✨ *MATANA* ✨
*Mallakar*
AUTAR MAMA*FREE BOOK*
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*
*Comments*
*Vote &*
*Share fisabilillah**032*
Kallon Hydar kawai Mustapha yake yi yana jin wata iriyar soyayyar yaron na shigarshi, Dr Aminatu ce ta kalleshi with beautiful smile on her face ta ce, " I think he's sleeping now, zaka iya fita ko? "I'm going nowhere Dr. Kin tabbatar dai Bacci yake? Murmushi tayi tana kallon Hydar ta ce, "It's like a miracle, actually His mother tried! Duk da cewa bad idea ne saboda an masa surgery, but it helps, da taimakon Allah da taimakonta da kuma kokarin Dr Logan, that why I like his work! Naji daɗi komai ya faru kamar kiftawar ido! I'm so sorry da abinda ya faru, sometimes kasan irin hakan na faruwa" "Dm, ai na fahimta, ya ita Zaran? Cewar Mustapha yana kallon ta "Well, zata iya farkawa a kowani lokaci, dan banyi ma tunanin zata kai up to 2 days bata farka ba, karku wani damu anyi surgery ɗin lafiya kuma inshallah zai tashi lafiya" "Thanks" Ya fada yana kallonta. Murmushi ta ɗanyi tana gyaran murya kaɗan ta ce, " Wani abu ya shige min duhu, who's the father? I mean hydar's father, You our Dr Ammar? Kansa ya shafa yana ɗan sauke numfashi kafin ya ce, "He's my son" "Ok" Ta faɗa tana tunani kala² a ranta, but wannan be shafe ta ba hakan yasa ta kalleshi ta ce, "Muje ko? "Ai na faɗa miki babu inda zanje" ya fada yana murmushi "ok then, amma kasan ba'a nan zaka kwana ba ko? Gyada kai yayi ba tare da yace komai ba. Murmushi tayi tana barin ɗakin. Ward din da Zarah take ta nufa, a zaune ta tarar da Ammar ya riƙe hannunta yana kallonta. "Your wife is ok Dr Ammar! Cewar Dr Aminatu tana ƙarasowa ciki Nunfashi ya sauke a hankali yana kallonta ya ce, "Na sani ina jin tsoran halin da zata shiga idan ta tashi, kinsan condition ɗinta, and now the baby is ok! Idan idan ta shiga cikin wani yanayin bazan iya jurewa ba, komai yana faruwa ne ta dalili na! "Kar kayi blaming ɗin kanka, kawai kayi mata addu'a ita da Hydar insha Allah zasu warke, ina mahaifiyarta? Ko ta tafi? "Eh, amma zasu dawo kafin dare insha Allah" Ammar ya bata amsa. Kai ta Gyaɗa tana mai da dubanta kan Zarah dake kwance Idanunta a lumshe ga karin ruwa ta jikin cannula ɗin dake hannunta. "Na Barka lafiya" Ta fada tana fita. Kallon Zarah yayi yana shafa gefan fuskarta cikin soyayya da kaunarta ya ce "Dan Allah ki farka haka" Haka Ammar yayi ta zama a wajenta har kusan zuhur prayer, knocking ɗin kofar ɗakin akayi, ɗagowa yayi daga jikin gadon da Zarah take dan yayi resting ɗin kansa. "Come in" ya faɗa yana kallon ƙofar. Mustapha ne ya shigo, har ya sauya kaya zuwa long sleeve brown da baƙin jeans yayi kyau abinsa. "Ya Zarah? Ya faɗa yana ƙarasowa. "As you can see! Cewar Ammar yana ɗauke kansa daga gareshi. "Kai fa matsala ce dakai wallahi! Tambaya nayi just amsar da zaka bani sai ka faɗa min bakar magana? "Amsa na baka ai dai² da tambayarka! Cewar Ammar yana ɓalla masa harara kamar wata mace. Murmushi kaɗan Mustapha yayi dan ya lura kishin banza da wofi Ammar ɗin ke yi! Wajen zama ya samu ya zauna yana kafe Zarah da idanu duk ta rame sai hancinta daya ƙara fitowa sosai. Blanket