Chapter forty one

660 60 24
                                    

✨ *MATANA* ✨

*Mallakar*
       AUTAR MAMA

*FREE BOOK*

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*Comments*
*Vote &*
*Share fisabilillah*

*041*

      Bayan sallar Isha'i Mustapha da Inna na tsakar gida su na hira Ammar yayi sallama. Inna ce ta amsa masa tana gyara masa wajen zama. Ƙarasowa ya yi ya na tsugunnawa ya gai da ita sannan ya miƙawa Mustapha hannu sukayi musaba sannan ya zauna yana fad'in ' Ya Zarah? "Tana ciki ka shiga mana" cewar Inna. Tashi yayi ya nufi bedroom ɗin inna. Zarah na kwace dan har bacci ya fara ɗaukarta. Saukar nunfashinsa taji a fuskarta, a hankali ta buɗe idanunta tana kallonsa, kawar da fuska tayi tana ƙoƙarin tashi, taimaka mata yayi ta tashi zaune, a gefan gadon ya zauna yana kallonta ya ce, "Dan Allah kiyi hakuri ki dai na wahalar dani  haka kizo mu koma gida" "Ni fa ba in da zan koma" "me kike nufi? Ya faɗa yana kafeta da idanu. "Kawai bazan koma ba, ban taɓa tunanin dangin ka zasu iya aikata abu irin wannan ba! Ban taɓa tunanin tsanar da suke min ta kai haka ba, bazan iya cigaba da rayuwa da mutanen da zasu iya min sharrin sata ba! Is better a san mafita" Ajiyar zuciya ya sauke yana fad'in " Me kike so nayi? Ko har kinyi give up a kaina? Kina so nayi ending ɗin auren? Shuru tayi zuciyarta na bugawa. Hannunta ya kamo yana fad'in "Bazan iya ba Zarah! Duk ranar dana sakeki tabbas zan iya kamuwa da mental problem, maybe ban taɓa zama na faɗa miki irin soyayyar da nake miki ba shiyasa kike ganin kamar abun wasa ne, Zarah zan iya miki koma a duniyar nan in hat bazan saɓawa Allah ba, Dan Allah kiyi haƙuri mu koma gidan mu, na miki alkhawarin abubuwa zasu canza, excluding my mother duk wanda ya miki rashin mutunci ki rama ni na saki ko waye in har ba Mami bace, dan Allah Zarah" "Shikenan naji amma bazan koma yanzu ba" Ta faɗa tana ɗauke idanunta a kansa. Murmushin jin daɗi yayi yana kallon ta ya ce, "Shikenan na gode, ina kuma fatan zaki dawo nan kusa" Banza ta masa tana kwanciya. Kiss yayi mata a kumatu yana fad'in "Good nite Allah yayi miki albarka" Karo na farko daya furta masa kalmar Amin a fili a duk lokacin daya saka mata albarka. Murmushi yayi sannan ya fito. Mustapha ya gani yana cin tuwo da cokali, zama yayi yana ɗan murmushi ya ce, "Gayu! "Gyara zaman ka muci mana" Cewar Mustapha yana kallonsa. "Wa?! Ni?! Allah ya kiyaye" Ammar ya faɗa yana dariya. "Bangane Allah ya kiyaye ba? Dani ne bazaka ci ba ko yaya? Mustapha ya faɗa cike da rashin fahimta. "A'a bana cin wannan koriyar miyar ai, kai, tuwan ma sai ya zama dole" Dariya Inna tayi tana fad'in "Ai kaine ɗan gayun ba Mustapha ba" "Toh inna bari na wuce gida, a dai kula min da mata" Ya fada yana tashi daga kusa da ita dan kaɗan daga aiki ta maka masa maficin dake hannunta "Ai da kafin ka santa kai kake kula min da ita, zaka ɓace min da gani ko sai na zabga maka maficin nan? Dariya yayi yana fita. Bayan Mustapha ya kammala cin abincin ya kalli Inna ya ce, "Inna bari na wuce" "Ka wuce ina? Cewar Inna tana kallonsa. "Hotel ɗin dana kama" "wani otal kuma ana zaune ƙalau? Tas na saka Saude ta gyara maka dakinsu na da, ga katifa da komai a ciki ka dai yi maleji an saba rayuwar turai" Shafa kansa yayi yana fad'in "Kayana suna chan ai" "Eh kuma hakane sannan ka biya kuɗi ko? "Eh Inna amma ba matsala suna refunding, bari naje zan dawo" da toh