Chapter twenty two

495 38 10
                                    

✨ *MATANA* ✨

*Mallakar*
      AUTAR MAMA

*FREE BOOK*

*EXQUISITE WRITER'S FORUM*

*Comment*
*Vote* &
*Share* Fisabilillah

*My WhatsApp group link, Dan Allah mata kawai*
https://chat.whatsapp.com/BrUNywiBsPxDJjxclwHfdU

'''Assalamualaikum jama a ina sanar daku cewa wanna shaharariyar Mai makeup dinna Wanda akaf maiduguri babu kamarta wato AMMIS GLAM tana sanar daku cewa akwai ingantatun man gyara gashi ga Mai bukata zai iya tutubar number ta kamar haka..... 08030687711 muna bada sari a kowani state kike za a iya aika Miki kedai Yar uwa kiyi Kokarin mallakar naki kamin ya kare 500 ne kachal Amma idan sari zakiyi akwai discount sanna wanna man gyaran gashin Yana Kara tsowon gashi da laushi sanna Yana hana karyewar gashi sanna Yana sa gashinki yayi baki sosai sanna Yana maganin amotsrin gashi Yar uwa karki Bari a baki  labarin don wanna man Basu da wani illa domin an hada sune da ingantataun kuma nagartatun mayuka masu aminci da karfi da basu da wata illa sai ma taimakawa da yakeyi karde ku Bari abaku labarin  wanna Mai gashi na AMMIS HAIR OIL/CREAM'''

'''sanna pls don Allah idan kinsan ba siya ko sari zakiyi ba pls karkimin magana ko kikirani'''