Ammar ya ja yana rufe mata jiki ya bar iya fuskarta ba tare da yace da Mustapha komai ba. Dariya Mustapha yayi kaɗan yana shafa kansa idanunsa a kan Ammar ya ce, "Dirty mind ɗinka yace maka jikin matarka nake kalla ko? Nasan addinina Ammar! "Did I say a word? Na rufe mata jiki saboda sanyi kai ne dai me dirty mind! Cewar Ammar. "Shikenan naji Mr Ammar, but can we talk? Very serious issue! Ya fada yana kallonsa. "Not on Zarah dai ko? Cewar Ammar yana masa kallon tara saura kwata. " Kasan zaman gauronta babu daɗi, i need a wife! "Ok yaushe nace maka na fara safarar mata? Ko na taɓa faɗa maka ni mai dalilin aure ne? "Kai fa ka fiya yarinta wani lokacin! Serious magana fa nake maka! Cewar Mustapha yana ɗan bata rai "Ok me zan maka? Ammar ya faɗa ko a kwalar rigarsa. " Mom ɗina tana son nayi aure and I have no GF" "Yaushe har na zama abokin ka da zaka dinga tattauna irin wannan issue ɗin dani? Cewar Ammar yana kallonsa. "Zamu iya zama ai! Dama kai kake jin haushina" "Uhumm kai ne dai ka fara jin haushina tun lokacin da Zarah ta dawo gidanku i have no issue with you then! Ammar ya faɗa yana kallon Mustapha. "Amma yanzu kai kake jin haushina! Maimakon ma ka fara praising ɗina kana gode min! "For what? Ammar ya fada cike da rashin fahimta. "Na divorcing Zarah mn har ka aureta! "Don't try me! Dama chan haka Allah yayi, na rigada na sani we were made for each other! Rabon zaku haifi hydar ya saka kukayi aure" Gyaɗa kai Mustapha yayi yana jin zuciyarsa tayi nauyi, yana fatan ace better partner ɗinsa zata shigo rayuwarsa ASAP, ko zai manta da Zarah" "Tunanin fa? Ammar ya faɗa yana kallonsa. "Nothing, so we are friends right? Kai Ammar ya girgiza yana kallonsa ya ce, " Sai Zarah ta yarda ka jira ta farka! Murmushi yayi me kyau yana kallon Ammar ba tare da ya ce komai ba. Sai 8pm suka bar asibitin, washe gari da safe Mustapha ne ya fara zuwa, wajen Hydar ya fara nufa, ya buɗe idanunsa har ana feeding dinsa through naso gastric tube, Murmushi yayi yana kallon nurse ɗin ya ce, "Ya condition ɗinsa? "Lafiya lau, anjima dai za'a je a duba kan sa idan komai yana lafiya" Kai ya gyada a hankali sannan ya ce, "Bari naje na dawo" Da ok Nurse ɗin ta amsa sannan ya bar ɗakin. Wajen Zarah ya nufa, a zaune ya ganta da Nurse ɗinta tana daure mata gashi, har an sauya mata kaya zuwa pink dress na asibiti. Ƙarasawa yayi yana kallon Nurse ɗin tare da yi mata sannu da aiki. Amsawa tayi tana ɗorawa da faɗin " Yanzu tana lafiya babu abinda ke damunta, zaku iya zuwa ɗakin Hydar ta ganshi tun da na sanar da ita yana raye take son zuwa" "Ok insha Allah, ta daɗe da farkawa ne? "Tun jiya da daddare" Nurse ɗin ta bashi amsa. Kai ya Gyaɗa kafin ya miƙa godiyar sa ga Allah. Fita tayi dan dama ta gama abinda ya kawota. "Sannu" Cewar musty yana kallonta. Sauke Idanunta tayi daga kallonsa tana jin hawaye na ƙoƙarin cika Idanunta. "Ya jikin? Shuru tayi dan idan tace zatayi magana kuka ne zai kufce mata. "Kin dai na magana ne? Ɗagowa tayi tana girgiza kanta ta ce, "Kayi hak... Maganar ce ta kakare sakamakon kukan daya kufce mata.. "Shiiiiiii, kinaso raina ya ɓaci ne? Ko kina so su Ummi suzo su