Chapter ten

553 36 32
                                    

✨ *MATANA*✨
 

*Mallakar*
       AUTAR MAMA

*FREE BOOK*

*EXQUISITE WRITERS FORUM*

*Wannan labarin ƙirƙirarre ne, banyi shi ɗan cin zarafin wani ko wata ba! Sannan idan yayi shige da labarinka/labarinki coincidence ne Yawwa*

*Comments share and vote dinku yana da matukar mahimmanci idan yayi karanci zan maida abuna ba kudi💃*

*010*

           Cikin fada Mami ke magana kamar zata ari baki, kan Ammar a ƙasa ya ƙagu ta gama ya tashi ya tafi dan jirginsu karfe 2pm zai tashi gashi yanzu 1 harda 45. "Kana jina ko surutun banza nake yi Ammar? "Inajinki Mami" Ya fada yana ɗagowa. "Toh ka cire maganar auren yarinyar nan a zuciyarka! Kwata² watanka ɗaya fa da aure? Shine ɗan wulakanci zaka je ka samu Baffa da maganar kana son karin aure? Ammar! Wallahi ka fita a idona na faɗa maka! "Toh Mami" Ya fada cikin cool voice. "Tohm nidai na faɗa maka, tashi kaje gidan Khadijah zata baka saƙo ka kawo min" Shafa kansa yayi yana miƙewa tsaye ya ce, "Mami ki aika ko Maryam ce an kirani a wani hospital dake Abuja kuma by 2pm jirgin zai tashi" "Toh shikenan, Allah ya tsare" Da Amin ya amsa yana fita. Gidan Hajiya Babba ya wuce, Umar ne ya kaishi airport sai da jirginsu ya tashi sannan ya dauko hanyar dawowa gida. A wajen me siyar da fruit ya tsaya dan Hajiya ta bashi sautu.. "Zarah Please zaki rakani hostel sai ki dawo Kinga kayan zasu yi min yawa" "Shikenan toh" sansassayan muryarta ya doki dodon kunnensa. Da sauri ya kalli direction din,  bayan mace kawai ya gani sanye da uniform na nursing school sai wata black beauty lady dake facing dinsa tana zabar abaya. "Zarah! Yayi risking kiran sunanta. Aikuwa ta juyo tana kallonsa cike da tsantsar mamaki, lokaci daya kuma ta fara kallon surrounding din wajen dan tasan ba mamaki suna tare da Ammar. "Ni kadai ne" Ya faɗa yana sakin murmushi dan yasan manufar  kalle²n d take "Ina yini? Ta fada calmly. "Lafiya lau, ashe kina Kano? "Eh" Ta amsa a takaice. "Allah sarki, nursing school kike yi ashe, toh Allah ya taimaka" "Uhmm, Please karka cewa Ammar ka ganni" Ta ƙarashe maganar cikin sigar roko. Murmushi kawai yayi dan kam kamar Ammar din yaji ne. Shi ya biya musu kudin fruit din yace su jira yasauke su, Zara'u taso cewa ya barshi amma Zainab tuni ta shige front seat, siyan nashi fruit din yayi yana kallon Zara'u da Haryanzu bata shiga motar ba. Murmushi ta kirkira tana kallonsa ta ce, "Ka kaita makarantar ni zan wuce gida Nagode" "Kinsan is impossible ko? Just get in mu tafi" Babu yadda ta iya hakannan ta shiga suka bar wajen. Zarah ya fara saukewa sannan ya tafi da Zainab. Bayan ya dawo gida kuma ya tabbatar su Ammar sun sauka ya shiga kiran layinsa. Har ta tsinke be dauka ba, sake kira yayi, sai data kusa tsinkewa sannan ya dauka yana fad'in " Ya dai? "Guess what? Cewar Umar. " Ina jinka man! "Ok, naga Zarah, Ni nayi dropping dinta ma a gida" "Is this a joke? "No it's a gist! Umar ya fada yana dan murmushi. "Seriously, nasanka fa! Ammar ya fada daga dayen bangaren. "I'm serious fa, da ita da wata naji ta kirata da Zainab, ta fara ma school alamar ta daɗe a Kano" "Damn it! Wannan Saudan zanyi dealing da ita, jiya fa naje kuma tace min bata nan, definitely nasan taxo Kano tunda Saudatu ta faɗa, kasan yanzu ma ina kofar gidansu? Dariya Umar yayi yana fad'in " Sai ka dawo dan wallahi Zarah na Kano" "Ok ganinan amma bana so Mami ko su Hajiya su san zan dawo yau" "Ok baka da damuwa" Daga haka sukayi sallama. Daf da magariba ya dawo Kano, Umar ne ya daukoshi a airport. Sai da yayi relaxing a kujera sannan ya ce, "Gidansu Zara'u zaka kaini" "Tab, babu