✨ *MATANA* ✨
*Mallakar*
AUTAR MAMA*FREE BOOK*
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*
*Comments*
*Vote &*
*Share fisabilillah**034*
Misalin ƙarfe tara da ƴan mintina, Zarah na kwance a jikin Ammar dake latsa wayarsa, tun da suka dawo hotel ɗin take tunanin maganganun ta da Mustapha, ajiyar zuciya ta sauke dan zuwa yanzu ta yanke hukuncin abinda zatayi. "Kasan me? Ta faɗa tana wasa da botirin dake jikin rigar baccinsa. "ina jinki" Ya faɗa yana mai da hankalin shi kanta. "Tunda Hydar ya samu lafiya kawai mu koma gida kaga na samu nayi exams tun kafin a sake ɗaukar wani lokacin" "Ok shi Hydar ɗin a nan zaki barshi? "Eh, ko da an sallame shi Mustapha yace zai zauna a wajensa, kuma kaga dama bayan 3months akwai check up da za'ayi masa" "Ok Shikanan, zan nema mana flight ko zuwa jibi ne sai mu tafi gobe kuma muje kiga gari ko? Murmushi tayi tana gyaɗa kai alamar toh. Bai kara cewa komai ba ya cigaba da latsa wayarsa, ita kuwa Idanunta ta lumshe bata daɗe ba bacci ya ɗauketa. Washe gari da safe Ammar yayi insisting sai sunje wajen Mustapha dan su duba shi, babu yadda Zarah ta iya haka suka shirya, sai da suka fara zuwa asibiti wajen Hydar sannan suka ɗauki hanyar gidan da Mustapha yake, Ammar na riƙe da hannunta suka sakko daga cikin cab zuwa kofar gidan, door bell ya danna sau biyu, yana shirin kara dannawa Mustapha ya buɗe kofar, murmushi ya ɗan saki yana shafa kansa ya ce, "Ashe Dagaske kake" Banza Ammar yayi masa yana jan hannun Zarah suka shigo. "Ya jikin naka? Cewar Ammar yana taɓashi. "Ya kake shafani? Mustapha ya faɗa yana ɗan matsawa. "Kai fa dan air ne wallahi! Shafa ka nayi ko jin temp ɗinka zanyi? Dariya Mustapha yayi yana fad'in "Sorry I'm kidding, ga waje ku zauna" "Munƙi! "Yaya ya jikin? Cewar Zarah Idanunta a kansa. "Lafiya Alhamdulillah" Ya amsa ba tare da ya kalleta ba. Zama tayi a kan kujera tana kallon gidan, yayi kyau sosai komai kuma cikin tsari, magiyar da Mustapha yayi tayi mata a kan ta dawo su zauna tare ce ta faɗo mata a rai! Allah kaɗai yasan zunubin data kwasarwa kanta lokacin da take auren Mustapha! Ita kanta tasan ta cuceshi, tabbas Mustapha be chanchanci mace irinta ba, Mustapha ya chanchanci macen data fita, shi ɗin mafarkin ko wace mace ne, hakuri, kawaici da iya zama da mutun duk yana dashi da sauran abubuwan da ba'a rasa ba.. duk da babu wanda Ammar yayi lacking amma tasan ko kusa bazata haɗa Mustapha da Ammar ba. Ajiyar zuciya ta sauke tana jin ba daɗi a ranta, maybe abinda ta aikatawa Mustapha ke bibiyarta a yanzu! Aure har 3weeks ace babu abinda ya shiga tsakaninta da mijinta auren syy bana kiyayya ba! Anya kuwa ba hakkin Mustapha bane? "Zaraaaaaah! Ammar ya kirata yana taɓa hannunta. Da sauri ta kalleshi ta ce "Me kace? "Ta ina zaki san me nace kina tunani? Faɗa min tunanin me kike? Cewar Ammar yana kallonta. "Ba wani abun bane, kawai ina tunanin exams ɗina ne ko zasu bari" "karki damu zasu bari insha Allah" Kai ta gyaɗa masa alamar ok.. Tea da cookies Mustapha ya kawo musu yana fad'in " abinda zan iya affording by now, sai dai ko matarka zatayi muku girki" "Baka da kai! Muzo gidanka kace matata ce zata tashi tayi girki? Why not ka nemo taka matar? Gansameme da kai ba aure, soon zanje na zuga Ummi da Daddy! Kansa ya shafa yana ɗan murmushi. "Toh ko dai Maryam zan baka? "Ai yana da budurwa" Zarah ta faɗa da sauri. "Haka yace miki? Bashi da ko ƙawa bllnt budurwa, kawai zan haɗashi da Maryam, zan turo maka da