ganki kina kuka? Kai ta girgiza tana ƙoƙarin tsayar da hawayenta. "Good, taso muje wajen Hydar" Kai ta gyada tana sakkowa a hankali, taimaka mata yayi ganin kamar zata fadi, bayan sun isa ɗakin ta kafeshi da idanu, sai wasa yake abunsa da alama sauki ya fara samuwa, hawaye masu zafi ne suka sakko mata, ɗaukarshi tayi tana rungumeshi a jikinta bugun zuciyarta na ƙaruwa sosai. "Ka yafe min! Ta faɗa tana kallon fuskarsa. Shima kallonta kawai yake yi, "Be careful next time! Cewar Mustapha yana murmushi. Itama murmushin tayi tana gyada kanta. "Kinsan abinda zai ce kenan shine na ari bakinsa! Dariya ta yi me sauti tana ajiyeshi tare da kai dubanta ga Mustapha ta ce "Me ya faru bayan na shiga shock? " Well, kafin mu bar asibitin he started producing low sounds so sai na mayar dashi wajen Dr Aminatu itama kuma taji same sound da naji, so sun mayar dashi dakin surgery ɗin suna ciki dai wani likita yazo suna ce masa Logan sunce dai babba ne sosai and he was expert Amma duk da expert dinsa munsan cewa kwanansa ne be ƙare ba, insha Allah sai ya girma na zabo masa mace me kyau kamar shi" Dariya Zarah tayi tana goge hawayenta ta ce, "Zabinsa zai aura, babu wanda zai hadashi da wata! "Ok then! As you wish! Kai ta girgiza tana ɗan murmushi ganin har dan sunkuyar da kai yayi alamar girmamawa. "Kina buƙatar hutu muje ki kwanta" kai ta girgiza da sauri tana fadin " Zan zauna anan" "kinsan Kema dai patient ce! Kuma anjima kaɗan su Ummi zasu zo so kike ince musu kina musu da DRs? Kai ta girgiza tana kallonsa. "Good! "Ina Aysha? Yaji ta faɗa unexpected.. banza yayi mata yana fita daga ɗakin, biyoshi tayi tana fad'in " Kayi Shuru" "Nima bansani ba ai" Bata kara cewa komai ba har suka koma ɗakinta.. Yana gyara mata pillow Ammar ya turo ƙofar, tsayawa yayi ya ɗan kallesu kafin ya karaso ciki sai ƙhamshi yake yayi kyau cikin ƙananan kaya. Kusa da Zarah ya tsaya yana riƙo hannunta ya ce, "Sai da kika wahalar dani sannan zaki tashi? Zame hannunta tayi daga cikin nashi ba tare da tace komai ba. "Ina zuwa" Cewar Mustapha yana fita, da kallo ta bishi har ta daina ganinsa. Gefan gadon ya zauna yana matsowa daf da ita har suna iya juyo numfashin juna.. "Kina son bani wahala ko yaushe ko? Sauke Idanunta tayi a hankali tana jan nunfashi tare da saukewa a hankali. " Likita ta dubaki? "Eh, jiya bayan na farka tayi observing dina tare da ɗaukar vital signs Kuma tace I'm ok and nima bana jin wani ciwo" "Masha Allah, Hajiya, hafsat, Saude da Umar suna gaida ke" "Ina amsawa" Ta fada tana ɗan kallonsa. Murmushi yayi ganin kamar tana avoiding su haɗa ido. Hannu ya saka a habarta yana ɗago da fuskarta, still kin yarda tayi ta kalleshi.. " U'r a thief Zarah? "WHAT! ta faɗa tana zaro idanuwanta da sauri. Haɗe rai yayi yana kallon ta ya ce " Karya nayi? Kice ke ba thief bace? Juya Idanunta tayi dan yanzu ta gano inda ya dosa.. "thieves dai! Ta faɗa tana kokarin tureshi, riƙeta yayi yana murmushi ya ce " Kin sace min zuciya Zarah, i adore you zarah kin san me? Kai ta girgiza tana kallonsa. " You complete me, na gode for second chance ɗin da kika bani insha Allah baxan baki kunya ba kuma zan baki