Inna ta amsa sannan ya fita. Kayan da yaci abinci ta kawar ta naɗe tabarmar sannan ta shigo daki. A zaune taga Zarah ta kafe waje daya da idanu. "Wannan tunanin dai bashi da amfani, ki daina" cewar Inna tana ɗaura musu net. Ajiyar zuciya Zarah ta sauke tana kallon Inna ta ce, "Inna inason mijina amma meyasa nake mafarkin Yaya? "Waye yaya? Cewar Inna tana barin abinda take yi. "Mustapha" Xarah ta faɗa tana kallonta. "Mafarki kuma? wani iri? Inna ta faɗa cike da mamaki. Ka sa magana ta yi dan bazata iya faɗawa Inna cewa tana mafarkin Mustapha yana faɗa mata yadda yake kaunarta in such a romantic way. "Toh Zarah ki dage da addu'a Kinji? Yanzu ke matar aure ce kuma mijinki yana ƙaunarki danginsa ne kawai matsala amma watarana sai labari in sha Allah" Cike da damuwa Zarah ta kalli Inna ta ce, "Kuma Inna akwai wata likita da muka haɗu a turai, har da ita a kayi wa Hydar aiki, rannan take faɗa min wai sonshi take yi" "Toh ke ina ruwanki? Cewar Inna tana kwanciya kusa da ita. " Shine nima ban sani ba idan na tuna sai na dinga jin ba daɗi" Murmushin Inna tayi tana fad'in " Ki tsayar da zuciyarki waje ɗaya Zarah, Ammar shi ne wanda kike so! Rashin kwantar da hankali da rashi samun kwanciyar hankali a gidansa shi yasa duk kike tunanin ire²n wannan, bakiji masu iya magana sun ce duk wanda ya tuna bara be ji daɗin bana ba?... Ke kanki kinsan rayuwar aurenki da Mustapha tafi miki kwanciyar hankali, Allah ya baki shi kin yi watsi da zabinshi ke lallai Ammar kike so! Shiyasa ko wani bawa ana so ya zamana me neman zabin Allah a duk abinda zai yi a rayuwar shi, yanzu ba gashi Allah ya baki Ammaru ba? Amma me? Bakiyi tunanin rayuwar auren zata kasance a haka ba. Abinda nake so ki fahimta shine ita rayuwa sai haƙuri kuma ko wani bawa da tashi kaddarar, kar ki bari zuciya ta kai ki ta baro ki kinji ko? Ki rungumi mijinki shi kuma Mustapha Allah ya bashi alkhairin sa, dan tabbas Mustapha mutum ne" "Amma Inna bana so inga yana kula wasu matan bana jin daɗi" Xarah ta faɗa har cikin zuciyarta. "Wannan kuma sakarci ne irin naki, da haka zai ta zama? Ke ba gashi kinyi aure ba? Na dai faɗa miki kiyi addu'a shedan ne kawai, tunda da bakin ki kince kina son Mijinki, kar na ƙara jin zancen Mustapha a bakinki in dai ya shafi wannan, kuma ki shirya gobe ki bi mijinki dan banga amfanin zamanki anan ba da aurenki kuma shi mijin bai ce bazai iya jinyarki ba" Kamar Zarah za tayi kuka ta ce, " Dan Allah Inna ki bari ko sati ne nayi" "naki na bari ɗin" Inna ta fada tana gyara dankwalin kanta. Xarah bata kuma cewa komai ta koma ta kwanta, ita dai ta rasa me ke mata daɗi, tabbas tasan tana son Ammar amma family issue ɗinsa yasa taji ta gaji da auren, in the other hand Kuma meyasa a kwanakin nan zata dinga mafarkin Mustapha? She need to get rid of everything that happened, Ammar take aure kuma da chan bata mafarkin Mustaphan sai yanzu? What's wrong with her? "Da bacci kikayi ya fiye miki wannan tunanin" Taji inna ta faɗa. Gyara kwanciyarta tayi tana lumshe idanunta. Mustapha bai dawo gidan ba sai wajen 11 na dare, har Inna ta fara bacci taji shigowar shi, fitowa tayi daga ɗaki tana masa sannu da zuwa, jagora ta masa har ɗakin komai neat dai², kayan ta ajiye a gefan katifar tana fad'in " Idan kana buƙatar wani abun ka min magana" Yana murmushi ya amsa da toh. Sai data rufo gidan sannan ta koma ta kwanta.

MATANA ✓Where stories live. Discover now