*022*

        Raglan collar da handkerchief skirt ne a jikinta, tayi matuƙar kyau dan sosai kayan suka amsheta, kuma kalar kayan ta dace da kalar fatarta.. tun daga sama har ƙasa yake kallonta, tunda yake da ita bai taɓa ganinta cikin irin wannan shigar ba, kullum  abaya take sawa. Lumshe idanunsa yayi kaɗan sannan ya  sake buɗesu akanta, "Kinyi kyau!" Ya faɗa very soft. Murmushi tayi me kyau tana gyara veil ɗinta ta ce, " Nagode, mu tafi nasan su Daddy sunata jiranka" ɗan buɗa idanunsa yayi kaɗan alamar mamaki.. "What? Ta faɗa tana kallonsa. "Har da Daddy? Na dauka iya step Mom dinki kawai zan gani?" Dariya tayi me sauti tana ɗan juya idanunta ta ce, " No harda daddy na, muje ko? Shafa kansa yayi kaɗan yana tashi daga zaunen da yake.. ita ta fara fita sannan shi. Driver dinta ne ya ɗauke su har zuwa gidansu Aysha dake nan UK din. Bayan sun sakko ta kalleshi ta ce " Just act like my BF buddy! Tun a gidanka naso muyi maganar but I'm nervous, Bansan yadda zaka ɗauki maganar ba! Daddy nane ya matsa min akan aure har ana son haɗa ni da ɗan uwan step Mom dina, kuma ni I'm not interested please Buddy ka min wannan alfarmar" "Ok Aysha Amma kinsan ramin karya kurarre ne ko? "Na sani amma bawai dadewa zamuyi akan fake relationship din ba, nan gaba kaɗan zansan me zancewa Daddy na" a hankali ya ce " Shikenan! Cikin jin daɗi ta ce " Nagode! Kai kawai ya gyada mata.. ita ta fara yin gaba sannan ya biyota. A zaune suka tarar da Stepmom dinta tana kallo.. "Mom, Aysha ta kirata a hankali. "Har Kunzo? Cewar Stepmom din Aysha tana faɗaɗa murmushinta.. izinin shigowa akayiwa Mustapha, kansa a ƙasa ya ƙaraso ya zauna sannan suka gaisa, tashi Stepmom dinta tayi ta basu waje.. "Ka wani sunkuyar da kai,  dama haka kake da kunya? Ɗagowa yayi ya kalleta fuska ba yabo babu fallasa ya ce " Are You sure of this Aysha? "Yeah, Dan Allah karka bani kunya hun? "Ok" Ya amsa yana sauke ajiyar zuciya. Serving dinsa tayi abincin da aka shirya dominsa, ƙin cin komai yayi duk yadda Aysha taso yaci.. suna ɗan hira Daddynta ya fito fuskarsa cike da annuri.. zama yayi a kujera yana kallon Mustapha. Cikin mutunci suka gaisa da Mustapha.. ɗaki Aysha ta wuce tana fatan kar mahaifinta yayi wa Mustapha tambayar da zai kasa amsawa... "Masha Allah, Mustapha... Ka san mu hausawa ne kuma har yanzu al'adarmu nanan! Cewar Daddy cikin raha.. "yawwa, Aysha tace kana zaune a nan, wace sana'a kake yi anan ɗin? "Ina aiki da Company ne, suna manufacturing kayan sawa da sarkoki" kai Daddy ya jinjina kafin ya dora da faɗin " A Nigeria a wace unguwa kake? "ABUJA! Mustapha ya amsa cikin ladabi. "Toh Masha Allah, ashe unguwar mu ɗaya, me sunan mahaifinka? "Alhaji Abubakar Imam! Mustapha ya kuma bashi amsa. "Toh toh Masha Allah, kasan dai Aysha ta taɓa aure ko? Sannan tana da yaro" "Eh na sani Abba" Mustapha ya faɗa kansa a ƙasa. "Yawwa, insha Allah xansa ayi min bincike akanka, kaima zaka iya fara bincike akanmu, nasan Aysha zata faɗa maka inda muke a Abuja, kuma insha Allah idan babu wata matsala abune da za'ayi shi cikin ƙanƙanin lokaci, Allah ya baka ikon yi adalci a tsakanin su" Shuru Mustapha yayi yana ɗan runtsa idanunsa tunowa da Zarah.. "ai Aysha ta sanar damu kana da iyali, muna fatan zaka kwatanta adalci" "Inshallah! Ya amsa zuciyarsa na zafi. Tashi Daddy yayi ya wuce cikin daki.. be dade ba da shiga ba Aysha ta fito idanunta akan Mustapha.. "Tashi muje" Ta fada tana ficewa. Tashi yayi yabi bayanta, a jikin mota ya tsaya yana kallonta ya ce, " Kinsani nayi abinda bantaba yi ba Aysha, I'm feeling uncomfortable" "Kayi hakuri, amma ai u'r my friend more than this ma zaka iya ko? Shafa kansa yayi yana furzar da iska ya ce, " So yanzu kina ganin zaki nemo way out? Kar tazo ta ɓaci! "Insha Allah babu abinda zai faru, kayi hakuri, nasan kana son matarka kuma Baxaka so taji wannan b, nima kuma banyi hakan da mugun nufi ba, sorry please" "Is okay Aysha! Ya fada yana kallonta. "Ok nagode, driver zai maida kai gida sai mun ƙara haɗuwa take care" Kai ya Gyada mata kawai sannan ya buɗe motar ya shiga.. yana isa gida ya shiga toilet, wanka yayi sannan ya fito yana zama a gefan gado tare da dafe kansa da tunanin abinda Aysha ta saka shi ya aikata.. wayarsa ce ta fara ruri.. iska ya furzar me ɗumi sannan ya dauko wayar yana karawa a kunne.. cikin sanyin murya ta ce, " Hello"  cire wayar yayi daga kunne yana duba sunan.. lumshe ido yayi kadan kafin ya ce, "Bari na kiraki" Daga haka yayi disconnecting din kiran sannan ya sake dialing din number ta. Sai data kusa tsinkewa sannan ta ɗauka very calmly ta ce, " Bansan me zancewa Ummi ba, nasan fushi take dani kuma zamu koma makaranta and za'a biya kudin fees, then Naje asibiti bana jin dadi kwana biyu an rubuta min drugs, kuɗin hannuna basu kai ba kuma Inna ta han... "Ya isa! Ya fada yana dan shafa kansa zuciyarsa na zafi.. Numfashi ta sauke a hankali tana kuma faɗin " Kayi hakuri idan na takura dayawa" "Responsibility dinane kula da ke har ki haihu sannan kuma in kula da abinda kika haifa, It's only the school fee's shine bai zama dolena ba Zarah! Me ya sameki kika je asibiti? Sai data dau kusa second 10 sannan ta ce, "Ciwan baya nake" "Are You stressing your self? Ya fada a nutse.. "Banda option, i have to do all my chores, yanzu ko kallona inna  bata yi, Bansan me nayi haka ba! Nifa kawai inaso in sauƙaƙa wa kainane, bana so ina saɓawa Ubangiji na, bana so sanadiyyar abinda nake yi na shiga wuta! Bana son cigaba da cutar da kai da kuma cutar da kaina, meyasa toh kowa zai kama fushi dani? Meyasa babu wanda zai fahimceni? Ban taba kukan rashin uwa ba sai a ƴan kwananinkin nan, nasan da ace yau ina da mahaifiya zata fahimci halin da nake ciki! Ita zuciya ba'a tilasta ta akan abu! Nayi iya kokarina akan naga na hakura na zauna a ɗakina amma Zuciyata taƙi aminta da hakan, banda tsinuwar Mala'iku da fushin Allah babu abinda nake jawowa kaina, amma meyas... "Ya isa Zarah! Kina da ciki duk yawan waɗannan tunanin basu da daɗi a wajenki! Ki dane kinji ko? Kar kisa wata cutar ta kamaki, kuma nasan Inna zata sakko, zan kirata insha Allah take care please, zan turo miki da kudi kiyi settling school fee's ɗinki kuma ki siyi drugs, Dan Allah ki Dena stressing kanki ki zama very careful Zarah please" "Insha Allah, Nagode" Ta amsa a sanyaye. "Ok good nite" bata ce komai ba ta katse wayar. Ajiye wayar yayi yana rike kansa.. yana son Zarah, be taɓa son wata ƴa mace ba sai a kanta! Be taba sanin menene soyayya ba sai akan Zarah, amma yana fatan hakanne yafi musu alkhairi. Haka ya ƙare darensa wajen kai kukansa ga mahallici... Yana avoiding kiranta ne saboda a duk lokacin da ya kirata shi kadan yasan ya zuciyarsa take masa, sau da dama yakanji kamar yace ya mayar da ita amma idan ya tuna irin abubuwan da suka faru sai ya hakura.. sai da yayi sallar asuba sannan ya samu ya ɗan kwanta kafin ya tafi office...

MATANA ✓Where stories live. Discover now