farinciki na miki alkhawarin wannan" "Ok" Ta fada a hankali. "Ni kuma alkhawarin me zakiyi min? Kai ta girgiza tana ɗan murmushi ta ce "Ai nayi me wuyar tunda na kara trusting dinka har na aureka" "Uhm me wayo, amma dai yau tare zamu tafi ko? Kai ta girgiza tana kokarin barin jikinsa. "Meyesa a'a? Ya fada cikin sexy voice. "Ni zan zauna wajen Hydar fa" "Ok shi kuma baban hydar fa? Dariya tayi tana ɗan tureshi. "I'm serious fa, ki ma shirya mu koma hotel tare" "Ni wajen Ummi zanje tun da tazo ko gaisawa bamuyi ba" "Duk wayonki dai yau tare zamu tafi insha Allah" "Nifa ba inda zanje" "Kyayi kya gama" bata ƙara cewa komai ba sai numfashi da take saukewa a hankali. Har 12pm basu ƙara ganin Mustapha ba, sai su Ummi da suka zo, by 2 suka bar asibitin saboda ba'a son relatives suyi yawa. Da daddare bayan Isha'i Zarah na zaune kusa da Hydar tana rike da mini wrist ɗinsa tana murzawa a hankali, ita sai taji ma tafi son Hydar a yanzu da baida lafiya akan da chan, wata iriyar soyayyarsa ta daban ce ta ke ɗawainiya da ita a yanzun. Nunfashi ta sauke tana mikewa tsaye tare da kallon nurse ɗinsa ta ce " Zan tafi dan Allah ki kula da yarona" murmushi nurse ɗin tayi tana kallonta ta ce "hakkina ne wannan baki da damuwa" Godiya tayi mata sannan ta fito, veil ɗinta ta gyara tana kallon corridor ɗin wajen. Tafiya ta fara yi dan Ammar ya ce da ita by 8 zai zo gashi har 8 din ta wuce.. lifter ta hau ta sakko ƙasa, lifter na budewa taga Ammar, fitowa tayi tana kallonsa ta ce, "ashe zaka zo? "Sorry i was late bacci ne ya daukeni, muje" Bata ce komai ba ta bishi suka tafi. Bayan sun isa masaukinsu veil ɗinta ta fara cirewa tare da cire rubber band ɗin data ɗaure gashinta dashi. Kusa da ita ya zauna yana kallonta ya ce, "Kinsan destiny never change it can only be delayed! A lokacin dana barki duk da cewar gangar jikina ce kawai ta barki, nayi tunanin bazan kuma samun gurbi a zuciyarki ba, Cox nasan ba kowace mace zaka je wa da irin wannan batun ba ta yarda da kai ba tare da tayi tunanin yaudararta zakayi ba, kinsan me? Ya ƙarashe maganar yana kallon cikin Idanunta. "Kai fa baka gajiya da magana, Ni kuma bacci zanyi saboda inaso na tashi da wuri" "Ok haka zaki ce? Banza ta masa tana tashi ta wuce toilet. Yana kwance yana latsa wayarsa ta fito daure da towel, ko kallon inda yake batayi ba ta nufi wajen kayansu, tas ta duba kayan amma babu sleeping wears, juyowa tayi tana kallonsa, ɗauke kai yayi dan dama kallonta ya ke... "Wai baka ɗauko min kayan bacci ba? "Kinsan a yanayin da muka taho, na manta! "Eh amma ai baka manta da naka ba, ta faɗa tana ciro kayan baccinsa" tasowa yayi yana kwace kayan ya nannaɗe ya koma kan gado tare da cusa kayan karkarshin filo. Kwafa tayi ta fara bincika kayan, shirt ɗinsa ta gani mara nauyi, daukowa tayi ta saka sosai tayi mata yawa, bata damu ba ta ɗauko skirt underwear ta saka tana ta kumbure². A gefansa ta zauna tana fad'in " Bazan kara dawowa ba! "Baki isa ba kuma" Ya faɗa yana latsa wayarsa. Ƙwace wayar tayi tana kallon screen din wayar, chatting yake yi, contact din ta duba, Mustapha taga an rubuta, sai kuma idiot da Mustapha taga ya turo yanzun