✨ *MATANA* ✨
*Mallakar*
AUTAR MAMA*FREE BOOK*
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*
*Comments*
*Vote &*
*Share fisabilillah**042*
Ranar Friday Zarah da wuri ta dawo daga school saboda tana exams, Fatima ta gani a falon gidan tana cin abinci, gaba ɗaya ta rame kamar ba ita ba, toh ko dai ciki ne? Taɓa baki tayi dan taga me ruwanta ma aciki idan cikin ne? Wucewa tayi bata ce da ita uffan ba, bata daɗe da shiga ɗaki ba Bilkisu ta shigo tana rarraba idanu kamar shege a rabon gado. "Dama cewa nayi bari na tambayeki me za'a dafawa baƙin Hubby da zasu zo? Cike da bala'i Zarah ta juyo tana kallonta ta ce, "Ina ce ke ya faɗawa zai yi baƙi? Me ruwana a ciki? Ko da chan idan zakiyi wa baƙinsa girki ni kike tambaya? Ko gulma ce ta kawoki yanzu? Dan Allah fitar min a ɗaki" "Zarah, nifa bana son wannan halin naki kuma! Nifa dagaske nake inaso mu yi zaman lafiya, mu zauna ba'a matsayin kishiyoyi ba, meyasa ki ka kasa yarda dani? "Dan Allah Bilki ki fitar min daga ɗaki! Ta faɗa tana nuna mata hanya. Ficewa Bilkisu tayi. Dogon tsaki Xarah taja tana fadin "Ni za'a lulluɓe? A shiga jikina a cuceni? Ni zaku rainawa hankali? Idan shi kun raina masa nashi hankalin wallahi ni baku isa ba, mutanen da tun farko suka nuna min tsana ƙiri², wani irin cuta ne baku min ba? Sanadiyyar ku na haɗu da paralysis har yanzu hannuna baya aikatuwa kamar da! An cuceni a banza sannan yanzu a kawo min maganar banza? Wallahi bazan ɗauka ba duk wanda ya min sai na rama ai shurun da nake ba tsoron uban kowa nake ba! Daga haka ta faɗa toilet ranta duk a ɓace.
By 3pm abokan Ammar suka zo na wajen aiki, tsaf Bilkisu ta gyara falon yayi kyau, shi kanshi Ammar was impressed. Ga abinci wanda tare sukayi da Fatima shima tsaf a kan dining gwanin birgewa. A kan kujera suka zauna sannan ya shiga ɗakin Zarah. Tana zaune tana kallo hankali kwance. "Kun sha aiki, sorry na baki wahala ga school ga kuma girki" Taɓa baki tayi tana kallon sa ta ce, "Sun sha aiki dai" "Su waye? Cewar Ammar cike da rashin fahimta. " Bilki da Fatima mana, ni girkina yana kitchen, baka sanar dani zakayi baƙi ba! Ko ka faɗa min? "Ban sanar dake ba amma ai na sanar a faɗa miki? Sanin kanki ne tun jiya bana gidan nan, wayar ki kuma a kashe na kira Bilkisu na faɗa mata ta sanar miki kuma nasan ta faɗa miki, meyasa kike son ɓata min rai ne kullum? Duk irin ƙoƙarin da nake na son ganin na faranta miki rai ke kullum son ganin nawa ɓacin ran kike Zarah? Zaman lafiyar ne bakya so ko me? "Eh bana so! Kowa yayi rayuwar shi! Kawai dan anga bana magana sai a nemi raina min hankali? Wallahi ba Bilki ba ko kai ne kayi min abu na daina haƙura kaji ma da kyau! Daga haka ta wuce ta barshi. "Toh me yake damun ta? Kafin dai Bilkisu ta dawo lafiya lau suke zaune, soyayya kuwa ba irin wadda baya gani toh meyasa zata canza? Anya kuwa Zarah bata da aljanu? Ganin ɓatawa kanshi lokaci yake ya sashi nufar bedroom ɗin yana fad'in "Ki saka hijabi ki fito ku gaisa" daga haka ya fita. "Ka shanye mu kamar kilishi" Cewar DR Sadeeq yana kallon sa. "Ai kunfi kilishi ma, ina zuwa" Ya faɗa yana wucewa ɗakin Bilkisu. A gaban dressing mirror ya ganta ga Fatima a kwance a kan gado. "Ke lafiya? Ya faɗa yana kallon Fatima. "Bata da lafiya ne fa, kuma gaskiya Hafiz baya kyautawa ace daga yin aure har ya fara mata masifa? "Laifi tayi ai, sai ta gujewa laifin