inda zanje, yarinyar ta rokeni kar na faɗa maka na ganta, kuma idan kaje kasan yadda zaka fidda ni, yanzu zan koma gida sai ka tafi kai kaɗai" Da ok kawai ya amsa yana lumshe idanunsa. Sai daya shiga gidansu Umar yayi wanka yaci abincin Umar da Hajiya ta kawo lokacin yana toilet. Tsaf ya shirya cikin yadi me kyau. Kallonsa Umar yayi ya ce, "Ka taho min da takeaway dan nasan babu ragowar abinci yanzu Hajiya kai da kai take girki wallahi" "Tayi min dai dai! Takeaway kuma kawo kuɗi! Wani kallo Umar yayi masa ba tare da yace komai ba. Dariya Ammar yayi yana fitowa daga dakin, ba kowa a falon hakan ya bashi damar ficewa da sauri. Sai da yayi isha'i a masallacin unguwar su Zara'u sannan ya aika yaro ya kira masa Saudatu. Ba'a jima ba ta fito tana turo baki dan Inna ce ta korota. Tana ganinsa ta haɗe fuska zata koma ya cafkota yana kallonta da kyau ya ce, "Kinsa naje Abujah kuma ance min Zara'u bata chan that means tana gidan nan har yanzu ko? Kwace hannunta tayi tana kallon sa ta ce, "Eh tana nan kuma ba fitowa zatayi ba, haka kawai ka takura mata? Toh bari kaji Aunty Zarah Yaya Mustapha zata aura dan ance sati me zuwa mahaifinsu zai zo wajen baffanmu a tsaida magana, ba kayi aure ba? Toh itama gashi Allah ya bata wanda yafika? Idan gayu kake ji dashi Yaya Musty ya fika! Idan kyaune shima ya fika kawai fari zaka nuna masa, toh me farin ma? Duk wani fari ai mummuna ne! "Har dake? Ya fada yana sakin murmushi. Shuru Saudatu tayi tunawa da cewa itama fa fara ce, farin nata ma har ya fi na Ammar. Turo baki tayi tana kallon sa ta ce, " Eh ɗin, Aunty Zarah kuma bazata fito ba ahtoh" Daga haka tayi shigewarta. Ko hijabin jikinta bata cire ba sai ga Ammar a cikin gidan bakinsa dauke da sallama. Inna dake kunnawa Zara'u maganin sauro saboda tana karatu kar sauro ya cijeta tayi saurin yarda asahanar tana fad'in " Hasbinallahu wa ni'imalwakilu me haka ni Aminatu? Tsugunnawa yayi ya ce, "Ina yini Inna? Kankance idanu tayi dan sai yanzu ta ganeshi.. "Wato daga dawowarta zaka zo ka takura mata? Munafuki? Me kazo dashi yanzu kuma? Cutar da ita da kayi be isheka ba? So kake ace maka ta mutu? Toh wallahi ta Allah ba taka ba Ammaru! Zara'u dai tafi karfinka! Kana ji kana gani zata auri yaron arziki Mustapha! Da mutuncina da ƙimata uwarka da ƴanuwanta da kannenka suka zo har cikin gidan na suka zageni suka ci mutuncin marainiyar Allah! Wallahi hakkin marainiyar nan bazai barku ba daga kai har ahalinka, baka ji tsoron Allah ba kazo ka yaudare min ƴa, bakai duba da halin maraicinta na rashin uwa da Uba ba, wallahi Ammaru ka cucemu! Dubeta yadda ta dawo, kamar me cutar ƙanjamau! Zaka tashi ka fita ko sai na zabga maka maficinnan? Inna ta karashe maganar tana kallonsa. Ajiyar zuciya ya sauke yana kallon Inna ya ce, "Wallahi Inna Ban yaudari Zarah ba kuma ina kaunarta har karshen nunfashi na, inas.. kukan da Zara'u ta fashe dashi ne ya dakatar dashi daga abinda yayi niyyar faɗa.. da sauri ta tashi ta shige daki zuciyarta na wani irin suya" Nannauyan ajiyar zuciya ya sauke yana miƙewa tsaye ya ce, "Kiyi hakuri Zarah, Please ki daina yawan kukan nan, I'm here ki fito ki amayar da bakin cikin ki akaina karki bar komai cikin zuciyarki zai iya haifar miki da abu mara daɗi, Please Zarah make it easy for me! I love you! Yana jiyo yadda sautin kukanta ke karuwa. Shima sosai idanunsa sukayi jaa, gaba daya ya wani susuce. "Zarah! Ya kara kiran sunanta.. "Yau naga jaraba, Dan Allah ka tafi mana, kai da kanka ka ganewa idanunka yarinyar nan bata ra'ayinka yanzu ko? Inna ta fada tana kallonsa. Da kyar ya iya hadiye miyau din dake bakinsa yana sauke nannauyan ajiyar