haɗe da voice note, "Waye Mustapha? Ta faɗa tana kallonsa. "Wanda kika sani" cewar Ammar idanunsa a kanta. Scrolling chats din ta fara yi, sosai sukayi chat kuma daga jiya ne zuwa yau... "Yaushe ku ka saba har haka? "Jiya fa! He's nice kuma" "Uhm" cewar Zarah tana miƙa masa wayarsa. "But idan bakya so zan iya yanke abotar" Kai ta girgiza tana kwanciya ba tare da tace komai ba. Shima offline yayi yana ajiye wayarsa ya kwanta suna facing din juna, shi kam kullum kara son Zarah yake yi, yasan soyayyarta a jininsa take. He's incomplete without her! Idanunsa ya lumshe, turo baki tayi tana juya masa baya. Gabanta ya dawo yana murmushi ya ce, "Baki isa kin haramta min kallon fuskarki ba, infant dukanki not even your face" Idanunta ta buɗe tana kallon sa. "As she knows Ammar is handsome, damn handsome ma kuwa, sai dai taga ya ɗanyi duhu haskensa ya ragu ba kamar da ba" "Ohk muni na zaki gano kenan? Murmushi ta ɗanyi tana ƙoƙarin sake juya masa baya amma ya hana hakan faruwa ta hanyar riketa. Washe gari da asuba shi ya tasheta sai daya jira ta fito daga toilet sannan ya jasu sallah, wanka ta shiga dan tana so taje asibiti da wuri dan taga abin ƙaunarta wato Hydar. Tana tsaye jikin closet zata dauki kaya Ammar yayi hugging ɗin ta yana shaƙar kamshin shower gel ɗin da tayi wanka dashi.. "Kaya fa zan ɗauka" Ta faɗa tana son tureshi, bathrobe din jikinta ya kwance da sauri ta riƙe tana zaro idanuwa kamar shege a rabon gado. " What? Ya fada yana kallon fuskarta. "Banaso" "Ni kuma ina so" Kamar zatayi kuka ta ce, "I'm serious" Bai kulata ba ya cire hannunta jikin bathrobe din yana mayar da gurbin hannunsa.. a hankali ta lumshe idanunta, gabanta ne ya fara fad'uwa tunowa da wancan ranar. "Ammar Pleas... Bai bata damar ƙarasawa ba sakamakon bear hand dinsa da taji cikin jikinta.. bathrobe din jikinta ne ya faɗi, hakan yasa tayi hugging din Ammar dan kunya ce ta rufeta... "I'm your husband Zarah, wannan jin kunya bashi da amfani, kuma bana so kinji ko? Ya raɗa mata a kunne, kamar zatayi kuka haka taji, ita ta rasa gane kan abu, wancan time ɗin ma yazo da zafinsa daga karshe kuma abu ya garara, bata so hakan ta sake faruwa, na farko tana cutuwa na biyu kuma tana saka Ammar raina kansa kuma sam bata son yana jin hakan. "Abinda kike tunani bazai faru ba insha Allah" Ya faɗa yana sauke numfashi a hankali dan yasan bazai wuce abinda ya faru kwanaki ba take tunawa, kuma dai shi yasan lafiya lau yake, ko da yajewa Bilkisu and see if any problem will occur normal normal komai ya tafi smoothly yana fatan yanzu ma bazai samu wata matsala ba. Ni kuwa ganin abun yana son din karfin idona ya saka na kwaso littafina da nake ɗauko muku rahoto na bar ɗakin a 360 lol... Few moments later na koma, Zarah na kwance cikin duvet, Idanunta a rufe amma ba bacci take yi ba, ita kadai tasan zafin da zuciyarta take yi, ita kadai tasan yadda take ji, zuwa yanzu ta sawa ranta kusantarta ne kawai Ammar baya sonyi! Idan Dagaske bashi da lafiya ta yaya har Bilkisu ta haifi Raihan? Amma kuma idan daga baya cutar ta kamashi fa? Kai ta girgiza tana tunanin indai yasan bashi da lafiya tasan halin Ammar bazai