sai ta daina shan masifa" Tashi zaune Fatima tayi tana kallonshi ta ce, "Yaya abu kaɗan da faɗa yake yi, kuma kasan bani kaɗai bace ba komai nake iya ci ba toh sai yayi ta faɗa wai tsirfa ce ni wallahi na gaji" Ta ƙarashe maganar tana goge hawayenta. "I'm coming za muyi magana, Bilki ki fito ku gaisa, kuma kwalliyar ta isa haka and make sure kinyi whipping wannan jambakin" "Tohm " Ta amsa tana ciro Whipper ta fara goge jambakin lebanta. "Ki saka hijabi kar na ganki da mayafi nasan ba hankali kika cika ba" "Wai da lafaya zan saka" Ta faɗa tana kallonsa. "No ki saka atamfa ko dai wani abun sannan ki dora hijabi" Da toh ta amsa sannan ya fita. Dubanta ta mayar kan Fatima ta ce, "Ki daina kuka kuma ni bansan ta yadda za'a masa bayanin Hafiz cewa yayi ki dawo gida ba idan kin haihu kya koma" "Bilkisu nima ban sani ba wallahi, ban san ta yadda zasu ɗauki maganar nan ba, wallahi Hafiz ya bani mamaki! Ban taɓa tunanin zai min haka ba" "Kiyi haƙuri zamu san matakin da zamu ɗauka wallahi zai gane kuranshi! "Gaskiya, dan bana so na rasashi" Fatima ta faɗa tana wasu hawayen. "Bazaki rasa shi ba, yadda muka fara kama Yaya a hannu kema haka zaki kama shi wallahi, ai ni da Umma muna da babban shiri wallahi, kuma in dai kina so ki riƙe shi a hannu zanyi wa Umma magana, itama ta ce wata ƙawarta ce ta dorata a hanya, ai da tun farko ma tasan wannan hanyar da bazata bari Abba ya auri waccan mayyar ba, ke dai bari na shirya naje mu gaisa na dawo muyi magana" Gyaɗa kai tayi alamar toh. Riga da wando ta saka sannan ta zumbula hijabi har ƙasa, fitowa tayi, a falo ta gansu Ammar yayi serving ɗinsu suna cin abinci sai hira suke, ƙarasawa tayi suka gaisa sai yaba girki suke yi, godiya tayi musu tana ƙoƙarin tashi DR Sadeeq ya ce, "Ina Zarah? Murmushi tayi tana fad'in " Tana ɗaki ta ɗan kwanta ne bata jin daɗi, ai da tuni ta fito kun... Kafin ta ƙarasa sai ga Xarah ta fito tasha hijabi har ƙasa, gaisawa sukayi sannan tayi excusing ɗin kanta ta fita, da idanu kawai Ammar ya bita yana mamakin ina zata data kasa haƙuri har baƙin su tafi" ɗaki Bilkisu ta koma tana cire hijabin jikinta ta zauna kusa da Fatima ta ce, "Kinga ki dena tunani kar wani mugun abun ya sameki, bari na kira Umma in sha Allah bazaki wahala ba da rai da lafiyar ummata, dan nasan Mami babu abinda zata ce sai dai tace kiyi haƙuri, duk tabi tayi sanyi tunda Ammar ya auri waccan jakar Zaran" Fatima dai bata ce komai ba saboda ita kaɗai tasan me take going through! Zarah kuwa tana fita wajen da ta ga wannan haƙon Bilkisun ta nufa, icce ta karyo ta fara tonawa amma bata ga komai ba, ƙaramin tsaki tayi tana fad'in "Na tabbatar ba shuka bace a wajen nan wallahi, amma dai shikenan" mayar da ƙasar tayi tana barin wajen, bata koma falo ba ta zauna a kan lilon dake garden ɗin gidan dan bata so ta kuma wuce abokon Ammar dake zaune a falo. Ta ɗau tsahon lokaci a garden ɗin tana zaune tunani kala² na zuwar mata zuciya. "Zarah! Taji Ammar ya kira ta. Bata juyo ba hakan nan bata amsa masa ba. Numfashi ya sauke a hankali kafin ya ce, "Rabi'u yace min nan kika shigo, meyasa kike behaving haka ne? Ni fa ban san ki da wannan ɗabi'un ba, Zarar dana auro na kawota cikin gidana ba haka ta ke ba" "Gidan naka ne ya canza ni Ammar, haka kawai saboda anzo an nuna maka komai ya wuce sai ka hau ka zauna? A kan me? Da ina da saurin yarda