pictures ɗinta, don't mind tana da kyau fa, very Obedient, gata yarinya just 16-17yrs, ballantana kace ta maka girma, kaga sai a haɗa da auren Fatima, ko baka so? "Ina so mana" Cewar Mustapha yana murmushi. "Kai I'm serious fa! "Nima haka in dai tana sona" cewar Mustapha yana kallon shi, Ita dai Zarah Shuru tayi tana jinsu! Sam bata kaunar wannan hirar! "Yawwa, ka cewa su Ummi kayi musu Daughter in law, bari na nuna maka pictures ɗinta ma yanzu, amma fa she's a little bit naughty! Kasan yaran zamani" Ya ƙarashe maganar yana kunna wayarsa, kallonsa Zarah tayi a hankali ta girgiza masa kai, bai ce mata komai sai murmushi da yayi mata. "Gata nan, and bafa talla nake maka ba? Taimaka maka zanyi" Ammar ya kuma faɗa yana mika masa wayar. Shidai Mustapha murmushi kawai yake yi, karɓar wayar yayi ya kalli hoton Maryam, lokacin saukarta ne tana sanye da hijabi har kasa ga allon sauka a hannunta wuyanta rataye da tag... "Har ta fika kyau" Cewar Mustapha yana miƙa masa wayarsa. "Eh saboda ita macece ba, za'a shafa wancan a goga wancan, yanzu dai if you are serious idan ka samu time kazo gidanmu kaji ko? "Amma ai sai ka bari kaji ta wajen Maryam din, kamar ma fa tana da saurayi kawai sai ka hanata wanda take so? Cewar Zarah tana kallonsa. " Maryam bata da saurayi da tana dashi da Mamina ta faɗa min, kuma nasan zata soshi insha Allah" Shuru tayi dan in dai da ranta bazata bari Mustapha ya auri Maryam ba sai dai idan dama haka Allah yayi shi mijinta ne babu yanda ta iya. Sun daɗe sosai a gidan Mustapha sai da sukayi sallar magariba sannan suka fara niyyar tahowa.. sai a lokacin Ammar ya ce, "Gobe fa by 7pm zamu tafi" "Kana nufin 9ja? Mustapha ya faɗa. "Eh, Zarah ce take so saboda school" Ɗan kallon Zarah yayi wadda ta ɗauke kanta tana kallon gefe daban. "Toh safe journey, Allah ya kaiku lafiya" da Amin ya amsa yana jan hannun Zarah suka tafi. Bayan sun isa gida ita ta fara yin wanka ta ɗauro alwala saboda sallar Isha'i sannan ta kwanta a kan gado, wayar Ammar dake charji ta zare tare da kunnawa, password ne a jiki, sunan Raihan ta saka amma bai buɗe ba, ta saka sunan Mami, bata taba tunanin cewa sunanta ya saka ba kawai ta gwada ne ai kuwa sai gashi ya bude, murmushi ne yayi escaping lips ɗinta sannan ta cigaba da abinda ya kaita daukar wayar.. Layin Mustapha ta shiga kira tana tashi tayi hanyar waje.. a hankali ta kulle kofar bayan ta fita, har ta tsinke bai dauka ba, sake dannawa tayi, bugu biyu ya ɗauka.. "Yaya ni ce, naga kamar Ammar ya ɗau maganar ka da Maryam so serious, nidai bana son wannan haɗin wallahi, kayi ta addu'a Allah ya baka mace ta gari" "Ohk shikanan, amma akwai wata matsala ne? Cewar Mustapha daga ɗayen side din. "Kawai bana so! Yarinyar bata da kunya, shi yake ganinta saliha, kai dai karka yarda" "Shikenan, good nite" Daga haka ya katse wayar. Tana shigowa Ammar ya fito daga toilet, kallonta tsaya yi from head to toe, rigarsa ce a jikinta duk da bata kamata amma iyakarta gwiwa. "Daga ina kike? Ya faɗa yana haɗe rai. " Dama knocking akayi sai na leka" "Waye zai mana knocking? Babu me yin knocking saboda bamu bukaci komai ba! Baki san ba'a gida kike ba? Meyesa zaki fita a haka? "Ba kowa fa! Ta faɗa tana karasa shigowa cikin dakin. "Kar na sake gani" Bata ce kala ba ta koma kan gado ta fara danne² a wayarsa... Ringing ta fara yi, Mamina shine sunan daya bayyana, miƙa masa tayi tana fad'in "Mami ce" Karɓa yayi yana katse kiran sannan ya kirata, a handsfree