanji haushi? After all she's your wife, so why are you apologizing? "Ok shikenan tunda haka kika ce, kinsan i hate this kind of punishment ko? Ki cigaba da baƙan ta min rai kullum! Is hardly dama ka nunawa mace tsantsar so bata maka wulakanci ba, wannan dabi'ar ku ce ta Mata, duk inda ake sonku ake riritaku kamar ƙwai kun fi yin wulakanci, ranar da babu ni zaki yi dana sani! Ki cigaba da min abinda kike so Zarah! Daga haka ya fice. Kuka ta fashe dashi me ƙarfi, runtsa idanunsa kawai yayi ya ƙarasa fita daga falonta dan yana jiyo sautin kukanta. Har ƙarfe 10na dare Ammar be dawo ɗakin ba, waken ma data dafa kasa ci tayi dan bata da appetite. 1am saura ya shigo bedroom ɗin nata kunna fitilar ɗakin yayi yana kallon direction ɗin da take, ta ƙudunduna cikin bargo, kashe filitar yayi yana fita ya koma ɗakin shi. Wa she gari da ƙyar ta iya shirin makaranta, a compound ɗin gidan ta gashi suna magana da Rabi'u, tsayawa tayi dan ya kammala cox bata da kuɗi a hannunta. Bayan ya gama abinda yake yi ya nufota, sunkuyar da kanta tayi ta ce, "Kuɗin makaranta" "Muje ciki" daga haka ya wuce ya barta. Itama bin bayan shi tayi. Ɗakinshi ya shiga bai daɗe ba ya fito tare da Bilkisu dake faɗin " Wai har yanzu ba'a buɗe Portal bane? Nima na ƙagu na fara zuwa" "Idan an buɗe ai zan faɗa miki ko? Saurin me kike? In dai nursing school ce zaki yi bayani" Cewar Ammar yana miƙawa Zarah 2k. Karɓa tayi tana yin godiya sannan ta wuce. "Yau bazaka kaita bane? "No, kyaleta! Ya bai wa Bilkisu amsa yana komawa ɗakin shi wani evil smile tayi tana ɗan cize lebanta na ƙasa. Gaba ɗaya Zarah haka tayi yinin makarantar duk jikinta ba daɗi ko jira a tashi ba tayi ba ta baro school ɗin saboda ciwan kai da jiri da take ji. By 3 ta isa gida. Maryam, Fa'iza da ita Bilkisu ta gani a falo sunci uwar sabada dan dama tun daga gate take jin tashin ƙida, sosai falon yayi kacha². Ko da tayi sallama babu wanda ya amsa mata hakan yasa ta wuce ɗakinta direct. Bacci take so tayi amma kiɗansu ya hanata dan ƙara mata ciwan kai ma yake yi. Kasa jurewa tayi ta fito falo tana kallon Bilkisu ta ce, "Dan Allah ku rage volume ina ciwan kai" "Ba fa za'a hana mu jin daɗi ba wallahi gidan yayan mu ne! Cewar Fa'iza tana huhhura hanci. Ƙaramin tsaki Zarah tayi tana kallonta ta ce, "Kije kiyi tutiya da ɗakin mijinki ba gidan yayanki ba! Nan gidan mijina ne i have the right to decide! "Ahayyyyyyeeee! Daɗinta dai da ubanki bane ya siyo mata kayan kallon da spikun da aka kunna ƙidan ba! Ko da kuɗin faskare aka siyo? Ko kuma da kudin gawayi da kuka? Faɗa min mana! Ko kuma da kuɗin dadiro? Waye bai san Innar taku dadiro ta dinga yi bayan mutuwar me faskare ba? Waye bai sani ba? An mutu an barta da sauran ƙuruciya ace har ta tsufa bata sake aure ba? sha'awa duk tabi ta dameta yo bama dole ta dinga bin maza ba! Da dai bamu san asalin balbela ba,..... Fa'iza ta ƙarashe maganar tana dariya. Tafawa sukayi duka su ukun. Sannan Bilkisu ta ɗora da faɗin " Ai halin uwar aka kwaso ciki harda satar gwal a biki" Xarah kuwa kasa motsi tayi tana jin komai nata ya tsaya. Ta