da mutum amma zaman gidanka ya ko ya min hankali" "Kina so kice canzawar da suka yi ba har zuciyoyinsu ba? Kai ta girgiza tana cewa "Point of correction, ba ina so in ce ba dan gaskiyar lamarin ne naga kamar ka faɗa trap ɗinsu kuma there are up to something, kawai suna so a yarda dasu ne dan idan sunyi abu ba'a zargesu ba ko dai wani abun, bansan actual plan ɗin su ba amma dai wanann ba aynahin kalar su bace" Ajiyar zuciya Ammar ya sauke yana kallon ta da kyau ya ce, "Are You sure? Kai ta gyaɗa alamar toh. Murmushi yayi yana kamo hannunta ya ce, "Da kin zaunar dani tun farko kinyi min wannan bayanin, in har kuwa hasashenki gaskiyaa ne zamu bisu yadda suke so, su suka saka wasan mu ma kuma zamuyi namu plan ɗin a ciki, zamu bisu yadda suke so kuma su zasuyi loosing wasan da yardar Allah, just keep your trust in Almighty" Gyaɗa kai tayi tana tashi daga kan lilon. "Problem solved? Kai ta gyada a hakan. Janyota yayi jikinsa yana murmushi ya ce, That's my girl, Allah yayi miki albarka" "Amin" ta amsa tana barin jikin shi. Kuɗi ya ciro a aljihun shi yana saka mata a hannunta ya ce, " In ji su Sadeeq" kallon kuɗin tayi sannan ta kalleshi ta ce, " Ai Bilkisu zaka bawa domin ita ce tayi duk aikin" "Itama an bata nata, just take it" Karɓa tayi tana fad'in "Na gode" "Yawwa" ya amsa yana riƙe hannunta suka dawo falo. Fatima kawai ya gani ta fito daga kitchen, kallonta yayi da kyau yana fad'in " Ke!" Ɗago da idanunta tayi ta kalle shi. "Lafiyar ki kuwa? Kasa riƙe hawayenta tayi ta fashe da kuka tana. Kallon juna Zarah da mar su kayi kafin Ammar ɗin ya ce, "Kuka nace kiyi min? Bilkisu ce ta fito daga kitchen ɗin hannunta riƙe da Plate din abinci tana kallon Ammar ta ce, "Ba wani abun bane fa, wai cikin ne yake bata wahala kuma bazata koma gidanta ba saboda bata so mijinta yana takura mata shine fa tun ɗazu nake faɗa mata hakuri ake yi" "Ok, ke shirya na mayar dake yanzu, ko wace mace ai haka take haƙuri, ɗauko hijabinki" "Ka barta tayi kwana ko biyu ne kafin nan ta warware ko? Cewar Zarah tana kallon shi, dan daga yanayin maganar Bilkisu ta gane ƙarya take akwai wani abun da suke ɓoyewa tana dai fatan ba matsala ta fara samu a gidan mijinta ba" "Daga yin aure kuma? Meyesa bazata tafi gida ba? So kike Mami ta ɗora min laifi? Cewar Ammar yana kallon Zarah. Kai ta girgiza tana fad'in "Tun da kaga tazo nan bata je wajen mahaifiyarta ba kasan tana da dalili, ka bata lokaci mana" "Shikanan" Daga haka yaja hannun Zarah suka wuce ciki. "Muje ɗaki, mun godewa Allah ta gaban goshi ta saka baki nasan da bazai yarda ba" ita dai Fatima bata ce komai ta nufi bedroom jikinta duk ba ƙwari, gani take idan aka san halin da take ciki dariya za'ayi mata. "Yanzu bilkisu idan Yaya yaga ban tafi ba fa? "Ba laifi ki bane ai, shi Hafiz ɗinne ya ce ki dawo gida kawai karya zakiyi kice ya bugo miki yayi tafiya shi ne ke kuma bakya jin dadi ga ciki sai kika ce zaki zauna dani shikenan fa" "Amma kuma ta yaya hakan zata faru? Bilkisu na murmushi ta ce " Gobe zaki kira Mami ki faɗa mata ni kuma zan sanar da Ammar in ce kiranki yayi yace is urgent zai wuce UK zai ɗan kwana biyu ko beyi ba? Kasancewar bata da wani option ya saka ta faɗin "Ya yi" "Yawwa, kiyi haƙuri kiyi ƙoƙarin cire komai kar a mana dariya kinsan muna da magauta dayawa" Gyaɗa kai kawai Fatima tayi tana jin zuciyarta na zafi sosai.