ya saka yana ajiye wayar ya cigaba da shiryawa. Bayan sun gaisa Mami ta ɗora da faɗin " Ya jikin Hydar ɗin? "Da sauƙi Mami" "Toh Allah ya ƙara sauƙi, kana kusa da Zarah ne? Sai daya kalli Zarah a hankali ta girgiza masa kai.. "No tana toilet" Ammar ya bata amsa. "Ok kace ina mata yame jiki, ince dai kuna waya da Bilkisu? Dan bana son tashin hankalin Sadiya, jiya haka tazo gidan nan tana tayi, yanzu haka ta mai da Bilki gidanta, wai kasan tana da juna biyu ka share kayi tafiyarka? Kaga Ammaru bana so kana zalintar yarinyar nan! Tun da kuka tafi bata da lafiya, kasan yadda take idan tana da ciki, ga ciki danye kullum kasala, dalilin daya kawo sadiya kenan tana surfa min bala'i, kuma tace baka kiranta hakane? "Mami ban samu damar kiran nata bane, kuma ni Bansan da zancen cikin ba, ke kanki kinga ba wani yawan waya muke yi ba" "Shikenan ni dai ina ƙara faɗa maka, kayi kokarin adalci, kuma kayi kiranta" Da toh ya amsa yana mata sallama. Zarah kuwa tunda a kayi zancen cikin Bilkisu taji duk wani yanayin farinciki da take ciki ya tafi.. da ƙyar ta iya tashi tayi sallah ko jiran Ammar batayi ba, kwanciya tayi tana kudunduna tare da lumshe idanunta. Bayan Ammar ya gama abinda yakeyi ya dawo gefanta ya kwanta yana fad'in " Duk baccin ne ya saka yau ba'a jirani ba? Banza tayi masa tana pretending as bacci take yi, idan lissafin ta dai-dai ne sun kusa wata daya da aure, kuma ciki har na kwana bakwai ana ganewa bllnt tace karya Bilkisu take yi, kwanta uku ba gidan suka fara fuskantar wannan matsalar da Ammar! Zai yu ace hasashenta gaskiya ne? Dagaske Ammar ne baya son bata hakkinta? Toh kodai dagaske bai da lafiya, inda baida lafiya ta yaya Bilkisu zata samu ciki? Ko dai a iya kanta rashin lafiyar ke tashi? This is impossible kawai Ammar yana son raina mana hankali ne! Dama duk soyayyar da yake cewa yana mata ƙarya yake? Hawaye taji sun zubo mata masu zafi. Daga nan kuma ta barke da kuka mara sauti, sosai take jin zafi da raɗaɗin a zuciyarta. Tabbas namiji buhun ƙaya! So innocent human being like Ammar amma yake betraying ɗinta? "Zarah! Ammar ya kira sunanta jin kamar sautin kuka. Shuru tayi tana rufe Idanunta. Wutar dakin ya kunna yana ƙoƙarin juyo da ita amma taki barin hakan ta faru. "Ok sorry, kin sabar min da kwanciya a jikin junanmu shine yau zakiyi min tawaye? Banza ta masa tana jin wani baƙin ciki. Bai ƙara cewa komai ya kwanta ya kyaleta dan baya so suyi faɗa a daren nan da alama kuma ranta a ɓace yake dan shi kanshi bai so a kayi zancen cikin Bilkisu a gabanta ba. Ni kuwa nace uban waye yace ka saka waya a handsfree. Har karfe biyun dare Zarah bata iya bacci ba, tashi tayi daga kan gadon ta nufi toilet, sai da tasha kuka sosai sannan ta fito bayan ta wanko fuskarta, a zaune taga Ammar ya kunna lamp. Ɗauke kanta tayi ta koma kan kujera tana daukar remote.. "kallo da daddaren nan Zarah? Banza tayi masa zuciyarta na zafi. Kunna TV tayi ta kai MBC 2, kwanciya tayi ta ƙurawa TVn idanu amma a zahirin gaskiya ba kallon takeyi ba. Kashe TVn Ammar yayi yana kallon ta ya ce, "Me nayi miki? "Ni nace kayi min wani abu ne? Ta faɗa tana kokarin sai ta kanta. "Kinyi kuka! Meyasaki kuka? Bata amsa masa ba ta koma kan gado tana kashe lamp din daya kunna. Sake kunnawa yayi yana kallon Idanunta da sukayi ja sosai sannan suka rage girma. "Zarah! Dan Allah me yake damunki? Kukan me kikayi? Faɗa min" Ya fada Asif bai da clue a kan komai. Ƙoƙarin hugging din ta yake ta matsa tare