taɓa boye mata condition irin wannan ba dan yasan aure zasuyi dole ko ya boye zata gano! Toh ko dai dagasken bashi da lafiya yana tsoro ya sanar mata tun lokacin ta ki yarda da aurensa? Ko kuma dai sai bayan da akai auren abun ya samesa? Ko kuma dai kawai baya son having wani affairs da ita ne? Sam bata da amsoshin tambayoyinta, buɗe Idanunta tayi tana kara ƙudunduna cikin bargo, ita kam wannan wace irin rayuwa take ciki! Tana tsananin bukatar mijinta amma kiri² babu dama? Ni kuwa nace Allah ya kara kema ki ɗanɗana kiji in da dadi... lol. Ammar ne ya fito daga toilet, ba ƙaramin ciwo kansa keyi ba, a gefan gado ya zauna, slowly ya kira sunanta, banza tayi dashi tana jin wani haushinsa. "Ki tashi ki shirya ga abinci kici Kinga rana tayi" Nan ma bata ce komai ba. Ajiyar zuciya ya sauke yana yaye duvet ɗin data rufa, gyara bathrobe din jikinta tayi tana miƙewa zaune ba tare da ta kalli direction din da yake ba. Shima bai ce da ita komai ba sai riƙe kansa da yayi, ya rasa me yake damunsa duk wani bincike ya nuna lafiyarsa kalau, kuma ya kara tabbatar wa akan Bilkisu, meyasa sai akan Zarah zai dinga komawa mara lafiya? Wayake dashi da zaiyi sharing irin wannan lamarin ko zai samu mafita! He can't solve this alone! Bazai iya tunkarar Umar da maganar nan ba! Umar ne kaɗai abokinsa kuma ɗan uwansa da yake iya budewa cikinsa, amma ta yaya zai sameshi da wannan maganar? Toh ko dai text zai masa? Kai ya girgiza dan sosai maganar tayi masa nauyin furtawa, bayan Umar dai sai Mami, su kadai ne yake iya faɗa musu damuwarsa, ai har gwanda ma ya samu Umar da maganar akan ya samu Mami, amma yana fargabar ya sanar da Umar shi kuma Umar ya sanar da Matarsa wanda yana da tabbacin bakin Umar ba wani sakata ce dashi ba, zai iya cewa ma zai nemi shawarar Hafsat! Kai ya girgiza yana sauke ajiyar zuciya ganin duk bashi da mafita, indai kuwa ba Umar zai faɗawa ba toh bashi da inda zaije dan haka bai da wani choice hakan ya yanke shawarar sanar da Umar halin da yake ciki tare da gargaɗin kar wanda yaji batun including his wife Hafsat. "Mu tafi! Yaji Muryar Zarah, ɗagowa yayi ya kalleta, har ta shirya cikin doguwar riga ta yafa mayafi fuskarnan a tamke tamau! Shi zai iya cewa be taɓa ganinta cikin ɓacin rai irin wannan ba. Nunfashi ya sauke a hankali yana fad'in "Bari na shirya zauna" Bata ce komai ta nemi wajen zama, cikin kankanin lokaci ya shirya, har suka bar hotel din bata ce dashi komai ba, haka a hanya har suka isa asibitin, a reception suka ci karo da Aysha, wanda sam bata kula da ita ba saboda tafiya take tana tunani.. "Sorry! Cewar Zarah tana kokarin wucewa dan bata ma ganeta ba saboda hankalinta baya wajen. "Zarah! Cewar Aysha tana riƙota.. juyowa Zarah tayi tana kallonta from head to toe sai kuma ta ɗan saki fuska ta ce " Ashe kece! Me kike anan? "Wallahi dad ɗina ne ya samu accident muna A&E kefa? "Yarona akayi wa aiki" "Ayya Allah ya basu Lafiya, ya rayuwa? Kafin Zarah tace wani abu Ammar ya ƙaraso... Gaida shi Aysha tayi dan ta shaida shi. Amsawa yayi yana murmushi, wucewa yayi ya barsu. "Bari na ƙarasa biyan kudi, faɗa min a ward din da kike" Cewar Aysha tana