kai minti 5 a ƙame kafin ta juya ta koma ɗaki zuciyarta tana mata wani irin suya ga shi ta yi ma ta nauyi. A kan kujera ta zauna da ƙarfi tana tunano ƙazafin da akayi wa innarta. Kuka ta fashe dashi me ƙarfi sosai, wannan wace iriyar masifa ce ta saka kanta a ciki? Wace iriyar rayuwa ce ta jefa kanta? Ta daɗe tana kuka kafin ta tashi ta nufi daki, akwati ta ciro a sip ta kwashe kayan ciki sannan ta fara zuba kayan da zata buƙata, ita kam bazata iya rayuwar gidan nan ba, kasheta kawai suke so yi! Da me ake so taji? Kuka take sosai har ta kwashi abinda zata kwasa, uniform ɗin jikinta cire ta saka na gida sannan ta saka hijabi ta fito falo, da idanu suka bita, sai kuma suka kwashe da dariya Fa'iza ta ce, "Kin huta wallahi! A tafi a bar miki Mijinki! Bata kula su ba ta fice dan bata jin idan ta tanka musu zata kwashe musu da kyau a yau ɗinnan. Gidansu ta wuce direct ba kolo². Inna na shanya ta ganta ta shigo da akwati ga fuska duk ta kumbura alamar an sha kuka. Sakin mayafin tayi tana dafe ƙirji ta ce, ' Ba dai ya sakeki ba ni Aminatu? Kuka Zarah ta fashe dashi tana rungume inna da ƙarfi. "Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, Inna wa inna ilaihi rajiun, ai shikanan, shikenan Zarah! Cewar Inna idanunta na kawo ruwa. "Dan Allah Inna ki yafe min" Cewar Zarah dan gani take itace silar zagin da aka yi wa inna a yau ɗinnan. "Ba kiyi min komai ba Zara'u! Shegan naci da ƙwallafa rai a kan abu irin naki ne ya janyo miki" Inna ta faɗa tana sakinta. "Ki wuce ɗaki ki kai kayan ki, ai ba tsufa kika yi ba Allah zai kawo wanda ya fishi in sha Allah" "Inna ba saki na yayi ba" Cewar Zarah tana goge idanunta. "Kamarya ba saki ba? Inna ta faɗa cike da rashin fahimta. Hawaye na zuba a idanun Zarah ta ce, " Na gaji! Inna na gaji da zaman gidan kashe ni suke s... Xarah bata iya ƙarashe maganar ba sakamakon shaƙuwa data fara yi, riƙeta Inna tayi tana fad'in " Kwantar da hankalin ki kar kije ciwanki ya tashi dan Allah ya isa ba sai kin ban labari na fahimta" Jini ne ya fara fitowa ta hancinta, runtsa idanunta tayi inna kuwa innalillahi ta fara ambato, da kyar ta taimakawa Zarah ta zauna. Da sauri ta ɗauki wayarta a kan taga ta fita waje neman wanda zai kira mata Ammar. Luckily taga ƴar makotan. Da sauri ta ƙarasa in da take ta ce, "Ungo nan dan Allah kira min Ammaru, zaki ga an sa Ammaru" da toh ta amsa sannan ta shiga neman number cikin ƙanƙanin lokaci ta danna kiran, ta miƙawa Inna, inna da ko mayafi babu ballantana takalmi ta koma cikin gidan wayarta kare a kunne. A kwance taga Zarah tana ,hawaye. Ammar be ɗauka ba, kamar inna zatayi kuka haka taji, tasan yanzu idan taje wajen su baffa kafin suzo idan ma mutuwa Zarah za tayi zata iya mutuwa kafin suzo. Ganin babu sarki sai Allah ya saka ta saka jikakken hijabi ta fita neman Napep, bata ɗau lokaci ba suka dawo da me Napep ɗin, shi taimaka wa Zarah zuwa cikin Napep ɗin dan sam jikinta is not functioning tayi wani weak. Bayan sun isa asibiti nan ma sun ɓata lokaci kafin a tafi da Zarah Emergency, ko kuɗin Napep mutumin bai amsa ba sai fatan samun