da daga masa hannu wasu hawayen na zubo mata. "Kiyi hakuri! "Dama haƙuri zaka bani saboda kasan kana shiga hakkina! "Ban taba shiga haƙinƙki da sani na ba Zarah! Ina kokarin sauke duk wani haƙƙi naki daya rataya a wuyana, duk abinda na gazayi wallahi Zarah bada gayya naki yi ba! Meyasa zan cutar dake? Meyasa? Bani amsa" "Nima bansani ba" Ta faɗa tana ƙoƙarin tsayar da hawayenta amma sunƙi tsayuwa. "Toh ki yarda dani, wallahi Zarah bazan taɓa cutar dake ba, domin idan na cutar dake kamar kaina na cutar, meyasa zaki dinga irin wannan tunanin? Goge hawayenta tayi tana kwanciya ta kyaleshi, dan ba jin akwai kalaman da Ammar zaiyi amfani dasu a yanzu ta yarda dashi.. "Zarah dan Allah ki yi hakuri" Bata ce masa komai ba sai sabon kuka data fashe dashi. Kalmar innalillahi wa inna ilaihi rajiun ya furta yana kallonta, shi ya xaiyi? Da wani bakin zai faɗa mata a wajenta kaɗai yake fuskantar wannan matsalar? Ammar be koma bacci ba sai sallah da ya dinga yi har Asuba, ita kanta Zarah batayi wani bacci ba. Washe gari da safe yaso su fita taga gari amma bai ga fuskar yi mata wannan zancen ba, tunda ta tashi ko ruwa bata saka a bakinta, tana kwance sai zancen zuci takeyi. Bayan Ammar ya haɗa musu kayansu ya kalleta ya ce, "Ki tashi kici abinci" "Cin abincina ko rashinsa bai dameka ba Ammar! Daga haka ta tashi ta fita ta bashi waje. Chan wajen hotel din ta je ta zauna tana kallon jama'a.. "Hello! Taji an faɗa ana zama a gefanta kasancewar couch din da girma. Bature ne ɗan matashi dashi, da hi ta amsa ta cigaba da kalle², "Its being a long time that i saw such a natural look, where are you from? Cewar baturan yana kallon Zarah. Tashi tayi tana fad'in " Nigeria! Daga haka ta barshi a wajen. Beyi ƙasa a gwiwa ba ya biyota yana fad'in "Excuse me ma'am" Bata tsaya ba ta cigaba da tafiya abunta. Lifter ta shiga, da sauri ya shigo yana sauke ajiyar zuciya ya ce, "I'm not asking for much, just for friendship, I'm Eyersh by name" Ya faɗa yana miƙa mata hannu alamar su gaisa. "I'm sorry i can't accept your request" Daga haka ta koma chan gaban lifter ta tsaya, matsowa yayi inda take yana kallon bayanta, juyowa tayi dan sam hankalinta bai kwanta ba. Gani shi daf da ita ya saka ta zara ido tana haɗe rai ta ce "Kai dallah me haka? Ƙoƙarin riƙeta yake yi lifter ta buɗe, tana kokarin fita ya damkota, lifter ce ta rufe, kokarin kwatar kanta take yi amma yaƙi barin faruwar hakan, kuka ta fara yi tana ƙoƙarin yin ihu amma ya toshe mata baki, duka take kai masa ta ko ina, calmly ya ce " Just be mute beb! Riƙeta yayi sosai yana shaƙar ƙhamshi turaren jikinta, suma ne kawai Zarah batayi ba, gashi duk wani ƙarfinta ya kare, sakar mata baki yayi ganin nunfashinta na son ɗaukewa, looking at her cute lips ya fara kokarin hade bakinta da nashi, bai ankara ba tayi kakin majina ta tofa masa, da sauri ya saketa yana goge bakinsa, lifter ta dinga dannawa, luckily ta bude, floor din da suka iso ba wanda take bane, gudu ta saka ganin mutumin ya biyota, kuka take sosai dan iya tashin hankali ta shigeshi, wani ta gani ya fito daga lifter dattijo dashi, da sauri ta shiga lifter tana danna floor din dazai kaita, runtsa idanu tayi ganin mutumin ya iso, amma tsohon nan ya tsaya yi masa magana wanda hakan ya danyi distracting dinsa har lifter ta rufe. A wajen ta sulale tana fashewa da kuka, buɗewar lifter ce ta saka ta sauri miƙewa ta fito, Ammar da wani Bature ta gani suna magana da key a hannun Ammar din