kallonta. "Neuro surgerical ward! Ta faɗa tana mata sallama. Doctors ta gani a ward din da Hydar yake bayan ta isa, gabanta ne ya faɗi tana ƙarasawa da sauri, Dr Aminatu ce ta fito tana rayata stethoscope ɗinta, ganin Zarah ya sakata sakin murmushi ta ce, "Ai na ɗauka yau bazaki zo ba" "Ya Hydar yake? Cewar Zarah tana leƙen ward din. Dr Aminatu na murmushi tace " He's ok, Dr Logan ne yazo dubashi tare da sauran Dr kinsan yaron akwai shiga rai, but he's ok, result ma daya fito ya nuna komai lafiya, kinsan warkewa sai a hankali, soon ma zamuyi discharging dinku sai dai ku dinga zuwa checkup" Ajiyar zuciya ta sauke tana riƙe hannun Dr Aminatu ta ce, "Na gode" "Godewa Allah" Cewar Dr Aminatu tana murmushi.. barinta tayi a wajen ta wuce, sauran Drs ɗin ma tafiya sukayi Mustapha da Ummi kawai aka bari a ɗakin sai Hydar, ƙarasa shiga tayi tana sunkuyar da kanta ta gaida Ummi, amsawa tayi tana shafa kanta ta ce, "Ya kike? "Lafiya lau Ummi! "Yawwa haka nake so! Ga dai yayanku nan ku dinga bashi shawara, har yanzu yaƙi fito da mace yayi aure, Ni na bada shawarar yaƙi ɗauka bansani ba ko ku kannensa" Satar kallonsa Zarah tayi shima ita yake kallo, murmushi ta ɗanyi kafin ta ce " Toh Ummi! "Yawwa da yafi ai Kinga shima idan Hydar ya taso zai fi jin daɗi" kai kawai Xarah ta Gyada tana kallon direction din da Hydar yake. "Zainab da Farida suna gai dake" cewar Ummi tana kallonta. "ina amsawa Ummi" Zarah ta amsa very slowly. "Akwai magungunan da zan karbo a Pharmacy Mustapha muje ko? Ummi ta kuma faɗa tana kallonsa. "Zan biyoki" Kai kawai ta gyada sannan ta fita ta barshi. Nunfashi ya sauke yana ƙoƙarin saita feelings ɗinsa, idanunsa akan Zarah ya ce, "Ummi tana so nayi aure, Daddy ma haka, Nima kuma haka, so ko zaki samar min matar aure? "Ai na ɗauka kana son Aysha" Ta faɗa ba tare da ta kalleshi ba. " Ai nasha faɗa miki Aysha ƙawata ce kuma yanzu babu wannan ƙawancen" "Na ganta ai a reception ɗazu" "Ita Ayshar? Cewar Mustapha cike da mamaki. " Eh anjima kaɗan nasan zata zo nan ɗin saboda na faɗa mata inda nake" "Kin kyauta! Ya faɗa ransa a ɗan ɓace. "Da nayi me kenan? Ina ce tun farko kai ka fara gayyato ta cikin rayuwarmu? Infact ma ni banga macen data fi dacewa da kai ba sama da Aysha! Tana kaunarka ko ma dai menene ya rabaku ya kamata ku sasanta kanku tunda kun daɗe da fahimtar junanku" "Ban taɓa tunanin ƙiyayyar da kike min ta kai haka ba! Cewar Mustapha yana rungume hannayensa. " Uhm, kai dai ka sani ni gaskiya na faɗa maka" "Shikenan! Amma ni ko mata sun kare bazan iya auren Aysha ba, da ace ma kin canza shawara da yafi" "Ok ka cewa abokinka ya nema maka mana! "Aboki kuma? Idanunsa ta kalla sannan ta ɗora da faɗin " Eh ko kana da wani abokin bayan Ammar wanda naga daga kulla abotar har kun shaƙu?" Murmushi yayi me kyau yana shafa kansa sannan ya ce, "Ƙanina ne fa, ko dai a cikin siblings ɗinsa zai bani ɗaya? Da sauri Xarah ta kalleshi tana tsuke fuska ta ce, "Allah ya kiyaye! "Bangane Allah ya kiyaye ba, wani abu ya faru da hakan ne? Kai ta girgiza sannan ta ɗora da faɗin " Kawai dai Allah ya kiyaye, ga mata nan dayawa, kar ma kayi masa zancen ko da wasa, akwai match