lafiya da yayi wa Zarah sannan ya wuce. Basu ɗau lokaci ba aka fito da ita zuwa ward. Inna sai binsu take tana fad'in "Allah zai baki lafiya Zara'u" bayan an bata gado anyi duk abinda ya dace aka rubutawa Inna abubuwan da zata siyo, fita tayi ta siyo dan dama ta ɗauko kuɗi kafin su taho. Bayan ta dawo Nurse on duty ta duba komai ta siya sannan ta ce da Inna "Ina mijin nata? " Baya nan" Cewar Inna tana kallonta. "Toh yasan dai tana da juna biyu ko? "Eh ya sani" Inna ta amsa dan tasan bazai rasa sani ba tunda har Zarah tana da ciki. " Yasan tana da ciki yake barinta cikin wannan yanayin? Allah yaso ma cikin bai samu wata matsala ba, SOB(shortness of breath) fa ta samu, if not kinyi hanzarin kawota za'a iya rasata fa! Kuma yasan tana da hawan jini duk yake barinta cikin wannan yanayin? Be kamata ba sam, ya kamata a dinga kula da mara lafiya kunji ko? "Toh likita"Inna ta amsa tana kallon Zarah. Kasan cewar she's semi- conscious bata san me suke ba tana dai ɗan ji abubuwa ƙasa-ƙasa sosai. Inna na zaune da Zarah har dare babu wani improvement gashi ko waya bata ɗauko ba. Wa she gari Zarah ta dawo dai² kamar ba ita aka kawo ranga² jiya ba, all her vital signs are within normal range except her BP. Kunu kawai inna ta siyo mata ta sha sannan ta ce zata je gida ta dawo tunda an bata magani. Inna bata ɗau lokaci ba ta dawo ta ɗauko duk abinda zasu buƙata kafin a sallame su. Zarah na kallon sauran members ɗin dake dakin dan babban daki aka kaita, sosai PTs ɗin suke jin jiki duka kuma medical cases ne. Ajiyar zuciya tayi tana kallon inna dake Gyan gyadi ta ce, "Inna! Da sauri Inna ta kalleta tana fad'in "Jikin ne? "A'a inna kawai dai ciwan kai ne nasan kuma zai tafi a hankali. "Toh sun ce ai likita zata zo anjima sai na faɗa mata ko? "Zan faɗa in sha Allah" Zarah ta faɗa tana kwanciya. Ana ward round aka ƙara assessing dinta kuma aka tabbatar she's ok kawai BP ɗinne matsala, discharge likitan ya rubuta musu, sosai Zarah taji daɗin sallamar. Bayan azahar suka dawo gida. Ko da wasa Inna bata tayar mata da zancen ba haka itama Zarah bata kuma cewa inna komai a kan maganar ba. Da daddare tana zaune rike da handout amma sam ta kasa karatun maganganun Fa'iza sunki barin zuciyarta sai zafinsu take ji sosai. Ammar ne ya shigo bayan yayi sallama. Da sauri ta tashi zaune dan da a kwance take. Inna dake ƙulla kuka a leda ta ɗago tana amsa sallamar. "Ina yini inna? "Lafiya" Inna ta amsa babu yabo babu fallasa. "Na dawo gida Bilkisu take faɗa min Zarah ta tafi bayan minor misunderstanding ya shiga tsakaninsu, dan Allah Inna kiyi wa Zarah faɗa wallahi tana behaving wani iri kuma bana son irin haka" "Shikenan ai, Allah ya kyauta" Inna ta faɗa ba tare da ta kalleshi ba. Shafa kanshi yayi dan things ain't okay daga gani" Ajiyar zuciya yayi yana kallon inna ya ce, "Kiyi hakuri" "A'a ni me kayi min Ammar? "Naga kiranki jiya kuma ina meeting a lokacin dana fito kuma nayi ta kiranki baki ɗauka ba, naxo na tarar da gidan a kulle, na kuma dawowa da dadaddare shima still a kulle, yau ma nazo da safe shima a kulle, so na