zuciya, bai iya furta komai ba ya juya ya fice. "iKon Allah Inna, anya kuwa ba auren sukayi masa dagaske ba ba son ta yake ba? Cewar Saudatu dan jikinta duk yayi sanyi. "Ke rabu da maza! Gansameme dashi za'ayi masa auren dole? Uban wanine zai zauna masa da matar ko kuma su zasu biya masa sadakin? Duk yaudarace irin ta ƴaƴa maza, kyaleshi zai gaji ya bari" Gyada kai kawai Saudatu tayi. Washe gari Zara'u da kumburaran ido ta tashi, gaba daya jikinta a mace yake, da kyar ta iya shiryawa, sallama tayi wa su inna ta fito. Turus tayi tana karewa motarsa kallo cike da mamaki.. yana ganinta ya fito daga cikin motar ya ce, "Zarah! Da sauri ta ɗauke idanunta zuciyarta na bugawa, kada yace mata anan ya kwana? "Zara'u dan Allah horan ya isa haka wai bakya tausayi nane? "Uhmm! Ta fada tana kokarin wucewa. Fizgota yayi yana mata riko me kyau ya ce, "Why are you doing this? Me kike son maidani? Mahaukaci? Dan Allah ki bani peace of mind! "I don't have all this Ammar, please free me bani da strength din duk wannan i need to go to school" Ta ƙarashe maganar a mugun sanyaye. "Ok but ki saurareni ko sau daya ne"  Hawaye ne suka fara sintiri a idanunta tana jin komai na dawowa sabo a zuciyarta. Mota ya shigar da ita sannan shima ya shiga, barin layin yayi yana fad'in "I'm sorry! Nasan bani da bakin magana, amma idan kin yarda this week su baffan zasu zo gidanku" Tsayar da hawayenta tayi tana kallonsa cike da mamakin furucinsa. Shima dan kallonta yayi sannan ya mayar da hankalinsa kan titi ya ce, "Ko bakya sona?  "Ina da wanda zan aura" Ta fada da kyar. Murmushi yayi kadan yana riko hannunta very tightly ya ce, "Zarah tawace insha Allah, Ni ne zan aureki, kece zabina zabin zuciyata" Kwace hannunta tayi wani takaici na turnuketa, ya gama zuwa ya lallaba Bilkisu da yar murya yanzu kuma yazo yana mata dadin baki. Bata san lokacin da tsaki yayi escaping lips ɗin ta ba. Kallonta yayi ganin she's lost In thought ya saka ya maida kansa kan tuki. Har cikin makarantarsu ya kaita. "Munzo" Ya fada yana kallonta. Numfashi ta sauke ta tadan kalleshi kadan ta ce " Nagode! "U'r welcome darling" taɓa baki tayi ta fita abinta. Shima fitowa yayi yana kiranta da sauri. Tsayawa tayi ba tare da ta juyo ba. Shi ya isa gabanta yana mika mata kudin dake hannunsa ya ce " For break! Kallon kuɗin tayi sannan ta kalleshi, kai ta girgiza sannan ta ce, "Ina dashi na gode" riko hannunta yayi ya saka mata kuɗin, yana kallonta ya ce " Allah ya bada Sa'a karfe nawa kuke tashi? "Oho! Ta fada tana barinsa a wajen. Murmushi yayi me kyau yana bin bayanta da kallo wani irin farin ciki na lullubeshi. Zara'u na shiga aji ta dinga bin kudin da kallo, karamin tsaki tayi gaba daya sai take jinta wasai yau dinnan.. "Sannu! Taji Muryar mace a kusa da ita ta faɗa. Kallonta tayi tana dan sakin murmushi ta ce, "Kema sannu! "Yawwa, wanda ya saukeki yayanki ne? Kallonta take babu ko kiftawa sai kuma ta ɗauke kanta ta ce, "Eh" Dariya tayi tana fito da littafinta ta ce, "Sunana Waheeda, Kuma nasan Ammar, Yayata tana dating din Yayansa i mean cousin brother dinsa, an kusa ma bikinsu dan saura two weeks" "Uhmm" Shine kawai abinda Zarah tace. "And nasan kanwarki, dama tun da kika zo makarantar nan naga kamar nasanki, nasan kanwarki sosai tare mukayi saukar Alkur'ani ita ta koma hadda ni kuma ban koma ba, sunanta Saudat Right? "Ok! Shine kadai abinda Zarah tace dan ta isheta da surutu. Murmushi Waheeda tayi tana sake faɗin " Zamu iya zama friends? "Ok! Zarah ta kuma faɗa tana tashi dan so take ta fita tayi karatu kafin su fara lectures. Itama Waheeda tashi tayi ta biyota. Haka nan Waheeda ta dinga