sannan ga luggage ɗinsu, da sauri ta nufeshi tana rungumeshi jikinta duk rawa yakeyi... "What's wrong? Cewar baturan yana kallonsu. "Nothing sir Thanks" Ammar ya bashi amsa, da ok mutumin ya amsa sannan ya kira daya daga cikin ma'aikatan dake aiki a floor din su ɗauki kayan Ammar... "Zarah lafiya? Kasa magana tayi tana jin jikinta na rawa sosai. "Calm down" Cewar Ammar yana shafa bayanta. Ajiyar zuciya ta ke saukewa nunfashinta kamar zai ɗauke dan ta kusa samun Asphyxia lol... Ni kuwa nace maganinki. Da ƙyar ta iya sakinsa suka shiga lifter zuwa 1st floor. Cab suka tsara ya kaisu shopping mall, ba wani siyayya yayo ba, Zarah kam bata iya cewa komai ba... Tabbas sexual harassment ba karamin abu bane, Allah dai ya kiyaye ya kuma tsaremu a duk inda muke Ameen. Duk abinda ya daukarwa Zarah sai daya daukarwa Bilki, ita dai da idanu kawai take binsa har suka fito daga mall din, wajen shan ice cream ya kaisu amma sam Zarah bata wani enjoying komai, da kyar ta yarda yake musu pictures and she looks so sad.. jirginsu saura awa daya ya tashi suka tafi asibiti wajen Hydar a chan sukayi spending din lokaci saura 20mins suka nufi airport.. ita dai Zarah gata nan ne abun duniya duk ya tarar mata. Bayan jirgi ya tashi ta lumshe Idanunta tana mutumin ɗazu kawai take gani, da sauri ta buɗe tana sauke numfashi.. "Wai meyafaru? Cewar Ammar yana haɗe hannayensu. "Duk ba kai ka jawo ba? Ni ka sake min hannu" ta faɗa tana kokarin kwace hannunta Idanunta na kawo ruwa. "Shiiii, a jirgi fa muke Zarah! Bata ce komai ba ya shiga goge hawayenta da ɗayen hannun. "Kiyi haƙuri, nasan dama kina dashi" haka nan sukayi journey din har zuwa 9ja. Bayan sunyi landing an fito da luggage ɗin su suka fito daga cikin airport ɗin, napep ya tsarar musu zuwa gidansa. Suna isa Zarah ta wuce bedroom ɗinta, duk yayi ƙura, kamar ta ɗora hannu a kai haka taji, kayansu Ammar ya ajiye yana kallonta yace " Ya za'ayi kenan? Banza ta masa dan har yanzu haushinsa take ji. Hugging dinta yayi yana dora habarsa a kan kafaɗarta ya ce, "Bana so ina miki magana kina yin shuru kinji ko? Nan ma bata ce dashi komai ba. "ok kina so nima na nuna miki kalar nawa fushin? "Eh" Ta bashi amsa. Sake riƙeta yayi yana murmushi ya ce, "Bazan taɓa ba insha Allah, yanzu dai bari na tayaki gyara dakinki nima sai muje ki tayani gyara nawa" Da ok ta amsa sannan ya sakeya. Sun daɗe sosai suna gyara dakin har curtains sai data cire ta saka sababbi, ko ina ya dawo tas, toilet ta shiga tana hada ruwan wanka, Ammar kuma na saka turaren wuta a burner. Sanye da bathrobe ta fito tana kwanciya a kan gado... "Ya kikayi wanka? Ɗakina fa? "Gaskiya bazan iya ba" Ta bashi amsa tana rufe Idanunta. "Amma ai ba haka mukayi ba ko? "Na gaji toh " Ta faɗa tana kallonsa. Kai ya gyaɗa alamar shikenan. Shima wankan yayi, kafin ya fito har bacci ya ɗauketa. Ɗakinsa ya tafi ya ɗauko kaya, sannan ya koma ɗakin Zarah ya kwanta. Cikin bacci taji ana taɓata, a mugun firgice ta farka, ganin Ammar ya sakata sauke ajiyar zuciya, sai kuma ta riƙe hannunsa tana ɗan bata rai ta ce, "Bacci zanyi" "Na sani, kuma ban hanaki ba, bai sake bata damar yin magana ba, fatan sa kawai komai ya tafi yadda yake so ba Zarah kaɗai ba harshi ma yana cutuwa. Kamar zatayi kuka ta kalleshi, kamar me raɗa ya ce, " Trust me" romancing ɗinta yake sosai, tun bata responding har ta fara tana mayar masa martani.. ni kam kayan rahota na na kwaso na fenno a guje kar a makarantar min da idanu lol.