wuce wajen aiki ban dawo ba sai yanzu wallahi ko gida banje ba nazo nan" Tashi Zarah tayi ta wuce ɗaki" da idanu kawai ya bita. "Ni bakomai ae" Cewar inna tana cigaba da aikinta. Tashi Ammar yayi ya shiga ɗakin Inna a zaune ya ga Zarah tana goge hawaye ga cannula a hannunta kamar dai tana karbar allura. "Me ya faru? Ya faɗa yana ƙoƙarin riƙe hannunta. Da sauri ta miƙe tana fad'in " Dan Allah ka tafi " "In tafi ina? Faɗa min meyafaru? "Ba Bilkisu ta faɗa maka ba? Me kake son sani kuma? Ta faɗa tana kallon shi da jajayen idanunta. "Calm down mana kinsan irin wannan condition ɗin bai da daɗi a gareki ko? Kuma kinsan kina da ciki dan Allah ki kwantar da hankalin ki" " Idai hankalina kike so ya kwanta ki zo mu tafi meyasa zaki bar gida haka kawai? "Oh Haka kawai? Bayan duk abinda kayi min? Haka mukayi alkhawari dakai kafin na aureka? Irin zaman daka tanadar min kenan daman? Baka taɓa warning ƙannenka a kan zagin na gaba dasu ba? Baka taɓa yi musu huɗubar illar maltreating ɗin wani ba? Baka taɓa faɗa musu su ma Mata ne watarana za'a musu irin abinda sukeyi ba? Baka taɓa faɗa musu uwa uwa ce ba? Wani ikon suke dashi da zasu kiran Innata da Some thing so disgusting like Ashawo? What right do they have? Me kuke takama dashi Ammar? Tell me! Ta fada da karfi tana kallonshi. Kasa magana yayi dan shi sam ba abinda aka sanar masa ba kenan. "Dan Allah just get out! Ammar wallahi ko kai ne autan maza na haƙura da aurenka! Zan iya jure komai amma banda cin zarafin iyayena! Dan Allah ka fice! Ta kuma faɗa da karfi! Da sauri inna ta shigo tana fad'in "Rufa min asiri kar mu kuma komawa asibiti dan Allah! Kuka Zarah ta saki tana komawa kan gado ta zauna, sosai maganganun Fa'iza suke mata ciwo fiye da tunanin me karatu. Zuciyar Ammar a 100°c ya nufi gidan su, already yasan Faiza da Maryam sunje gidan shi dan Mami ta faɗa masa. A falo ya ganshi har Fa'iza dan holiday tazo yi wa Mami, belt ɗin jikin kayanshi ya cire yana kamo Maryam, ihu ta ƙwalla da ƙarfi kafin ta sake yin wani ya fara tafkar ta, ihu take tana kiran sunan Mami, ai kuwa da sauri Mami ta fiti tana fadin "Lafiya? Ganin Ammar yana tafkar Maryam ba ji ba gani ya saka ta faɗin " Lafiya Ammar? Bai ce komai ba ya saki Maryam dake kuka ya nufi ɗakin su dan tuni Fa'iza ta cika wandonta da iska. 'ki buɗe ƙofar kafin na buɗe da kaina if not wallahi sai na fasa miki jiki" "Dan Allah kayi Haƙuri" Cewar Fa'iza tana sauke numfashi. "AMMAR wai lafiyan ka kalau kaxo kawai kana tafkar min yara? Fatima ce ta fito daga ɗakin Mami tana kallon shi. "Ke ɗauko min spare key a ɗakin Mami" tsayawa tayi tana kallon shi. "Zaki wuce ko sai na zabga miki mari?! Ya faɗa cikin tsawa, da sauri ta koma daki bata daɗe ba ta dawo da makulli. "Ammar ya isa haka magana fa nake! Sanin Mami ne irin fushin Ammar da baya sauka da wuri kuma baya irin wannan fushin sai an kai shi maƙura. Buɗe kofar ɗakin yayi Fa'iza kuwa toilet ta shiga ta kulle tana barin key jin a jiki. "Wallahi idan baki buɗe kofar nan ba na shigo sai kin raina kanki! "Mami dan Allah ki bashi haƙuri" Cewar Fa'iza cike