shige mata a ranar har Zara'u ta fara sake mata kaɗan.. Karfe 4 aka tashi, tare da Waheeda suka fito, drivern Waheeda har yazo, "muje sai mu saukeki" Cewar Waheeda tana kallonta. "A'a Nagode, zan shiga hostel ne, yau bamu hadu da ƙanwata ba" "ok toh bye" Kai kawai ta gyada mata. Hostel ta nufa wajen Zainab, bata wani daɗe ba ta fito dan tana so ta koma gida tayi karatu. Tun da ta fito yake kallonta dan already yaga shigarta hostel ɗin, bata lura dashi ba dan hankalinta baya inda yake, da motar ya nufeta yana danna horn, jiyowa tayi ta kalli position din da taji horn, ganin motar Ammar ya saka ta juya ta cigaba da tafiya, murmushi yi kadan yana sauke glass ya ce " Zara'u Please ki shigo zan koma wajen aiki fa" banza ta masa duk da cewa ta jishi, fitowa yayi daga motar ya sha gabanta with puppy face ya ce " Dan Allah" Bata ce komai ba sai kallonsa data tsaya yi. Komawa mota yayi ya bude mata ɗayan side din, nufar motar tayi ta shiga sannan y rufe ya zaga ya shiga. "Y school ɗin? "Uhmm! Abinda ta fada kenan. Hannunta ya kamo yana fara murzawa a hankali, "ka sake min hannu" Ta fada a sanyaye. 'Meyasa? "Banaso! Ta sake fada tana kokarin kwace hannunta. Ƙin sakar mata yayi sai ma kai hannun da yayi saitin zuciyarsa, very calm ya ce, "Duk lub dub din da zuciyata zatayi toh tare da soyayyarki take bugawa Zarah, baxan iya Imagine rayuwata babu ke ba" Kwace hannunta tayi da karfi tana zabga masa wata harara. "Nasan kina sona haryanzu Please Zarah don't make it so difficult for me" "Nifa babu abinda zan kuma ce maka, kamar yadda Saudatu ta faɗa maka next week Daddy zaizo wajen baffanmu, ko da ace babu magana tsakanina da Yaya Mustapha ni bazan iya auranka ba" Numfashi ya sauke bai ce komai ba ya cigaba da driving. Babu wanda ya kara magana a cikinsu har ya iso kofar gidansu. "Zanzo anjima Please, kmr bayan isha'i" Bata ce dashi komai ba ta bude kofar ta sauka, da kallo ya bita har ta shige cikin gida. Kallon kayan dake tsakar gida kawai takeyi cike da mamaki, "Waye ya kawo food stuffs dayawaa haka? "Inna! Ta fara kiran sunan inna da karfi. "Shigo Zara'u gamu nan a ɗaka" cewar Inna. Dakin inna ta shiga, ganin inna tayi a baje a tsakar daki ga uban suturu da cosmetics Saudatu kuma a gefan gado tana kumbura fuska. "Wannan kayan fa inna? "Wannan mutumin ne ya kawo wallahi, Nima ban dade da dawowa daga kasuwa ba kinsan nace zanje na sari kuka ta wajena ta kusa karewa kar azo nema babu, toh ina dawowa naga kaya ashe shine yazo ya kawo, amma dan wulakanci Saude bata fita ba" "Wai Inna in fita in masa me? Nifa gaskiya bazan iya auransa ba wallahi, yayi min tsufa Allah! Inna bata kulata ba ta kalli Zarah ta ce, "Ki ci abinci ki huta sai ku shirya kayan abincin a dakin kusa da soro, wannan kayan kuma ki hadesu waje guda, ni bari naje na daura itace kar azo nema ban daura ba" "Amma Inna ya za'ayi a karbi kayan bawan Allah haka? Kinaji fa itama saudan tace bata sonsa" cewar Zarah. "Ku kuka sani! Daga haka Inna ta barsu a wajen. Kusa da Saudatu ta zauna tana kallonta ta ce, "Idan ya sake zuwa ki fita ki fada masa yayi hakuri kina da wanda kike so, sannan kayan nan daya kawo zamu mayar masa da abinsa duk lokacin daya zo, wai a ina kuka hadu dashi? "Na dawo fa daga islamiyya inna ta bani sautu in siyo mata danyar kubewa a hanya toh zan tsallaka titi ya kusa bigeni, ashe mayen mutum biyoni yayi yaga gidanmu, yo maye mana Aunty, sau daya fa ya ganni shikenan kuma sai ya fara sona? "Kar na kara ji kince masa maye, ko ba komai ai ya haifeki, idan yaxo ki faɗa masa abinda nace miki" Kai ta gyada alamar gamsuwa.

MATANA ✓Where stories live. Discover now