making da ake yi halal one sai ka nema a chan, app ne zan turo maka tunda kayi kwantai! Ta ƙarashe maganar tana yar dariya. Gyaɗa kai yayi ya ce, "Wato abin har ya kai ga match making? Bata kula shi ba ta ɗauki Hydar ta fara ƙalla fuskarta dauke da ni'ima, sosai yaron nata yake samun sauƙi tasan ko da ace zata haihu nan gaba toh tabbas Hydar na daban ne! "Bari nabi Ummi" Cewar Mustapha yana kallonta, kafin tace wani abu aka fara knocking din kofar. "shigo! Mustapha ya bada izini, Aysha ce tare da Ammaru. Kallo ɗaya Mustapha yayi mata ya ɗauke kansa... "Buddy! Cewar Ammar yana miƙa masa hannu. "Is better ka kirani da Mustapha! Na faɗa maka bana son wannan buddy din! Cewar Mustapha yana miƙa masa nashi hannun suka gaisa. "Ok, pardon me, ya Hydar din? "Lafiya lau, mun godewa Allah" Murmushi Ammar yayi yana ɗan kallon Zarah ya ce, "Ga baƙuwarki na ganta tana neman ɗaki shine muka taho tare" Ko uffan Zarah bata ce dashi ba haka zalika bata kalleshi ba. Kansa ya shafa kaɗan yana basarwa ya maida dubansa kan Aysha ya ce, "Zauna mana" murmushi tayi wanda yafi kama dana yaƙe sannan ta ja kujera ta zauna tana kallon Xarah. "Ya jikin nashi? Zarah na kallonta ta amsa da " Da sauki, ya kike? kwana dayawa" Alhamdulillah, ashe Kinyi aure? Da UHM Zarah ta amsa tana kallonta. "Toh Allah ya sanya alkhairi yasa gidan zama ne" "Amin Nagode" Zarah ta amsa tana murmushi. "Bari na wuce na bar Daddy na shi kadai" "Ayya ya jikin nashi? Cewar Zarah cike da tausayawa. "Alhamdulillah na gode, samin contact ɗinki mana" Gyada kai kawai Zarah tayi tana karɓar wayar da Aysha ta miko mata, in seconds ta saka mata digits dinta sannan ta bata wayarta, godiya Aysha ta mata sannan ta fita. Shima Mustapha excusing ɗin kansa yayi ya fita... Gefanta Ammar ya dawo yana kallonta da kyau ya ce, " Zarah fushi kike? Shuru tayi, kuma bata kalleshi ba. " I'm talking! "Wai Dan Allah me kake so nace? Me kayi min da zan yi fushi? Kawai abin magana ne babu! Ta ƙarashe maganar tana tashi tsaye. Nunfashi ya sauke me karfi yana rungume hannayensa a kirjinsa Idanuwansa akanta ya ce, " Nasan kina da right ɗin da za kiyi fushi amma kuma kinsan hakan zaiyi hurting ɗina sosai ko? Ajiye Hydar tayi sannan ta juyo tana kallonsa ta ce , " oh ban sani ba ai! Ƙoƙarin fita tayi ya riko hannunta yana kallon cikin Idanunta ya ce " Ok Shikanan bazaki zauna ki fahimceni ba? "Na rigada na fahimta, dan Allah ya wuce" Ta faɗa tana dauke Idanunta daga cikin nashi. "babu abinda ya wuce Zarah tunda naga kina fushi... Kafin Zarah tace wani abu aka Turi kofar dakin, Mustapha ne rike da jakar magunguna, kallonsu ya tsaya yi na ƴan seconni sai kuma ya ce, " Sorry" daga haka ya kulle musu kofar. Kwace hannunta tayi daga na Ammar tana gyara zaman mayafin abayar dake jikinta, fita tayi daga dakin ta barshi da takaici. Bata kalli inda Mustapha yake zaune ba ta wuce abinta dan gaba daya ranta duk ba daɗi ga ingiza ta da zuciyarta ke yi akan kawai ba wai bai da lafiya bane baya son having wani affairs da ita ne saboda this isn't her first marriage! With those silly² thinking's of hers ta koma hotel ɗin da suka sauka......
Autarmama ce.