da tsoro. "Buɗe ƙofar Fa'iza ki miƙa hannu ya dake ki" Cewar Mami. "Wallahi kasheni zaiyi! Ta faɗa daga cikin toilet. Dukan kofar Ammaru yayi Mami tana masa magana amma ko jinta bayayi. Gaban ƙofar taje ta tsaya, da jajayen idanunsa ya kalleta."Ban isa dakai ba kenan? Me haka kake yi? "Mami! Mami dan Allah ki matsa idan bana zane su zasu ɗauka tsoransu nake ji! Dan ubansu Xarah Sa'ar su ce? Ko danni bazasu girmama matata ba? Fa'iza ki fito if not Allah sai dai ki kwana a toilet kuma zaki gane kuranki" "Wallahi duk abinda tace maka karya take" Cewar Fa'iza daga cikin banɗaki. Maryam data daku iya dakuwa tana kuka ta ce, "Wallahi babu abinda nace mata saboda Mami ta hanani, Bilkisu ce da Fa'iza suka yi ta zaginta har da cewa innarta Ashawo shine ka kamani ka dakeni" ta ƙarashe maganar tana fashewa da kuka. "Wallahi ƙarya take! Cewar Faiza dake bayi. "Mami dan Allah matsa" Ya faɗa yana gyara belt ɗin hannun shi. "Naƙi na matsa, ai ka sarara mata dai kasan hutu tazo ko? "Da ita, Maryam da Fatima duk ɗaya na ɗaukesu! Hukuncin da zan yanke akan su Maryam itama shi zan yanke a kanta wallahi! "Ai Shikanan! Mami ta faɗa tana matsawa dan tasan bazai taɓa iya karya ƙofar ba. Ga mamakinta handle ɗin ya karya yana dukan ƙofar da ƙarfi ai kuwa ta buɗe sai ga Faiza ta saman toilet seat tana yarfa hannu. "A hankali dai" Cewar Mami dake ƙofar toilet ɗin. Ammar kuwa janyo ta yayi tana ta masa hauka, tsaf ya zaneta ya fasa mata jiki sannan ya fito daga toilet ɗin yana fad'in " in ga shegan da bai fasa zagar min mata ba a cikin ku tunda baku da kunya" daga haka ya fice ya bar gidan. Bayan ya koma gida Bilkisu an sha wankan cikin night wears masu kyau ta gyara gashinta ta sake shi sai ƙhamshi take abunta, tana jin shigowar shi ta ƙara turare, shuru² bai shigo ɗakinta ba, tashi tayi ta nufi nashi ɗakin a zaune ta ganshi yana danna computer. Zama tayi a gefanshi cikin yauƙi ta ce, "Yaya! "Will you get lost?! Ya faɗa yana mata wani side look. Da sauri ta matsa daga gefan shi dan taji tsoro. " Me kika ce min ya faru ɗazu? Ya faɗa yana cigaba da aikin shi. "Ruwa na zubar ina shirin gogewa Zarah ta fito ta kusa zamewa shine fa tace wai ina sane so nake na zubar mata da ciki, haka tayi ta masifa ina ta bata haƙuri amma bata haƙura ba shine ta kwashe kayanta ta tafi wai ta gaji da zaman gidan" "Ok, yayi, ashe dama baki canza ba? Wannan karon kallonta yake yi. "Kamarya? Ta faɗa zuciyarta na bugawa" bai ce komai ba ya ɗauki Wayarsa ya kira Mami, bayan ta dauka ya ce, "Ina Maryam? "Gata a kwance zazzaɓi ya rufeta" "Good for her, bata wayar" Yana ji Mami ta ce ta karɓa, muryarta na rawa ta ce, "Hello" A handsfree ya saka yana kallon Bilkisu ya ce, "Maryam mai-mai ta min abinda ya faru har ya saka Zarah tafiya gida" Muryarta na rawa ta kwashe komai ta faɗa masa in details. kashe wayar yayi yana kallon Bilkisu ranshi ya kuma ɓaci tunowa da yaudarar shi da Bilkin da uwarta suka so yi da suka nuna sun canza ashe they were up to something kamar yadda Zarah ta faɗa....
*A yi haƙuri Please nasan ana yi a ƙara*
Autarmama ce.